-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
 LABARI MAI DAƊI GA MANOMA: An Fara Amincewa da Sunayen Wadanda Suka Cike Shirin NAMP na Bankin Noma (BOA)

LABARI MAI DAƊI GA MANOMA: An Fara Amincewa da Sunayen Wadanda Suka Cike Shirin NAMP na Bankin Noma (BOA)

 LABARI MAI DAƊI GA MANOMA: An Fara Amincewa da Sunayen Wadanda Suka Cike Shirin NAMP na Bankin Noma (BOA)

Ana sanar da dukkan waɗanda suka nemi shiga shirin National Agricultural Mechanization Program (NAMP) cewa an fara bayar da amincewa (Approval) ga wasu daga cikin waɗanda suka cike shirin ƙarƙashin Bank of Agriculture (BOA).

Shirin NAMP wani babban tsari ne da Bankin Noma ya ƙaddamar domin bunƙasa harkar noma ta zamani a Najeriya ta hanyar amfani da injuna, tractors, da sauran manyan kayan aikin noma.

A cewar bankin, an tsara shirin ne domin aiwatarwa a mazabu 360 na tarayya a faɗin Najeriya, inda ake sa ran zai shafi noma a sama da hekta miliyan 1.2 na filayen noma.

Haka kuma, shirin zai haɗa da rabon tractors 2,000 da sauran kayan aikin noma domin ƙara yawan samar da abinci, rage talauci, da samar da ayyukan yi ga matasa a faɗin ƙasar.

Shugaban Bankin Noma, Ayo Sotinriade, ya bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen sauya tsarin noma daga na gargajiya zuwa noma na kasuwanci, tare da rage matsalolin ƙarancin abinci da rashin tsaro.

Muhimmiyar Sanarwa:

Duk wanda ya nemi shiga wannan shiri kuma yake son ƙarin bayani ko tabbatar da matsayinsa, ana shawartar sa da ya ziyarci reshen Bank of Agriculture mafi kusa domin samun sahihan bayanai.

Domin samun sabbin labarai kan tallafin gwamnati, noma, da guraben aiki a kullum, ku ci gaba da bibiyar shafinmu na Haskenews.com.ng.

0 Response to " LABARI MAI DAƊI GA MANOMA: An Fara Amincewa da Sunayen Wadanda Suka Cike Shirin NAMP na Bankin Noma (BOA)"

Post a Comment