-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Za'a Basu 250,000 Zuwa N3,000,000 Kuma A Basu Horo Don Tabbatar Da Cewa Sun Yi Amfani Da Bashin Yadda Ya Kamata - Cewar Ministan Wasanni Da Matasa

Za'a Basu 250,000 Zuwa N3,000,000 Kuma A Basu Horo Don Tabbatar Da Cewa Sun Yi Amfani Da Bashin Yadda Ya Kamata - Cewar Ministan Wasanni Da Matasa

Za'a Basu 250,000 Zuwa N3,000,000 Kuma A Basu Horo Don Tabbatar Da Cewa Sun Yi Amfani Da Bashin Yadda Ya Kamata - Cewar Ministan Wasanni Da Matasa

Kamar yadda kowa ya sani jiya Ministan wasanni da matasa, Sundaye Dare ya bayyana adadin matasan da zasuci gajiyar shirin NYIF karo na biyu in ya bayyan cewa matashi dubu goma ne zasuci wannan gajiyar duba sauran bayanan Ministan wasanni da matasa, Sundaye Dare da yayi a jiya.

Wannan shine zango na biyu na shirin NYIF da gwamnatin ta kaddamar

Abuja – Gwamnatin tarayya a ranar Talata, ta ce an sake sakin sunayen mutum 10,000 da a’a baiwa tallafin kudin jari karkashin shirin Tallafin matasa a Najeriya (NYIF).

Gwamnatin tace wannan ya biyo bayan mutum 5,285 da aka saki sunayensu da farko.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Kola Daniel, mai magana yawun Ministan wasanni da matasa, Sundaye Dare, ya saki, rahoton Tribune.

Ya bayyana cewa za’a horar da wadanda aka zaba kuma za’a raba musu kudaden da akayi alkawari.

Jawabin Ministan ya kara da cewa an zabi sunayen matasan ne bayan tantance matasa milyan uku da suka nemi bashin.

Yace:

“Bayan kammala sahun fari, NIRSAL ya fitar da sunayen mutane 10,000 don horar da su da kuma basu kudin jarin.”

“Bashin da za’a bada ya fara daga dubu dari biyu da hamsin 250,000 zuwa milyan uku (N3,000,000)

“Wadannan sunaye na kan shafin FMYSD da NOYA.”

“Dukkan wadanda aka zaba zasu yi horo don tabbatar da cewa sun yi amfani da bashin yadda ya kamata.”

Gwamnatin tarayya ta saki sunayen mutum 10,000 da zata baiwa bashin NYIF Hoto: Ministry of Sports 

 Domin sauke Sunayen Wayanda Za'a Turawa Rance LATSA NAN

0 Response to "Za'a Basu 250,000 Zuwa N3,000,000 Kuma A Basu Horo Don Tabbatar Da Cewa Sun Yi Amfani Da Bashin Yadda Ya Kamata - Cewar Ministan Wasanni Da Matasa"

Post a Comment