Za a fara rajistar shiga rukunin 'Batch B' na shirin YEIDEP a ranar 9 ga watan Maris, 2026
Za a fara rajistar shiga rukunin 'Batch B' na shirin YEIDEP a ranar 9 ga watan Maris, 2026
Za a fara rajistar shiga rukunin 'Batch B' na shirin YEIDEP a ranar 9 ga watan Maris, 2026. Da zarar an buɗe shafin rajistar, zan sanar da ku.
Bisa sanarwar da shugaban shirin na ƙasa (Coordinator-General), Kennedy Iyere ya fitar, za a gudanar da aikin ɗaukar sabbin waɗanda za su amfana da shirin a faɗin ƙasar nan ta hanyar yanar gizo.
Sai dai a Jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai jagoranci tsarin ta hanyar wani sabon Kwamitin Gudanarwa na YEIDEP na Jihar Kano, wanda aka ba wa alhakin daidaitawa da kuma kula da zaɓen masu cin gajiyar shirin a jihar.
Sanarwar ta ƙara bayyana cewa mutanen da suka yi rajista a rukunin 'Batch A' kuma suka riga suka mallaki tabbataccen asusun banki na YEIDEP, ba su cancanci sake shiga wannan sabon shirin ba.
To sai dai kuma, waɗanda suka yi rajista a 'Batch A' amma ba su samu nasarar buɗe tabbataccen asusun YEIDEP ba, ana ƙarfafa musu gwiwar su sake nema a rukunin 'Batch B'.
0 Response to "Za a fara rajistar shiga rukunin 'Batch B' na shirin YEIDEP a ranar 9 ga watan Maris, 2026"
Post a Comment