-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Da Dumi-Dumi: Buhari zai sallami wasu karin ministocinsa

Da Dumi-Dumi: Buhari zai sallami wasu karin ministocinsa

Da Dumi-Dumi: Buhari zai sallami wasu karin ministocinsa


Rahotanni daga Najeriya na cewa, akwai yiwuwar shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sake sallamar wasu daga cikin ministocinsa sakamakon rashin taka rawar gani.

Wata majiyar sirri daga fadar shugaban kasa ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, nan gaba kadan akwai karin ministocin da shugaba Buhari zai sallama.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya tube Alhaji Sabo Nanono daga kujerar Ministan Noma da kuma takwaransa na Wutar Lantarki Engr Sale Mamman.

A karon farko kenan da shugaba Buhari ke daukar tsattsauran mataki na tube wasu daga cikin ministocinsa tun bayan da ya dare kujerar shugabancin Najeriya a 2015.

Buhari ya maido da akasarin ministocin da ya yi aiki da su a lokacin wa’adin mulkinsa na farko bayan da ‘yan Najeriya suka sake zaben sa a 2019.

Source: rfi0 Response to "Da Dumi-Dumi: Buhari zai sallami wasu karin ministocinsa"

Post a Comment