-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa Jikin Masoya

Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa Jikin Masoya

Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa Jikin Masoya

 1. Ina bukatar tallafinki cikin wannan babbar rana mai dauke da tarin sirrikan albarka nake neman agajinki domin kibudemin kofofin zuciyarki hakan shine zaisa naji dadi wajen isar miki da Sakona
 2. Aminci agareki tare da gaisuwa mai fitowa cikin masarautar fadar zuciyar dake miki soyayyar Gaskiya
 3. Hakikanin Ainihin suffar motsin bakina yana juyawa tare da murmushin kallon halittar kyawawan Madaidaitan labban Bakinki
 4. Farin cikine mai fitowa daga sansanin tsakiyar ruhina yan zubewa a gabanki domin nuna isa da martabarki na mukamin sarautar gimbiyar yan Mata
 5. Shin kana daya daga cikin Samari Masu neman Budurwa wadda zasu aura? Ko kana shan Wahala Wurin tsayar da budurwa da kake so ka aura,?
 6. Nasan Soyayya itace take Ranka Wannan yasa kake ƙaranta Wannan Rubutun.
 7. To inda Kana Soyayya kuma kana cikin Samari Masu yin Soyayya Yana da kyau Duk Saurayi Yasan Cewa Budurwa Sai da Kalaman Soyayya
 8. Idan baka iya yimata Kalaman Soyayya to za,a Barka A baya Wurin Soyayya, Wannan Ita Magana ta Gaskiya,
 9. Domin sau dadama ansha amshe ma saurayi Budurwa ta Dalilin rashin iya kalaman soyayya.
 10. Wannan ne yasa Muka Tace, Muka Darje, Muka tsara muku Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa jikin Masoya.
 11. Gasu a nan kasa Asha Karatu Lafiya.
 12. Abubuwa kaɗan ne suke da daraja a wurina cikin wannan duniyar, ɗaya daga cikin su shine Murmushi ki, my priceless gift.
 13. Gari ya Waye, sabuwar rana ta fara, Ina Farin ciki da Nishadi saboda ina da ke a cikin rayuwata.
 14. Ina jin Soyayyar ki Wata Kyauta ce agareni da ban taba samun kyauta irin ta ba a rayuwata, my super lady.
 15. Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata! So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina!
 16. Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu
 17. wata a zuciyata sai ke kadai! 18. Congrats to me, saboda na Samu Mafi kyawu, Kulawa da Yarinyar da take Saurin Fahimta ta, kuma kece, my love
 19. Yarda da amincewarki gareni, sune zasu
 20. tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni!
 21. Yau nayi mafarki, Kin kawo mini ruwa mai sanyi tare da wani a hannun ki, wannan abun kuwa shine soyayya ta dana baki, ki riƙe shi kada ki sake. 22. Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan taba mantawa dake ba masoyiyata!
 23. Da Farko Ina Miki Sallama Irin Wacce Na Saba Miki a Kullum, Sannan Ina Miki fatan Alkhairi irin wanda na saba a kullum, kin tashi lafiya, Ya zuciyar ki take? Ta kasance lafiya, ko ta kasance kullum cikin tinani na? Ba sai kin bani amsa ba, bugun zuciyarki zai sanar dani.
 24. Nakan raba dare ina mai roqon Allah don
 25. neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko da nike roqo samu!
 26. Gari ya waye, hasken rana ya fito, nima kuma na fito domin cigaba da noma gonar soyayyarki dana saba a Kullum, ina fatan irin dake Zuciyar ki ya kasance dai dai da irin wanda nake shukawa, Domin samun yabanya mai albarka tsakani na dake, Soyayyar ki tasa ni yin hudar da ba tare da garma ba.
 27. Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi! Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata!
 28. Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki! 
 29. Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata!
 30. SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
 31. Akan ki zan iya komai banda Mutuwa, domin ina Son na kasance dake har abada, Nayi rayuwa dake mai kyau mai tsafta, Ina Miki barka da safiya Tare da fatan Zaki Wuni lafiya tare da farin ciki, Ki sani Ina Tare dake kuma Ina Qaunarki.
 32. Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki
 33. Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.
 34. Jarumta da hikimar iya launin bakinki wajen iya murmushin alfarma shine jagora wajen sanya zuciyata kamuwa da shauki na Musamman
 35. Kin Halittu: surar jikinki tana burge zuciyata hasken sinadarin shaukin murmushin fuskata Tananan tare da kyakkyawar halittar surar Jikinki
 36. Fararen hakoranki sun jeru daidai misalin kallon burge idanuna INA sonki
 37. SO shine fitilar dake haskake duhun kowane irin Ruhi sanna shine wakilin dake wakiltar damuwa mai gusar da dukkan wani farin ciki a rayuwar kowace irin Zuciya
 38. Iya kallonda nake yiwa kyakkyawar halittarki ya isa ya gamsardani cewa ke kykkyawace kuma wadda babu irinta a duniyar masoya. 
 39. Kwalliya, tafiya, kwalisa sae yan mata masu aji suke iya yin wanda zasu burge namiji, amma kuma ke ba iya burgewaba har numfashi take kusa da dauka domin dacewarsu.
 40. I luv yuh mah abar kaunata soyayyarki abun alfaharice agurina domin babu abunda nake nema in rasa idan na farin cikine.
 41. Sonki da kaunarki suna matukar wadatardani.
 42. Kece 'ya mace Guda Daya tilo da nake Alfari
 43. da Ita
 44. Koda Bayan Raina Soyayyata A gareki Ba
 45. Zata Shude Ba
 46. Nakan Dinmauce Sannan Kuma Na rude A
 47. duk Lokacin da Naji Muryanki Mai Kwatar Da
 48. Hankalin Duk Wani Mai Sauraro.
 49. Kece kyakkyawa mai Kyawan Hali Gami Da
 50. Kyawawan Dabi'u Nakan Kara Yiwa Allah
 51. Godiya Daya Mallakamin ke A matsayin
 52. Masoyiya.
 53.     I Love U Forever And Ever
 54. Soyayyarki tamkar wani haskene mai matukar jagorantardani a dukkanin duhun da natunkara a cikin birnin soyayyah,
 55. Soyayyah sanyine mai matukar sanyayarda xuciyar duk mai yinta, 
 56. Ina sonki ba ita bace kalmarda zata gamsarda zuciyarki da cewa hakane karfin soyayyarki a gunaba zan kasance mai bauta miki tamkar bawanki mai yimiki hidima a koyaushe. Ina matukar kaunarki tamkar yadda uwa take son danta.
 57. Kin kasance hasken farin wata wanda yake haske duniyar masoya dolene masoya suyi alfahari dake/
 58. Soyayya ruwan zuma wadansu sukace ruwan guba, amma ni nasan ruwan zumace domin nashata agurinki/
 59. So takalmin kayane duk wanda yatakashi sae ta wahalardashi, kada kibarni nasha wahala akan soyayya domin zan iya haukacewa sanadiyarki/
 60. Duk wanda baya soyayya ka tambayeshi dameye yake jin armashin rayuwarsa. So sarkine wanda idan ya shigeka zakaji kazamo tamkar sarki./

0 Response to "Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa Jikin Masoya"

Post a Comment