-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Azabtacciyar Soyayya Hausa Novels

Azabtacciyar Soyayya Hausa Novels

AUZUBILLAHI MINA  SHAIDANIR RAJIM,BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM
 

AZABTACCIYAR  SOYAYYA

Bismiallahi Rahmanir Rahim Wassalatu Wassalamu Ala Sayyidil Rasullahi Sallahu Wassalam.

Na sadaukar ga chaptan nan zuwa ga Mahaifiyata abun qaunata, Allah ya jiqanki da rahama yasa kina cikin rahamar Allah a daidai wannan lokacin dake da sauran Alumman Musulmi baki daya amin summa amin.

PAGE=>    A-A

        Wata yarinyace tana kwance kwanciyar nan da Annabi Muhammad SAW ya hanamu wato kwanciyar rufda ciki a wani haddaden gado na zamani wato China bed wanda yapi gadon da ake yayi a wannan zamanin wato Italian bed haduwa da kuma girma, juye – juye takeyi alamun ba bacci takeyi ba, juyin da ta qara yi ne  dara – daran idanuwanta suka hada ido da danqareren agogon bangon dake manne a dakinta inda ya nuna karfe 10:13am, dogon tsaki ta ja ta miqe tana yatsina fuska,  gyara rigar tayi da bajjajen gashin kanta, takalmin robanta na silifas ta saka inda ta nufi toilet don watsa ruwa, bata wuce minti 10 ba ta fito, ruwa kawai ta watsa sai kuma gashin kanta data sake chajewa ta gyarashi tsaff ta wankeshi, kai tsaye wurin kwaliyya ta nufa, karamar kwaliyya tayi bata jima ba, drawer din kayanta ta bude ta fito da wata riga yar kanti kalan jaa an rubuta I love `u` mom, ta sake dauko wani baqin wando ta saka, ta dauko wani abu shi ba dankwali ba shi ba mayapi ba  ta rataya shima kalansa ja ne kamar rigar da ta saka, wani hadadden takalmi mai kalan baqi ta saka wanda bashi da tudu sosai,   tana kan hanyar ficewa daga dakin, nasan mai karatu zai ce batayi sallah ba, babu sallah a tsarin rayuwar MISRA, gani takeyi kamar 6ata lokacine, karo sukaci da wata tsohuwa, tsohuwar ta tsuguna har qasa tace ina kwana? MISRA ko kallanta batayi ba balle tasan tanayi, wani daki ta iso, tana kwankwasawa aka amsa, MISRA ce tace anty ki fito da wuri ina sauri ne, ANTY tace to yar lelen baba, bude kofa akayi aka fito, ANTY tace ina kwana yar lelen baba? MISRA shiru tayi kamar ba zata amsa ba, an dau wasu daqiqai kafin tace lafiya qalau, ANTY tace naga kamar fuskarki ta bayyana farinciki, MISRA tayi guntun murmushi tace hakane anty, mafarki nayi wai talaka direban motan haya ya zazzageni shine abun yake firgitani kuma yake bani dariya, idan na tuna abunda nayi mafarki zai faru shine sai inyi murmushi nasan Wallahi sai yayi nadamar zuwansa duniya. ANTY ta riqe baki cikin mamaki, talaka kuma ya zageki, lallai kam kinga abunda babanki kullum yake nunamiki knan karda ki yadda talakawa su rainaki idan kikayi wasa wani har nan gidan zai debo tsumman rigansa yace yana sonki ko yaci miki mutunci, talakan mutum baiyi ba, banda hassada da zagin mutane basu da aikin komai, MISRA ce ta katse ta, ki rufewa mutane baki da-Allah malamarsu, nine talaka zaice yanaso wane shi wane uban ubansa mummunar fatanki ta qare akanki, ta juya zata tafi knan anty ta riqo hannunta yi haquri  MISRA ba mummunar addua nayi miki ba so nakeyi ki gane kinada bambanci da talaka kowa yasan babanki da irin bautar da yayiwa wannan qasar bama qasar nan ba kaf nahiyar afrika an sanshi, yanzu ki shiga ki dauko bindigarki idan mafarkinki ya zamo gaskiya Wallahi inji labarin kin harbeshi babu abunda zai faru. MISRA tace nagode anty ai na