-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

ƙididdigar marasa aikin yi a Najeriya ya ragu, cewar NBS

ƙididdigar marasa aikin yi a Najeriya ya ragu, cewar NBS

ƙididdigar marasa aikin yi a Najeriya ya ragu, cewar NBS

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa a Najeriya NBS ta fitar da rahoton da ke bayyana cewa an samu ragin matasa da ke fama da rashin aikin yi da kashi 4.1 cikin 100 wata uku na farko na wannan shekara.

Alkaluman rashin aikin yi a baya ya kai maki 33.1 cikin 100 a rahotonta na ƙarshe da ta fitar a ƙarshen 2022.

Hukumar NBS kafin wannan lokaci ta ce za ta yi amfani da dabarun fasahar zamani wajen tabbatar da haƙiƙanin alƙaluman ma'aikata da kuma marasa aikin yi a faɗin ƙasar.

A lokacin kaddamar da sabon tsarin fasaha a Abuja, NBS ta ce sabbin alkalumanta za su yi gogayya da irin waɗanda ake gani a ƙasashen Turai wajen sahihanci.


Source BBCHausa

0 Response to "ƙididdigar marasa aikin yi a Najeriya ya ragu, cewar NBS"

Post a Comment