-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Gyaran nono a sati daya

Gyaran nono a sati daya

Gyaran nono a sati daya

Barkarmu da yau, muna jin daɗin kasantuwa daku acikin wannan shafi namu mai daraja shafin Haskenews, ayau zamu amsa maku tambayarku da kuke aiko mana a ko yaushe wato Gyaran nono a sati daya.

Da farko dai wajibine ga remu mata mu sani cewa shifa Nono wata babbar kadarace da Allah subhanahu wata'ala yayi mana wadda take ban-bantamu da maza, kuma ya sanya shawar maza aciki don haka wajibine ne mu Kiyaye wannan ni'imar, ayau gyaran nono ko kiyayeshi ko kula dashi ya zama dole ga  kowace mace (budurwa, bazawara ko matar aure). So tari zakiga wata dazarar tayi aure an samu haihuwa daya, biyu sai kiga ta koma tamkar allo. Ki sani cewa zaki iya gyara nononki acikin sati daya ko kuma kasa da haka kuma yadawo tamkar a baya.

Idan kin kasance cikin masu kan-kanin nonuwa ko wadda nononta ya fadi to babu makawa kinzo wajanda za'a share miki hawayenki kuma kishigo cikin jerin mata. Batare da cikaku da surutuba zamu tsunduma acikin shirin na Gyaran nono a sati daya.

A kasa mun kawo maku hanyoyi biyar da zaku dawo da martabar nononku acikin Gyaran nono a sati daya, ki zabi hanya mafi sauki a wajanki kuma kiyi kamar yadda aka bayyana.

HANYA TA FARKO

  • kankana
  • gwanda
  • abarba

ayanka kanana a zuba aruwan zafi idan yayi laushi sai a shanye.

idan shayarwa akeyi man hulba cokali2 abi da zuma cokali1.

Idan ya zube ne a dafa hulba da yansun idan ya dafu atace,asha,sannan a kwaba hulbar da kwan salwa arika.Kafin shafawa.

HANYA TA BIYU

shima wanna wani hadine da akeyi don gyaran nono kuma yanada muhimmanci sosai , yanda akeyi shine za'a Samu

  • kindirmo
  • tumatur
  • lemun tsami
  • garin kubewa
  • da garin sallaja

Sai ki hadasu guri daya ki kwabasu ki rinka shafe nonon dashi, bayan kimanin 1hr ko minti 30 sai ki wanke ki shafe nonon da man ridi.

HANYA TA UKU

  •  Farar shinkafa
  • Garin Alkama
  • Garin habbatus sauda
  • Garin Ayaba (Plantain).
  • Gyada mai malfa (mai zabo)
  • Aya Madarar gari.
  • Zuma

Zaa bare bayan plantain sai a yanka shi, a shanya ya bushe, sai a daka, a hada da garin alkama da garin farar shinkafa, sai a hada aya da gyadar a markada a tace ruwan. Bayan nan, sai a dora kan wuta a zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da muka hade a guri daya, sai kuma ku zuba garin madara da zuma, ku dama ya yi kauri sai a rika sha safe da yamma. Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati biyu kafin yaye, kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi rigar mama, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa mamanki su tsaya sosai, ki rika sakawa.

Ki yi haka na tsawon sati biyu, da yardar ALLAH ni'imarki zata dawo fiye da yadda kikeda a baya

Idan kuma baki da halin siyan duka wadannan kayayyakin da aka ambata to kina iya yin kunun alkama ki rika sha sau biyu a rana, amma za ki rinka sa madarar gari, wato kunun alkama da madara ke nan.

HANYA TA HUDU

IDAN nononki kanana ne kina so suyi man ya kamar yadda kikeso dai-dai kina iya yin wannan hadi domin samun lafiya nononki

  • cukwul
  • garin alkama
  • aya
  • nonon saniya
  • madara
  • garin hulba.

Cukwul wanda yawansa zai Kai guda uku sai ki samu garin alkama gwangwanin daya sai aya itama gwangwanin daya sai ki daka su zasu zama gari ki tankade ki samu nonon saniya idan kuma bakyashan nonon saniya ki samu madara ki zuba wannan garin kamar cokali 3 ki dama kina shan kullum Sau 1 sannan ki Lura lokacin da zakiyi wanka ki tafasa ruwa da garin hulba a ciki ki Bari yayi sanyi sai ki wanke nonon da shi sannan Kiyi wankan.

HANYA TA BIYAR

wanna wani hadine da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wanna hadi kuma kowace mace inda tana da bukata zata Iya amfani dashi saboda tasirinsa, yanda akeyi shine.

  • garin waken soya.
  • garin alkama.
  • garin zogale.
  • garin bawon lemun Zaki.

Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin mungode da ziyartarku.

0 Response to "Gyaran nono a sati daya"

Post a Comment