-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Gyaran nono ga bazawara ko budurwa

Gyaran nono ga bazawara ko budurwa

Gyaran nono ga bazawara ko budurwa 



Mai karatu, assalamu alaikum, mu na yi ma ka marhabin da zuwa shafinmu na "Lafiyar Iyali". Wannan shafi ya dukufa wajen kawo mu ku magunguna da za su taimaka wa ma'aurata samun farin ciki da nihsadi a zamantakewar aurensu.

A wannan makala za mu yi bayani dalla-dalla kan yadda mace za ta gyara nononta, ya dawo kamar na budurwa, kwarai kuwa, wannan ba wani abu ne mai wahala ba. Da zarar kin yi amfani da wanna hadin, nononki zai koma ya tsaya cak kamar na budurwa.

Abu na gaba kuma sai wani hadi ga mata ma su fama da karanci ko rashin ni'ima gaba daya. "Lafiyar Iyali" na samun bayanai daga 'yan uwa mata da yawa game da yadda su ke fama da rashin ni'ima yayin saduwar aure. Ga ma su fama da wanan matsala, sai mu ce, kayanku ya tsinke a gindin kaba.

Baya ga wannan akwai wani hadin da maza da mata za su iya amfani da shi don iya gamsar da juna yayin jima'i. Allah Ya sa mu dace, amin.

Ba tare da bata lokaci ba, za mu kawo mu ku yadda za ku yi wadannan hade-hade cikin sauki. Da fatan a sha karatu lafiya, da fatan kuma bayan an karanta za a jarraba.

Karanta: Amfanin Man Kwakwa Guda 11 Da Mutane Ba Su Sani Ba.

1. Gyaran Nono.

Wannan wani hadi ne da masana kiwon lafiya su ka samar bayan gudanar da zuzzurfan bincike. Kuma babban abin farin ciki game da wanan hadi, baya ga saukin hadawar sa, an jarraba an ga fa'idarsa, sannan ba shi da wata illa ga lafiyarmu, saboda dukkan kayan hadin dangogin abincin da mu ke ci yau da kullum ne.

Abubuwan Da Ake Bukata:

a. Hulba

b. Gyada.

c. Alkama

d. Ridi

e. Shinkafa

f. Karas

Wadannan kayan abinci ake bukata mace ta tanada. Abin da za ta yi shine, ta samu garinsu. Abin nufi kamar shinkafa, sai ta gyara ta sosai ta daka ko nika yadda za ta samu garinta. Haka za ta yi wa gyada, ridi, da alkama. Ita kuwa hulba sai ta sayo garinta, shi kuma karas sai ta shanya shi ya bushe sannan ta samu garinsa.

Bayan ta sami garin wadannan abubuwa da mu ka ambata a sama, sai ta hada su waje guda ta gauraye, daga nan ta adana su a mazubi mai tsafta, kuma mai murfi.

Yadda za ta yi amfani da wannan hadin gyaran nono shine, za ta sami madara 'Peak' idan son samu ne, ta ke zuba wa ta sha a kullum. Za ta sha mamaki matukar ta juri amfani da wannan hadin gyaran nono, domin kuwa nononta zai dawo tamkar na budurwa, da iznin Allah. 

2.  Karin Ni'ima

Kamar yadda mu ka fada a sama ana samun mata da kan yi kukan rashin ni'ima, wanda hakan kan hana jin dadin jima'i tsakanin ma'aurata, sannan ya haifar da rashin gamsuwa tsakaninsu. Idan har kina fama da wannan matsala ko matar ka na fama da matsalar rashin ni'ima, sai ka karanta ka fada ma ta don ta hada, saboda a wannan harka ba kunya.

Kayan Hadin Da Ake Bukata:

a. Ruwan Kankana, Kofi 1 

b. Garin Dabino, babban cokali 3

c. Zuma, babban cokali 3

d. Madarar "Peak" rabin gwangwani.

Idan amarya ko uwargida ta tanadi wadannan abubuwa da mu ka ambata a sama, abin da za ta yi shine, za ta cakuda garin dabinonta da ruwan kankana da zuma, ta tabbatar sun gaurayu sosai, sai ta zuba cikin madararta, ta ke sha, da iznin Allah matsalarta za ta kau. Shi wannan hadin namiji ma zai iya amfani da shi.

3. Karin Ni'ima Da Gamsuwa Yayin Jima'i

Shi kuma wannan hadin, baya ga karin ni'ima da mace za ta samu, hakanan zai kara mata dadi yadda za ta iya gamsar da mijinta.

Kayan Hadin Da AKe Bukata:

a. Aya, babban cokali 5

b. Ridi, babban cokali 5

c. Cikwi, babban cokali 3

Yadda mace za ta yi wannan hadi shine, tun da farko za ta gyara ayarta, sannan ta soya ta, bayan haka sai ta daka ayar don ta samu garinta. Shi kuma ridi bayan ta gyara shi ta cire duk wani datti da ke cikinsa, sai ta nika shi don samun garinsa. Hakanan, shi ma cikwi za ta daka shi ne don samu garinsa.

Bayan ta samu garin wadannan abubuwa 3 da aka zayyana a sama, sai ta hada su waje guda ta gauraya su, ta tabbatar sun gaurayu sosai, sannan ta adana a mazubinta mai kyau.

Abu na gaba shine, ta samu madara ko nonon shanu mai kyau, sai ta ke zuba karamin cokali 2 cikin nonon ko madarar, ta ke sha safe da yanna a kowanne yini. Samun ni'ima da gamsuwa yayin jima'i ba sai an fada ba.

4. Karin Sha'awa.

Wasu matan kan yi kukan rashin sha'awar jima'i. Akan samu mata da ke fama da wannan matsala da har ta kai ta kawo, a dole ta ke saduwa da mijinta, amma ba wai don ta na da sha'awar jima'in ba. Da iznin Alla idan ta yi wannan hadin ta yi amfani da shi za ta kasance mai sha'awar jima'i.

Kayan Hadin Da Ake Bukata:

a.  Sassaken Baure, babban cokali 5

b. Kanumfari, babban cokali 3

c. Zuma, babban cokali 2

d. Lipton

Yadda za ta hada, za ta daka sassaken bauren bayan ta bar shi ya bushe don ta samu garinsa. Sai ta daka kanumfari, shi ma don ta samu garinsa. Za ta gauraya garin kanumfarinta babban cokali 3 da garin bauren babban cokali 5, bayan ta tabbatar sun gaurayu sai ta zuba zuma babban cokali 2 ta cakuda su, su cakudu sosai. Za ta debi karamin cokali daya na wannan hadi ta zuba cikin ruwan lipton ta sha sau biyu a rana. Sauran bayani mu na jiran amsar ki a sashen "Comment" na wannan shafi na "Lafiyar Iyali".

5.  Gamsar Da Maigida.

Kayan Hadin Da AKe Bukata.

a. Garin gero (Amma kar a surfa)

b. Garin furen(huda) tumfafiya babban cokali 3

c. Garin 'ya'yan zogale babban cokali 3.

Bayan an samu garin wadannan abubuwa sai a gauraya su, mace ta ke shan karamin cokali sau biyu a rana


0 Response to "Gyaran nono ga bazawara ko budurwa"

Post a Comment