-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tsohon Sanata Shehu Sani Ya Yiwa Buratai Wankin Babban Bargo Dan Gane Wa'adin Da Ya Bai Wa Boko Haram

Tsohon Sanata Shehu Sani Ya Yiwa Buratai Wankin Babban Bargo Dan Gane Wa'adin Da Ya Bai Wa Boko Haram

Tsohon Sanata Shehu Sani Ya Yiwa Buratai Wankin Babban Bargo Dan Gane Wa'adin Da Ya Bai Wa Boko Haram

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a ranar Alhamis, ya caccaki shugaban rundunar sojin kasa, Lt. Janar Tukur Buratai, a kan yadda yace ta'addanci zai iya cigaba da wanzuwa har nan da shekaru 20 a Najeriya.

The Punch ta ruwaito yadda shugaban sojin kasa yayi wata magana bayan 'yan kwanaki da 'yan Boko Haram suka kashe manoman shinkafa 43 a jihar Borno 

Tsohon sanatan ya mayar da martani a kan maganar, ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Alhamis, inda yace kalaman Buratai suna nuna karewar basira da rashin dabarun yaki.

Kamar yadda Shehu Sani ya wallafa, "Sanar da mutanenmu cewa tabarbarewar harkokin tsaro za su cigaba har na tsawon shekaru 20 alamace da ke nuna gazawa da karewar basirarka a matsayinka na soja. 

"Kuma alama ce wacce take nuna kana bukatar murabus, sannan kuma kana nuna wa duniya alamar cire rai daga samun nasara ne."

A cewarsa, ya zama tilas mutanen kirki, maza da mata, su hada karfi da karfe wurin kawo karshen rikicin addinin. Dr Gumi, wanda shine shugaban KHF ya fara shirin kawo karshen rikicin addini da ke addabar kudancin Kaduna, wanda yake hana cigaba da zaman lafiya.

Source: legit

0 Response to "Tsohon Sanata Shehu Sani Ya Yiwa Buratai Wankin Babban Bargo Dan Gane Wa'adin Da Ya Bai Wa Boko Haram"

Post a Comment