dauka tana cikin jaka ta, anty tace yawwa take care yourself { ki kula da kanki} MISRA tace I will { zanyi}, tana fita kenan naga wasu zaratan sojoji su 3 sun nufota, nan take suka durqusa sukace good morning ur royal highness, ko kallansu batayi ba, wurin wata baqa qaramar mota ta nufa, tana kokarin budewa, babban sojojin yace ur royal highness mune zamu fara gaba ko ke, MISRA juyowa tayi a fusace tace ohh my God! ugly moron can`t u leave me alone? ( wayyo Allahna, mummunan daqiqi meyesa ba zaka barni ba saika dameni) yau ni kadai zan fita ba tare da ku ba, Captain ya riqe baki yana takaicin baqaqen maganganun da MISRA kullum sai ta fada musu wani lokacin harda mari, babu yadda ya iya ya juya shida yaransa su 2 suka koma suka zauna akan benci, MISRA makulli ta sakawa mota, ta tayar da ita, ta nufo bakin gate, wani tsohone yana riqe da radio yana jin BBC yana girgiza kai, yanzu jiya da Asubah ma saida bomb ya tashi a massalaci Allah ya kyauta, horn takeyi masa (wato qara na mota) amma baijiba saboda abun ya bashi tausayi, fitowa tayi a mota, tana tahowa da huci hartana tuntu6e, tazo daf dashi kenan hucin isowarta yaji ya dago itakuma a lokacin ta kawo masa mari sai ya kawar da fuskarsa gefe, MISRA tace kai wannan tsohon wane irin dabbane iyyeh? Allah wadaranka shashasha kuma Wallahi wannan shine karonka na qarshe daman na ta6a yi maka gargadi sau 2, Baba Isa mai gadi yace yi haquri ranki ya dade ina hango su captain ne banga sun tashi ba shiyasa nima ban tashi ba, MISRA tsaki taja tare da danqara masa harara, wato saboda ni akuyace sunyimin tirke idan bada su ba akace maka bazan iya zuwa ko ina ba ko? Ko haihuwar kashin awaki muka fito dasu? Baba Isa yace a a kiyi haquri bazan qara ba, MISRA mota ta nufa, zaka tashine ka budemin kofa ko zaka tsayamin shirmenka daka sa ba, miqewa yayi ya nufi gate ya bude mata, MISRA tayar da mota tayi da niyyar fita waje. Tana fitowa bata duba kan hanya ba, hanya kawai ta dosa ba tare da ta duba ko akwai mai motar da yake zuwa ba, a daidai wannan lokacin  wata mai jar mota yana kan gudu akan hanyarsa, karo suka kusa yi, fasinjoji suka fara ambatan INALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN shikuma direba kokarin riqe motar yakeyi karda ta fadi, ita kuwa MISRA tasan abunda tayi amma ko a jikinta, tsayawa tayi tana dubawa akan ko sun buga mata mota ta koya musu hankali, fitowa tayi ta gama dubawa, bataga komai ba, cije baki tayi alamar mugunta Allah yaso su, tana kokarin komawa cikin mota su kuma masu motan sun iso, direban yace ke amma wace irin jaka ce? Tsinanniya shegiya wacce batasan meye takeyi ba, kin kusa kashe mutane shine ko ki tsaya ki duba balle ki bada haquri ya qare zagin yana tsaki yana nuna mata yatsa daga cikin mota. MISRA mutuwar tsaye tayi, ta rasa maganar a mafarki takeji ko a zahiri, baqin gilashin idanunta take kokarin cirewa don taga wanda yake neman tafiya lahira, muryar wani saurayine yace kai amma Wallahi kayi kuskure direba abunda yafi maka sauqi kaja mota mu gudu karda wannan tsinanniyar tazo ta sameka don Wallahi ta sameka sai kashinka ya bushe yarinyar yar tsohon major general Abubakar ne, nan mutanen da suke mota suka riqe baki sukace major Abubakar kuma? Direba kabi maganar wannan bawan Allahn don harka da sojoji babu dadi, direba yana tunani amma ya yanke shawarar bin magaanr mutanen motar da yake ance ba`a qin ta