-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Dalilan Da Ke Haifarda Bauɗewar Babban Yatsan Kafa

Dalilan Da Ke Haifarda Bauɗewar Babban Yatsan Kafa

Dalilan Da Ke Haifarda Bauɗewar Babban Yatsan Kafa 

Bauɗewar ko karkacewar babban yatsan ƙafa da a ke cewa "hallux valgus" a likitance na daga cikin matsalolin da kan shafi tafin sawu. Wannan matsala na faruwa ne yayin da babban yatsan ƙafa ya karkace zuwa yatsa na biyu sakamakon canje-canje a tantanai (jam'in tantani) da ke riƙe da ƙasusuwan babban yatsa. Sai dai, wannan matsala ta fi bayyana ga mata. 

Daga cikin abubuwan da ke kawo matsalar sun haɗa da:

1] Gado: Kaso mai yawa na masu bauɗaɗɗen yatsan ƙafa suna gadonsa ne ta ɓangaren uwa ko uba. Haka nan masu shimfiɗaɗɗen tafin sawu  wato "flat foot" a turance, na da ƙarin haɗarin samun bauɗaɗɗen babban yatsan ƙafa.

2] Bayan samun wannan matsalar ta hanyar gado, ana samu ta hanyar sanya matsatstsen takalmin da ke matse yatsun ƙafa sosai, kamar takalmi coge. Sanya irin waɗannan takalma yau da kullum kan haddasa canje-canje a tantanai da tsokokin da ke riƙe da babban yatsan ƙafa. Saboda haka, akwai buƙatar sanya takalmi mai yalwataccen masakar yatsun ƙafa.

3] Ciwon kumburin gaɓɓai, kamar ciwon amosanin gaɓa (osteoarthritis), ciwon sanyin ƙashi (rheumatoid arthritis), ciwon gawut (gout arthritis), da sauransu.


Alamomin bauɗewar babban yatsan sun haɗa da:


  1. Bauɗewar babban yatsan ƙafa zuwa yatsa na biyu.
  2. Bayyanar kanta, wani lokacin tare da kumburi, a gefen maɗaukar babban yatsan.
  3. Ciwo tare da kumburi a dai-dai kantar babban yatsan ƙafa.


A yayin da kake / kike fama da irin wannan ciwon yatsan ƙafa, tuntuɓi likitan fisiyo domin duba ka / ki da bayar da shawarwari kan yadda za a shawo kan .


Daga Phusio Hausa

0 Response to "Dalilan Da Ke Haifarda Bauɗewar Babban Yatsan Kafa"

Post a Comment