-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Shirin Samar da Ayyuka 93,731 na Hukumar NDE: Yadda Zaku Duba Matsayin Aikace-aikacenku da Sauke Bayanan Aikace-aikacenku

Shirin Samar da Ayyuka 93,731 na Hukumar NDE: Yadda Zaku Duba Matsayin Aikace-aikacenku da Sauke Bayanan Aikace-aikacenku

Shirin Samar da Ayyuka 93,731 na Hukumar NDE: Yadda Zaku Duba Matsayin Aikace-aikacenku da Sauke Bayanan Aikace-aikacenku

Bayani kan Shirin "Creation of 93,731 Jobs Initiative"  

A karkashin Tsarin "Renewed Hope Agenda" na Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da rage talauci, Hukumar Samar da Ayyukan Yi (NDE) ta kaddamar da shirin koyar da sana'o'i da ake cikewa daga watan Oktoba zuwa Disamba 2024. Wannan shirin ya kunshi horar da mutane kan sana’o’i guda 30 don rage matsalar rashin aikin yi da karfafa samar da arziki a Najeriya. Domin tabbatar da cewa shirin ya samu tasiri ga jama’a a matakin kasa, ana aiwatar da shi ne a matakin mazabar zabe.  

Sanarwa ga masu neman shiga shirin:  

Wa'adin neman shiga shirin "Creation of 93,731 Jobs Initiative" ya riga ya wuce. Ana shawartar masu neman shiga su shiga shafukan su na yanar gizo don:  

  • 1. Duba matsayin neman aikin su.  
  • 2. Saukar da bayanan neman aikin da suka gabatar.  

Yadda Zaku Duba Aikace-aikacenku  

  • 1. Shiga shafin yanar gizon NDE: https://nderegistrationportal.ng/
  • 2. Shigar da Email da Password ɗin ku sannan ku latsa Login.  
  • 3. Bayan kun shiga, latsa View Programme Details.  
  • 4. A nan, za ku ga zaɓi mai suna Download Application Data; ku latsa don saukar da bayanan aikace-aikacenku.  

Allah Yasa Mu Dace Baki Daya 

0 Response to "Shirin Samar da Ayyuka 93,731 na Hukumar NDE: Yadda Zaku Duba Matsayin Aikace-aikacenku da Sauke Bayanan Aikace-aikacenku"

Post a Comment