-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
Shirin Horas da Matasan Najeriya a Sana’o’in Hannu: Gwamnatin Tarayya da ITF Sun Kaddamar da "Skill-Up Artisans (SUPA)"

Shirin Horas da Matasan Najeriya a Sana’o’in Hannu: Gwamnatin Tarayya da ITF Sun Kaddamar da "Skill-Up Artisans (SUPA)"

Shirin Horas da Matasan Najeriya a Sana’o’in Hannu: Gwamnatin Tarayya da ITF Sun Kaddamar da "Skill-Up Artisans (SUPA)"

Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar Hukumar Industrial Training Fund (ITF), ta kaddamar da shirin horar da matasan Najeriya a fannoni daban-daban na sana’o’in hannu domin ƙarfafa dogaro da kai. Shirin ya kasu gida uku:

  1. Ƙwararrun Masana (Skilled Artisan) – Wadanda ke da ƙwarewa a wata sana’a kuma suke son shiga shirin.
  2. Masu Sha’awar Koyo (Intending Artisan) – Wadanda ke son koyon sabuwar sana’a.
  3. Cibiyoyin Horaswa (Training Center) – Masu bada horo a fannin sana’o’in hannu.

Bayan kammala shirin, mahalarta za su sami takardar shaidar kammalawa tare da tallafin fara kasuwanci domin su ci gaba da aikin da suka koya.  

Sana’o’in da za a koyar sun haɗa da:  

- Gina da Gine-gine (Building and Construction)  

- Gudanar da Masauki da Otal (Hospitality Management)  

- Harkar Wutar Lantarki (Power)  

- Fata da Kayan Fata (Leather Works)  

- Noma da Harkokin Noma (Agric/Agro Allied)  

- Zanen Kaya da Dinki (Fashion Design)  

- Fannin Kwamfuta da Sadarwa (ICT)  

- Sana’o’in Hannu da Fasaha (Arts and Crafts)  

- Gyaran Kayan Amfani (Appliance Service Technician)  

- Kawata Ciki da Tsara Gida (Interior Design)  

- Gyaran Motoci (Vehicle Auto Services)  

- Kula da Fata da Kyau (Cosmetology)  

- Gudanar da Muhalli da Tsare-tsare (Facility Management and Planning)  


Yadda Za Ku Cike  

Domin cike wannan dama, ku latsa shafin yanar gizo a ƙasa:  

Latsa nan ➝ https://supa.itf.gov.ng


Allah Ya sa mu dace, baki ɗaya!


0 Response to "Shirin Horas da Matasan Najeriya a Sana’o’in Hannu: Gwamnatin Tarayya da ITF Sun Kaddamar da "Skill-Up Artisans (SUPA)""

Post a Comment