-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
FG Ta Bude Gasar Creative Minds 2026 ga Matasa ’Yan Najeriya

FG Ta Bude Gasar Creative Minds 2026 ga Matasa ’Yan Najeriya

FG Ta Bude Gasar Creative Minds 2026 ga Matasa ’Yan Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta bude gasar Creative Minds Contest 2026 domin bai wa matasa ’yan Najeriya masu basirar kirkire-kirkire damar nuna hazakarsu.

Ma’aikatar Matasa ta Tarayya ce ta shirya gasar tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Fasaha, Al’adu, Yawon Bude Ido da Tattalin Arzikin Kirkire-kirkire, da Initiative for Self Esteem Education and Advocacy (ISEEA).

Taken Gasar

“Lived Experiences Heard, Real Voices, Real Change”

Gasar na mayar da hankali kan darajar kai (self-esteem) da lafiyar kwakwalwa (mental health), tare da karfafa matasa su yi amfani da fasaha wajen yada sakonni masu kyau da kuma rage kyama da rashin fahimta game da lafiyar kwakwalwa.

Bangarorin da ake karba

Ana karbar ayyukan kirkire-kirkire a fannoni hudu:

  1. Film – bai wuce mintuna 5 ba.

  2. Music

  3. Spoken Word

  4. Visual Arts – zane, digital illustration, daukar hoto da graphic design.

Waɗanda Za Su Iya Nema

Mai nema dole ne:

  • Ya kasance dan Najeriya.

  • Ya kasance tsakanin shekaru 15 zuwa 35.

  • Ya gabatar da aikin da ya kirkira da kansa.

  • Aikin bai taba lashe wata babbar gasa ko lambar yabo ta kasa ba.

  • Aikin ya kasance yana da alaka da self-esteem da mental health.

  • Aikin ya dace da taken gasar.

Kyaututtukan Gasar

  • 🥇 Matsayi na 1: ₦200,000

  • 🥈 Matsayi na 2: ₦150,000

  • 🥉 Matsayi na 3: ₦100,000

Ranar Rufe Neman Shiga Gasar

5 ga Oktoba 2026

Za a gudanar da Dinner and Awards Night a Abuja ranar 23 ga Oktoba 2026, inda za a bai wa wadanda suka yi nasara kyaututtukansu.

Yadda Ake Nema

Masu sha’awar shiga gasar su cike fom din neman shiga sannan su loda aikinsu na asali kafin ranar rufe gasar.

Creative Minds Contest Application Form

Lura: A tabbatar da cewa aikin da aka tura na mutum ne da kansa kuma ya cika dukkan sharuddan gasar kafin gabatar da shi.

0 Response to "FG Ta Bude Gasar Creative Minds 2026 ga Matasa ’Yan Najeriya"

Post a Comment