NERSI: Yadda Za Ku Bincika Ko Kun Cancanci Samun Tallafin N50,000 Na Gwamnatin Tarayya
NERSI: Yadda Za Ku Bincika Ko Kun Cancanci Samun Tallafin N50,000 Na Gwamnatin Tarayya
Shin kun ji labarin tallafin kuɗi naira dubu hamsin (₦50,000) da Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ke bayarwa ga wasu talakawa da iyalai masu ƙaramin ƙarfi a ƙarƙashin shirin NERSI?
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI) domin tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi da waɗanda ke cikin mawuyacin hali sakamakon tsadar rayuwa.
A ƙarƙashin wannan shiri, waɗanda aka zaɓa za su samu tallafin kuɗi na ₦50,000 sau ɗaya, wanda za a tura kai tsaye zuwa asusun ajiyar kuɗin wayarsu (Mobile Wallet).
Yadda Za Ku Bincika Ko Kun Cancanci Samun Tallafin N50,000
Domin bincika ko kuna cikin waɗanda aka zaɓa domin amfana da tallafin, za ku iya amfani da lambobin USSD na kamfanonin da ke gudanar da biyan kuɗin.
Ga lambobin da za ku yi amfani da su:
1. ALAT by Wema Bank
Ku danna:*945*23#
2. MoMo PSB
Ku danna:*671*0#
3. NairaGram
Ku danna:*726*00#
Bayan danna lambar da ta dace da kamfanin da kuke amfani da shi, ku bi umarnin da zai bayyana a wayarku, sannan ku zaɓi zaɓin Check Eligibility domin bincika ko an zaɓe ku.
Idan Ba Ku Cikin Waɗanda Aka Zaɓa Fa?
Idan ba a zaɓe ku ba a wannan zangon rabon tallafin, za a sanar da ku ta hanyar saƙon da zai bayyana a wayarku cewa ba a zaɓe ku a halin yanzu ba.
Sai dai kada ku yanke ƙauna, domin ana gudanar da rabon tallafin ne a matakai daban-daban, kuma ba kowa ne zai samu saƙon sanarwa a lokaci guda ba.
Waɗanne Mutane Ne Suka Cancanci Samun Tallafin?
Bisa bayanin da hukumar shirin ta wallafa, ana zaɓar waɗanda za su amfana ne daga sahihan bayanan rajistar al'umma masu ƙaramin ƙarfi (National Social Register) da kuma bayanan tantance shaidar zama ɗan ƙasa.
Haka kuma, ba a buɗe rajistar neman wannan tallafi ga kowa ba, kuma babu wani mutum da zai iya saka sunanka cikin jerin waɗanda za su amfana ta hanyar karɓar kuɗi.
Muhimman Gargadi Ga Masu Neman Tallafin
Samun wannan tallafi kyauta ne, babu kuɗin rajista.
Kada ku biya wani mutum domin ya saka sunanku cikin jerin waɗanda za su amfana.
Kada ku bai wa kowa PIN, OTP ko kalmar sirrin asusunku.
Ku guji danna hanyoyin intanet da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Kada ku tura kuɗi ga duk wanda ya ce zai taimaka muku wajen karɓar tallafin.
Lambar Tuntuɓa Domin Karin Bayani
Idan kuna buƙatar ƙarin bayani game da shirin NERSI, za ku iya kiran layin taimako na hukuma:
NERSI Helpline: 0700-022-2222
Haka kuma, za ku iya ziyartar shafin hukuma domin samun cikakkun bayanai:
https://www.fmhapr.gov.ng/nersi/
Allah Ya sa mu dace, Ya kuma sanya alheri a cikin wannan tallafi. Amin. 🤲
0 Response to "NERSI: Yadda Za Ku Bincika Ko Kun Cancanci Samun Tallafin N50,000 Na Gwamnatin Tarayya"
Post a Comment