mutane, MISRA tana kokarin tahowa wurinsu kenan shikuma ya tayar mota ya fara gudu, juyawa tayi inda ta zabga zagi tace kan uba Wallahi ko ubanka waye yayi karya yau saika gane shayi ruwane, da gudu ta koma mota har tana faduwa, tana shiga mota ta tayar da ita, tana tafiya sai saqe – saqen rashin mutuncin da zatayiwa wannan direban takeyi, can kuma maganar anty ta fado mata da tace ta dauki bindiga, baki ta cije, tace wallahi da saina harbeshi idan yaso nima inga mai harbeni, Mallam Idi direba gudu yakeyi babu sassautawa saboda wannan saurayin sai qara fadamsa rashin mutuncin da sojojin major general sukeyi, MISRA ma gudu takeyi tana ta tunane – tunane, isowa hanya sukayi mai hannu 4, Malam Idi yabi hannun kudu, itakuma MISRA saboda ta sunkuya dauko wayarta tana qiranta babanta kafin nan harta rasa inda yabi, hango wata jar mota tayi ta doshi hannun arewa, tace yawwa gashi can,  a zuciyarta tace lallai idan nayi wasa wankin hula zai kaini dare,  qarawa mota gudu takeyi tsaki taja babanta bai dauki wayarta ba, Malam Musa direban daya motar da Misra ke bi, kana ganin fuskarsa kasan yana cikin farinciki, yau tuqi ya kar6eshi ya samu kudin da zai biyawa dansa guda daya tilo Uzairu dama yau sati 2 kenan da aka koroshi saboda bai biya ba, kuma ya biya kudin hayan motan  masiffafen maigidansa Alhaji tanimu mutuncinka Naira. Tuni MISRA harta iso sa kallonsa tayi tace Allah sarki tayi murmushin mugunta, cinkoson ababen hawa suka samu sosai wato abunda bature yake cewa GO SLOW amma saboda Mallam Musa ya fita iya tuqi kuma motarsa qaramace haka ya lalla6a ya bar MISRA tana cizon yatsa, tunani tayi kamar ta fito ta hau mashin sai kuma daya zuciyar tace motar da kika bari a tsakiyar titi fa? Malam musa harya sauqe fasinjoji inda ya koma can bayan wani gini yana kirga da lissafin yadda zai karkasa kudin, yana cikin lissafin MISRA ta shigo dubawa takeyi ko zata hango jar motarsa amma bata gani ba, tambayar wani tayi don Allah ina ofishin shugaba yake? Mutumin ya nuna mata da  yatsa, ta ciro  wayarta ta qira captain sadiq cikin tsawa take Magana pls kuyi sauri kuzo ina Gombe Line, na baku minti 5 bata jira meye zaice ba ta kashe wayarta tana tsaki, harta kama hanya zata nufi ofishin da aka nuna mata ta fasa ta  yanke shawarar jiran captain sadiq. Captain sadiq cikin gida ya shiga ya fadawa Anty akan MISRA ta qirashi… anty ta fara yi masa masifa meyesa kabarta ta fita ita kadae? Captain sadiq yace Wallahi zagina tayi – tayi kuma tace ba zamu bita ba, anty tace ai shikenan saika hanzarta kuje, indae wani abu ya sameta kayi kuka da kanka. Captain sadiq juyawa yayi tare da sauran sojojin farar mota qirar hilux suka shga da sauri, gudu sukeyi mutane suna buda musu hanya, basu jima ba suka iso inda suka hango MISRA tana tsaye a bakin wata mota, har zatayi musu masifa akan sun jima sai kuma ta share kawai, tayiwa sadiq bayanin komai, da sadiq da sauran sojojin ofishin shugaba suka nufa MISRA tana take musu baya, suna shiga babu ko sallama suka cakomo Umar shugaba, direbobi nawane masu jar mota a wannan tashar? Maganar tana shashaqewa yace su 2 ne, sukace muje ka nuna mana su, duk sauran direbobi da fasinjoji sai mamaki sukeyi yadda sukaga an cakwame shugabansu. Wurin motar Malam Musa ya kaisu  aka duba akaga baya nan, tsawa captain sadiq ya daka masa gidan ubanwa yaje to? Umar yace a a yana nan yanzu ma ya ajiye motar