-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya na Hausa

Kalaman Soyayya na Hausa

Kalaman Soyayya na Hausa

SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.

Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki! HMM!! KI YARDA DA NI. A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.

ZAN SO KI JI. Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki! KE CE MURMUSHI NA. Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.

Na maza KIN ZARCE SAURAN MATA Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki. SINADARIN RAYUWA TA. SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.

DAKE NAKE

Dukkanin abinda zakiji daga gareni babu Karya ko niyyar yaudara a cikinsu yanxu ko kuma a chan gaba,Gundarin abinda maganata zuwa gareki zata kunsa KALMAR SO che,amma fa idan zaayi mata gunduwa gunduwa bani tsammanin zan iya warware maki zare da abawa,RANKI YA DADE kamar da wasa kyakykyawar tarbiyyarki ta saKa min SONKI a cikin zuciyata a cikin Kankanin lokachi,idan da zan samu yanda nake so DAKE NAKE fatan shiga babban dandalin masoya na wannan duniyar da kuma wanda ke a Kiyama,koda ban samu yanda nake so ba ina fata zaki rubuta sunana a madaukakiyar fadar zuciyarki a matsayin masoyi mai daraja koda bata farko Dukkanin abinda zakiji daga gareni babu Karya ko niyyar yaudara a yanxu ko kuma a chan gaba,Gundarin abinda magana zuwa gareki zata kunsa KALMAR SO che,amma fa idan zaayi mata gunduwa gunduwa bani tsammanin zan iya warware maki zare da abawa,RANKI YA DADE kamar da wasa kyakykyawar tarbiyyarki ta saKa min SONKI a cikin zuciyata a cikin Kankanin lokachi,idan da zan samu yanda nake so DAKE NAKE fatan shiga babban dandalin masoya na wannan duniyar da kuma wanda ke a Kiyama,koda ban samu yanda nake so ba ina fata zaki rubuta sunana a madaukakiyar fadar zuciyarki a matsayin masoyi mai daraja koda bata farko bace.

Sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har na ya kasance kin ci gaba da nuna rashin kulawarki a kaina

kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma'abota debe kewa da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min

kiyi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki, sonki ya gama shiga jikina.

kada ki bar ni shawagi tamkar tsuntsu a sararin SAMANIYA.

KALAMAN SACE ZUCIYA sukuma wadannan wasu dadadan kalamaine da akefurta su ga abar qauna a mabanbanta lokaci ko yananyi. Dandanon su yafi zuma dadi balle sukari ,sukan sanyaya zuciya ,sukan raunana zuciya ,sukan qarfafa zuciya ,sukan sa a sallamar da zuciya duka ,saboda shauqin su da saka masoyiya cikin

Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata! So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina!

Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke!

Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai!

Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni! Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata!

Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko da nike roqo samu!

Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi! Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata.




PROMO


YANDA ZAKA ZAUNA LAFIYA IDAN KANA DA BUDURWA BAHAUSHIYA

1. Karka taba tsammanin zata kira ka awaya idan ba haka ba zaka mutu kana jira.

2. Ka sani idan kace mata "I love you" ko ina sonki nagode kawai zata ce amma girmankai bazai barta tace maka I love you ba.

3. Karka taba tsammani zata fara maka magana idan tana online.

4. Idan ka tura mata love messages kar kayi tsammanin zata yi maka reply.

5. Kasani kai ke sonta, kuma kai zaka kula da ita, ita bazata iya yi maka komai ba.

6. Ko yaushe zata iya rabuwa da kai idan ta samu wanda yapi ka kudi.

7. Kasani cewa bakai kadai bane saurayinta.

Haqiqa idan kayi haka zaka zauna lapiya da budurwar ka bahaushiya.

Zaku Iya?

0 Response to "Kalaman Soyayya na Hausa"

Post a Comment