-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
Yadda Zaku Cike Aikin Sojan Saman Najeriya (Nigerian Air Force)

Yadda Zaku Cike Aikin Sojan Saman Najeriya (Nigerian Air Force)

Yadda Zaku Cike Aikin Sojan Saman Najeriya (Nigerian Air Force)

Hukumar Sojan Saman Najeriya (Nigerian Air Force) ta fara ɗaukar sabbin sojoji ga waɗanda suka kammala karatun digiri ko HND, wato ba na waɗanda suka gama sakandare ba, sai dai na masu digiri da kuma HND. Ana kiran wannan Direct Short Service Commission.

An buɗe shafin yin rajistar ne tun ranar 27 ga watan Agusta, kuma za a rufe shi ranar 7 ga watan Oktoba 2024 na wannan shekarar. Don haka, duk wanda yake da sha'awa zai iya ziyartar shafin domin cikawa.

https://nafrecruitment.airforce.mil.ng/ Sai ka shiga inda aka rubuta DSSC, ka danna, sannan ka buɗe profile. Bayan haka, za ka koma ka ci gaba da cikawa.

Daga cikin abubuwan da ake buƙata, ya kasance ba ka da aure, sannan kai ɗan Najeriya ne mai shekaru tsakanin ashirin zuwa talatin. Bugu da ƙari, dole ne ka mallaki sakamakon "Second Class Upper Division" ko kuma "Credit" daga makarantun da aka yarda da su. Sannan kuma dole ne ka samu takardar shaidar kammala NYSC (discharge certificate), domin ba tare da ita ba, ba za ka iya cikawa ba.

Allah ya bada sa'a.

0 Response to "Yadda Zaku Cike Aikin Sojan Saman Najeriya (Nigerian Air Force)"

Post a Comment