-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Shirin Tallafin P-Yes: Matsalar Username da Password Na Shirin Tallafin P-Yes

Shirin Tallafin P-Yes: Matsalar Username da Password Na Shirin Tallafin P-Yes

Shirin Tallafin P-Yes: Matsalar Username da Password Na Shirin Tallafin P-Yes

LABARAN P-YES - Yanzu dai shirin P-Yes ba wani sabon labari ba ne,  cewa shirin ƙarfafawa matasa na shugaban kasa ya dawo kuma daga tashar P-YES ta nuna shirin ya zuba ido yana karbar aikace-aikacen 'yan Najeriya masu shekaru 18 - 40. Sai dai wannan ba shi ne karon farko da kungiyar ta PYES ke bude aikace-aikacenta ga matasan Najeriya ba.

Shirin Karfafa Matasa na Shugaban Kasa ya fara bude shafinsa na aikace-aikacen 2019 kuma ya karbi miliyoyin aikace-aikace daga 'yan Najeriya da suka cancanta kuma tun lokacin babu wanda ya ji wani labari game da shirin. Ofishin sakataren gwamnatin tarayya kuma babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin matasa da dalibai, PYES na da burin samar da akalla 774,000 damar karfafawa ta hanyar karfafa matasa kai tsaye a cikin mafi karancin shekaru biyu. 

Kamar yadda muka sanarda cewa gwamnatin tarayya zata sake bude shirin P-Yes, kuma tuni dimbin matasan Najeriya ke sa ran sake neman shiga wannan shirin na P-YES.

Hakan zai faranta maku rai, amma ina so ku sani cewa shafin aikace-aikace na P-Yes yana nan a bude amma kuma shafin bayan an kammala cike abubuwanda suke bukata baya wucewa inda zai fitarda da wani sakon cewa a saka "Username da Password". Ku sani cewa yanar gizon P-Yes yana kan matakin haɓakawa(the website is still in its developmental stage) kamar yadda bayanai suka nuna. Bugu da kari, har yanzu ofishin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin matasa da dalibai wanda shi ne ke kula da shirin bai sanar da jama’a a hukumance ba. 

Hakan yasa muke kira ga masu son cin gajiyar sharin na P-Yes da su kara hakuri amma shafin akwai yuyuwar yadawo daram/kalau acikin kwanannan kamar yadda wani rahato yanuna a shafin Twitter, Duba sakon a kasa

ALLAH Yasa Mu Dace

0 Response to "Shirin Tallafin P-Yes: Matsalar Username da Password Na Shirin Tallafin P-Yes"

Post a Comment