SPO, PO, APO, RAC Manager da RATECH: INEC Ta Bude Shafin Daukar Ma’aikatan Wucin Gadi (Ad-Hoc Staff) na Zaben 2027
SPO, PO, APO, RAC Manager da RATECH: INEC Ta Bude Shafin Daukar Ma’aikatan Wucin Gadi (Ad-Hoc Staff) na Zaben 2027
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shirya daukar ’yan Najeriya da suka cancanta domin aiki a matsayin ma’aikatan wucin gadi (Ad-Hoc Staff) a babban zaben shekarar 2027.
Ayyukan sun hada da SPO, PO, APO, RAC Manager da RATECH. Ana gudanar da neman aikin ne ta yanar gizo, kuma kyauta ne.
Mukaman da ake da su
SPO – Supervisory Presiding Officer
PO – Presiding Officer
APO – Assistant Presiding Officer
RAC Manager – Registration Area Centre Manager
RATECH – Registration Area Technical Support
INEC kan dauki daliban manyan makarantu, masu yi ko wadanda suka kammala NYSC, ma’aikatan gwamnati da masu ilimin ICT, gwargwadon sharuddan kowane mukami.
Abubuwan da ake bukata
Masu sha’awar neman aikin su tanadi:
Adireshin email mai aiki
Lambar waya
Hoton fasfo na baya-bayan nan
Ingantaccen katin shaida
Shaidar karatu
Bayanan asusun banki
Katin dalibi ko na ma’aikaci, idan ya dace
Bayanan NYSC, idan ana bukata
Sunaye da bayanan mutane biyu da za su zama referees
Mai neman aikin ya tabbatar da cewa duk bayanan da ya bayar gaskiya ne kuma cikakku ne.
Yadda ake neman aikin
Shiga shafin INECPRES: pres.inecnigeria.org
Tabbatar cewa an bude neman aikin zaben 2027.
Duba mukaman da ake da su da sharuddan su.
Yi rajista sannan ka cike fom din neman aikin.
Loda takardun da ake bukata da hoton fasfo.
Sake duba bayanan da ka shigar kafin turawa.
Bayan kammalawa, ajiye ko buga Acknowledgement Slip.
Muhimmin gargadi
Masu neman aikin su rika amfani da shafin INEC na hukuma kawai. Kada a biya wani mutum kudi domin samun aikin INEC, domin neman aikin kyauta ne.
Haka kuma, kafin neman aikin, yana da kyau a tabbatar da ranar bude da ranar rufe daukar ma’aikatan 2027 kai tsaye daga shafin INECPRES.
Ku ci gaba da bibiyar Haskenews domin samun sabbin bayanai kan ayyukan yi, tallafin karatu, horo da sauran damammaki a Najeriya.
0 Response to "SPO, PO, APO, RAC Manager da RATECH: INEC Ta Bude Shafin Daukar Ma’aikatan Wucin Gadi (Ad-Hoc Staff) na Zaben 2027"
Post a Comment