-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya 2025

Kalaman Soyayya 2025

Kalaman Soyayya 2025



Assalamu alaiki ya ke sarauniyar Zuciyata Na Zo miki da Sakon jaddada soyayyata da kauna zuwa gareki yake sahibata


Banda wani sukuni ko walwala a rayuwa ta face Samun yaddar ki Kuma in Samu kashi Dari acikin soyayyar ki Domin banda wani Muhimmanci a rayuwata idan Har ban sameki a Matsayin masoyiya ba Duba da irin kyakkyawan halayenki da kowa ke burin ya kasance tare dake. Hakika tun ranar da Allah ya haskamin kyakkyawan fuskar nan taki ban taba kwana cikin farin ciki irin na wannan ranar ba Domin kuwa acikin dare furkarki ta Bayyana a gareni amma ji nake kamar sha biyu na rana ne irin hasken da ya Bayyana a wannan lokacin Kuma hasken a Zuciyar ki da fuskarki yake marmasowa.


Na Jima ina burin Samun Mace mai irin sura da nasaba mai kyau irinki sabida da yawan samarin gari kowa baida wani buri face yaga ya kulla koda alakar yini gudace tsakaninku Dashi amma Abin yaci tura hakan baisa na ja daga bayaba Kuma nayi kasa a guiwa wajen kawo miki sakon soyayyaya ta zuwa gareki Domin inzama Dan gani kashenin ki a fannin soyayya, kauna da Kuma kulawa ta fannin so. Zuciyata sai tafasa takeyi idan Har na tuna watarana akwai ranar da zaki iya tafiya mai nisa dani inji ina ma ace zamu tsaya a wannan doron kasar muyi soyayya ni dake wacce batada karshe a tsakaninmu da Ni zanfi kowa farin ciki da Samun wannan dilleliyar dama da na jima ina burin Samu a rayuwata ta kasancewa a tare dake na Har abada.


Mi zai hana kibani damar kafa tubalin soyayyaya ta acikin tsakiyar birnin zuciyarki Domin haka gini da wannan tubalin koda zan Samu ma'adanin kafa zuciyata mai dauke da soyayyar ki ya ke mai raya zuciyata. Banson nayi fada da kowa a rayuwata amma idan anason aga fada na lalle a tabamin ke ma'ana duk lokacin da aka bata miki rai lalle ya zama wajibi inshiga in fita wajen Neman duk Wanda yayi sanadiyar bacin ranki Domin daukar masa matakin Gaggawa. Kuma wannan matakin ba hukumar yansanda ba, ba ta sojoji ba, ba ta alkalai ba Nine zanyi nawa mummunan hukunci akanshi sabida ya taba kyakkyawar da tabin ta ba karamin kalubale bane ga Mutum Kai Har ma aljani da ba'a ganin shi a shirye nake da Mu fafata Dashi wajen nema miki yancinki a Matsayinki na wacce ke Zuwa tana dawowa acikin zuciyata.


Na shirya bada duk wani Lokaci da nake Dashi Domin in raya soyayya ya Tsakani na dake Domin Mu rayu acikin farin ciki maras misaltuwa ta dalilin soyayya da amincewar juna a tsakanin Mu. Hakika nayi marhaba da zuwan soyayyar ki a zuciyata. Sannan banda wuni khaufi ko wani kalubale da zai dakatar dani daga barin soyayyar ki koda na minti Guda ne a rayuwata ya mai share kukana mai biyan bikatuna agogon da nake inkari Dashi in Duba lokacin da nake bacci da tashi a kowane awa mintuna da Sakan na zuciyata

0 Response to "Kalaman Soyayya 2025"

Post a Comment