-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake Zama Da Mata Ma'aikaciyar Gwamnati

Yadda Ake Zama Da Mata Ma'aikaciyar Gwamnati

Yadda Ake Zama Da Mata Ma'aikaciyar Gwamnati

A kullum Zama idan ya hadaka da mutum dole ne sai an saka hakuri aciki kowane irin Zama ne kuwa. Mata ko wacece bata aikin gwamnati ce a gida kawai take zaune sai kayi hakuri talkless of ace kullum fita takeyi a gaskiya idan anyi duba a wani bangare zaa aga cewa miji ya fita kuma mata ta fita kenan ba kowa a cikin gida idan b yara b idan kuma bakuda yara shikenan kullum gidanku a rufe yake a magana ta gaskiya idan kowa Yana fita aiki akasari baka sanin halin da yara suke a gida saboda kullum su kadai ke yini a ciki sannan kula da tarbiyar su zaiyi karanci koda kuwa ace kina jajircewa ki tsaya ki binciki abubuwan da suka gudana alokacin da bakyanan dole wani abu dai zai ragu naga tarbiyar yayanki idan anyi duba zamanki a gurin aiki yafi zamanki a gida yawa sannan Mijinki baya samun time dinki Yanda ya kamata zaiji a ranshi shi wai kullum matarsa tana waje kuma zatayi muamala harda maza irin dai wasu tunani duk zasu kama shigo shi wanda bazai ji dadi a ransa ba saboda irin wadannan abubuwan ne wasu mazan basa bari matansu suyi aikin gwamnati sai dai dan kasuwanci haka a cikin gida Amma ga shawara ga mazaje wadanda suke da mata maaikatan gwamnati shi hakuri dole ne sai kayi shi shine abu na farko da zakasa a gaba sannan ka kai zuciyarka nesa sannan kada ka nuna wa matarka aikin da takeyi bakajin dadi hakan zaisa abun ya fita zanta ka Zama mai encouraging nata a koda yaushe domin aikin da takeyi ai harda kai Yana amfana domin zata rage maka nauyi na gidanka duk wani little things da zatayi a gidan bazaka ma sani b kawai zaka tanayin abunta ne Amma idan ba aikin bazata samu kudin dazatayi wannan ba dole sai ka bayar tau  ko hakan kadai ai ka amfana sannan zakayi hakuri da yanayin girki ba a koda yaushe ne zaka samu Yanda kakeso ba watarana ma zaka iya tatar da gidan ba abinci maybe ko tayi late a zuwa aiki bata samu tayi ba ko kuma sometimes idan tanada yara wadanda suka dan girma haka more especially mata idan tayi late zata iya barwa yara su dafa abincin kuma kaga abincin bazaiyi dadi Kamar Yanda ita zata tsaya ta girka ba so all this sai mutum yayi hakuri sannan ya dauka yanayi ne kuma lalura ce ta kama shiyasa hakan ke faruwa ai idan kayi laakari ai idan bata zuwa koina duk wannan bazai faru ba so ka dauka bakomai bane sai ku samu zamantakewa mai kyau tare da yayanku Zama da Mace Maaikaciyar Gwamnati bashida aibu sannan a cikin kashi dari tana ragemaka kusan 40-50 percent na dawainiyar gidanka da yayanku sai dai Kamar Yadda na fada a baya dole zai zamana yanada aibu ko kadan ne idan akayi duba a wani bangaren Amma still kayi supporting nata a kullum ka karfafa mata gwaiwa sai taji dadi a ranta saboda kanason abinda takeso daga nan kun samu zaman lafiya mai dorewa a tare Allah yasa mudace

0 Response to "Yadda Ake Zama Da Mata Ma'aikaciyar Gwamnati"

Post a Comment