-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Munyi iya bakin kokarinmu wajen kawo karshen yajin aikin ASUU- Gwamnatin tarayya

Munyi iya bakin kokarinmu wajen kawo karshen yajin aikin ASUU- Gwamnatin tarayya

Munyi iya bakin kokarinmu wajen kawo karshen yajin aikin ASUU- Gwamnatin tarayya

Gwamantin tarayyar Najeriya ta ce ta yi iya bakin kokarinta domin ganin an kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'in kasar ta ASUU ke gudanarwa.

Ministan ilimi na kasar Mallam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja babban birnin kasar, a yayin da ake ci gaba da ganawa da shugabanni da iyayen jami'o'in gwamnatin tarayya a harabar hukumar kula da jami'o'i ta kasar.

Kawo yanzu dai an shiga ganawar sirri game da zaman, ana kuma sa ran Ministan zai yi wa manema labarai jawabi a karshen ganawar.

Adamu Adamu ya ce ''Abin da muke yi shi ne aiki da umarnin da shugaban kasa ya ba mu na cewa, a yayin da ake kokarin jawo hankalin ASUU da su koma bakin aikinsu, gwamnati ba za ta sake maimaita kura-kuran da ta yi a baya ba, na amincewa da sanya hannu kan yarjejeniyoyin da ta san ba za ta iya aiwatar da su ba''

''A kokarin shawo kan matsalolin yau, ba za mu shuka wa kanmu matsalolin da ba za mu iya girbinsu gobe ba'', in ji Ministan

Source: Jaridar BBCHAUSA


0 Response to "Munyi iya bakin kokarinmu wajen kawo karshen yajin aikin ASUU- Gwamnatin tarayya"

Post a Comment