-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Molewar Kan Jarirai,  Laifin Waye? , Hanyoyin Kaucewa Matsalar

Molewar Kan Jarirai, Laifin Waye? , Hanyoyin Kaucewa Matsalar

Molewar Kan Jarirai,  Laifin Waye? , Hanyoyin Kaucewa Matsalar

Molewar Kan Jarirai | Laifin Ungozoma Ne?

Ta wace hanya za a kauce wa matsalar?

Sau da yawa, idan mutane suka ga yaron da kansa ya ɗan mole ko ya taɓe daga goshi ko ƙeya sai su ce wai laifin ungozomansa ce da ba ta daidaita kan yadda ya kamata ba. Sai dai, wannan magana ta yi hannun riga da binciken masana. Domin ƙoƙon kan jarirai an haɗa shi ne da ƙasusuwa masu faɗi guda bakwai, waɗannan ƙasusuwa suna haɗewa kuma su yi ƙarfi har su bayar da cikakkiyar siffar ƙoƙon kai a cikin watanni shida.  

Saboda haka, kan jarirai na iya canja sifa idan aka samu ƙarancin lura yayin raino, musamman a watannin farko bayan haihuwa. 

Me ke kawo kan jarirai ko yara ke molewa, taɓewa ko kusurwa daga goshi ko ƙeya?

Daga cikin matsalolin da ke haddasa wannan matsala akwai matsalar nan da a ke cewa "Positional Plagiocephaly" a turancin likita. Wannan matsalar sifar ƙoƙon kai tana faruwa ne sakamakon kwantar da jarirai a bayansu tsawon lokaci ba tare da ana jujjuya su ba. Sakamakon ƙoƙon kan jariarai bai gama yin ƙwari sosai ba, wannan ya sa ƙoƙon kansu ke da haɗarin yin kusurwa.

Daga cikin alamun sun haɗa da:

1] Molewa, taɓewa ko kusurwar ƙoƙon kai daga ƙeya.

2] Saɓawar kunnuwa; ta yadda idan aka kalli kan yaro ko jariri daga sama za a ga kunnen ɓarin da ke da matsalar ya zarce gaba zuwa fuska fiye da na ɗaya ɓarin.

Wannan matsala an kasa ta zuwa : Mafi ƙaranci, matsakaiciya da kuma mafi tsanani.

Amma wannan matsala ba ta shafar aiki ko lafiyar ƙwaƙwalwa, sai dai matsalar sifar ƙoƙon kan kawai.

Abubuwan da ke iya janyo wannan matsala:

Bayan kwantar da jarirai tsawon lokaci a bayansu ba tare da ana jujjuya su zuwa hagu, dama ko rib-da-ciki ba.

Akwai abubuwan da ke ƙara haɗarin samun molewar kan jarirai kamar haka:

1] Ƙarancin ruwan mahaifa yayin goyon ciki.

2] Ƙuncin ƙugu ko mahaifar uwa.

3] Ɗaukar cikin tagwaye, ko fiye da haka.

4] Ɗaurewar tsokokin gefen wuya da ke kawo noƙewar wuyan jariri zuwa gefe guda wato "muscular torticolis", da dai sauransu.

Yadda za a magance faruwa matsalar.

Abin yi shi ne da zarar an haifi jariri to lalle ne a ɗinga lura da yanayin kwanciyarsa. 


Misali:

a] A riƙa zuya shi daga kwanciyar rigingine zuwa kwanciyar [magirbi] gefe; wato hagu ko dama ta hanyar tokarewa da naɗaɗɗen tawul ko zani. Ko kuma kwanciyar rib-da-ciki, amma a yayin kwanciyar rib-da-ciki akwai buƙatar ƙara lura da kuma sanya ido sosai. Domin kada hancin jariri ya toshe ya hana shi numfashi.

b] A ɗinga canja gurbin kai da ƙafafu, misali, idan yanzu kan jariri yana Gabas, to sai a juya ya koma Yamma. Hakan nan daga Kudu zuwa Arewa.

c]  A rage yawan lokacin da jarirai ke ɗauka a cikin kujerar raino ko keken raino.

d] A ɗinga jujjuya kai ko fuskar jariri daga wannan ɓari zuwa wancan ɓari.

Idan iyaye ko ungozomomi za su lura da waɗannan shawarwari za a rage afkuwar wannan matsala.

Sai dai, idan kan yaro ya wuce fiye da watanni uku bai koma daidai ba, ko kuma akwai jinkirin matakan girma, to akwai buƙatar zuwa asibiti domin ganin likita.

Bugu da ƙari, idan kin lura jaririnki ba ya son kallo ko juya kansa zuwa wani ɓangare, ko kuma idan aka yi ƙoƙarin juya fuskarsa zuwa wani ɓangare yana kukan ciwo, to akwai buƙatar ganin likitan fisiyo.


0 Response to "Molewar Kan Jarirai, Laifin Waye? , Hanyoyin Kaucewa Matsalar"

Post a Comment