Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Harkokin Matasa (Federal Ministry of Youth Development), tare da haɗin gwiwar kamfanin SAMU Technology da Ƙungiyar Masu Harkar Sarrafa Shara ta Najeriya (RAN), tana sanar da buɗe sabon shiri na musamman mai taken Circular Economy Youth Empowerment Initiative (CEYEI).
Wannan shiri, wanda aka yi wa laƙabi da Waste Management Empowerment Program, an tsara shi ne domin koyar da matasan Najeriya dabarun zamani na sarrafa shara domin samun arziki (Recycling/Waste to Wealth).
Shirin zai shafi dukkan jihohin Najeriya 36 da kuma ƙananan hukumomi 774, domin tabbatar da cewa matasa daga kowane lungu da saƙo sun samu damar amfana da wannan horo.
Ana kiran dukkan matasa masu sha'awar shiga wannan shiri da su hanzarta cike fom ɗin neman shiga ta hanyar danna mahadar (link) da ke ƙasa:
👉 Danna nan domin cikewa: https://wastetowealth.fmyd.gov.ng
Allah ya bada sa'a.
0 Response to "Hanzarta ku cike: Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Sabon Shirin Koyar Da Sana’o’i Ga Matasa (CEYEI)"
Post a Comment