baeyi nisa ba, ka sakeni musan ta inda za a nemosa, MISRA ce ta bashi umurni tukunna ya sakeshi, ciro sanduna sukayi a bayan motarsu suka fara bugun motar malam Musa sukayi mata kaca - kaca, banda injin babu abnda zaiyi amfani a motar duk ta lalace lokaci daya, malam musa yana kan lissafinsa, zan bawa tanimu dari biyar ya bini bashin dari biyu, in biyawa uzairuna kudin makarnta dari biyar, dari uku in saka mai a aikin mota na aikin gobe, Allah gobema ka bani sa a irin ta yau  amin Alhamdillah Rabbil Alamin, yana gamawa akace yawwa gashin nan inji wani baqin direba, ya riqo wuyan rigar malam Musa, yana cewa munafuki ashe kasan tsiyar daka shuka kazo ka 6uya a nan, Malam musa cikin mamaki malam yaya dae? Meye na maka? Wancan mutumin yana jan malam musa da qarfi muje mana duk munafurcin daka shuka zaka girbe aii, malam musa tun yana kallon abun a wasa, harya fara masifa kafin nan ma sun kusa isowa, suna qarasowa, malam musa ya hada ido da MISRA ya sunkuyar da kai, ya sake daga ido kenan sai yaga yadda akayi masa da mota, ya bude baki yace SUBHANALLAH, captain sadiq yace ur highness shine? MISRA ta daga masa kai alamar eh, sadiq yana isowa ya naushi bakin malam musa saida ya zube nan take haqorinsa daya ya fadi qasa, nan jini yace ai nima gani ya fara gangarowa kamar famfon da aka bude ruwa, wani soja ne ya qara dauko malam musa daga qasa ya naushe shi a ciki, malam musa yana nishi yana cewa wayyo Allah karku kasheni kubari inga uzairuna da mata ta, daya sojan yayi tsakii ya sake taka kan malam musa, saida yayi wata irin qara da saida ya bawa kowa tausayi a wurin, kowa ya dauka sun barshi kenan, sanduna suka qara daukowa, duka sukeyi kota ina, tun malam musa yana ihu harya daina, yana salati, salatin ma ya gagara, umar shugabane yaje ya durqusa a gaban MISRA yace ki duba girman Allah kice su barshi haka Wallahi zai mutu, idan ya mutu kuma zan shiga hatsari, MISRA cikin fushi tace kai kasan ni yar wayece? Bari in kasheka in kasheshi inga abunda zai faru, kai kasan meye  yayi min? mutane suka kewaye su sukace duk abunda yayi miki kiyi haquri, MISRA duk rashin mutuncinta indae mutane suka taru sukace ta bari ko tayi  haquri wannan halintane amma banda mutum daya, dagawa sadiq hannu tayi. Hey ya isa barshi haka, gobema wani shege ya qara zagina marassa mutunci kawai, ta wuce ta nufi motarta, umar shugaba ya durqusa yace mungode hajiya ko kallansa batayi ba,  suma su captain wucewa sukayi suka shga motarsa suka fita, wanine yazo ya ta6a kirjin malam musa yaji yana numfashi amma sama  - sama, yace shugaba akaishi asibiti, umar yace babu ubanda zai kaishi ai shine ya jawowa kansa kullum ana gargadinku akan zagi idan kuna tuqi bakwaji kundai ga darasi aii. Ya wuce ya nufi hanyar komawa ofishinsa, lubabatuce da bata wuce shekara 6 zuwa 7 ba tana tafe tana yekuwan a sayi ruwa mai sanyi mai tsafta! a sayi ruwa mai sanyi mai tsafta!, ta qariso wurin don ta ganewa idonta meye yake faruwa dakyar ta kutsa ta shiga wurin, tana shiga ta hada ido da malam musa, wata uban qara mai firgitarwa tayi tare da fadin baban uzairu! Lah baban uzairu! Na shiga3 bari inyi sauri inje in fada a gida. 


By Shining stars Writersss

Ruqayya Gambo Awe (Ummi polis)

Maryam Muhammad Wakili (Ameera Yola)

Sakina Usman Rijau (Maman Ihsan)

Hizbatullah Ashafa. (Hizba baby)

0 Response to "Azabtacciyar Soyayya Hausa Novels"

Post a Comment