-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tsoffin yan wasan Real Madrid sun doke tsoffin yan wasan Barca da ci 3-2

Tsoffin yan wasan Real Madrid sun doke tsoffin yan wasan Barca da ci 3-2

Tsoffin yan wasan Real Madrid sun doke tsoffin yan wasan Barca da ci 3-2Tsofaffin yan wasan Real Madrid sun samu nasara akan tsofaffin yan wasan Barcelona a Ranar Talatar nan da ci 2-3, Kuma Yan wasa sun haska sosai tamkar shekarun su Basu tura ba.

Ronaldinho shine ya Fara zura kwallon farko a bugun fenareti, sai dai Real Madrid ta samu nasarar lashe wasan da ci 3-2 ta hannun Pedro Munitis, Alfonso Perez da Kuma Ruben de la Red.

An tashi Barça 2-3 Real Madrid Kuma a wasan an ga Ronaldinho, Rivaldo da Deco da sauransu sanya da rigar Barcelona, sannan kuma munga Roberto Carlos do Figo a cikin fararen riga.

Yan kallo 25,000 a Tel Aviv dake kasar Israel sun halarci wasan kai tsaye, yan kallo sun ji daɗin ‘yan wasan waɗanda suka ba da abubuwa da yawa game da su a zamaninsu kuma waɗanda har yanzu suka bar wasu tarihai masu matukar mahimmanci.

Babban burin Rubén de la Red ya ba Real Madrid nasara da ci (2-3) a wasan Wanda akewa lakabi da El Clásico de leyendas

Jerin yan wasan da suka buga wasan sun hada da. Frank De Boer, Francesco Coco, Rivaldo, Mariano Angoy, carscar Arpón, David Tortolero, Okunowo, Miquel Soler, Xavi Guzmán. Jofre Mateu, Javier Saviola, Deco, Gaizka Mendieta, Ronaldinho, Goicoechea, Juan Carlos, Frederic Dehu da Guillermo Amor. José Emilio Amavisca, Luis Milla, Antonio Núñez, Iván Campo, Rubén De la Red, Alex Pérez, Fernando Sanz, Martín Vázquez da Jordi Codina. Pedro Munitis, Enrique Velasco, Roberto Carlos, Alfonso Pérez, Alberto Rivera da Luis Figo. A dukka kungiyoyin biyu.

0 Response to "Tsoffin yan wasan Real Madrid sun doke tsoffin yan wasan Barca da ci 3-2"

Post a Comment