-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Ga siffofin mata masu yin madigo ‘lesbians'

Ga siffofin mata masu yin madigo ‘lesbians'

Ga siffofin mata masu yin madigo ‘lesbians'Rayuwa mai yayi, rayuwa mai abin gani mai kuma abin fada, rayuwa mai kyara tarbiya mai kuma bata ta. Babban abu mafi muni shine rugujewar tarbiyar ‘ya mace, don tarbiyan mace daya al’uma dubu kan tarbiyantu, matsalar, idan tarbiyan mai kyaune, dubu zasu yi kyau haka idan mummunace dubu sun lalace.


Madigo wato ‘Lesbian’ tsakanin mata wani sabon salon lalacewan ‘ya mace ne da a yau ke dada tashe a cikin al’umma. Madigo na nufin saduwa ta hanyar gogayya tsakanin macce da mace ta amfani da tsiraicinsu ko cikon halittun matancinsu  don jin dadi ko kau da sha’awar junansu. Ayau bincike ya nuna akan samu yaran mata dag shekaru takwas zuwa sama na cikin harkar.


Ga siffofin mata masu yin madigo ‘lesbians'


Tsanan da namiji, rashin sha’awarsa  da rashin sha’war yin aure.

Suna nuna wa juna tsananin soyayya (macce da macce) da nuna damuwa idan basu hadu ba.

Suna nuna tsananin kishi yayin da abokiyar harkarsu ta fara mu’amala da wata.

Suna da kalaman gane juna, misalai, ‘muna tare ne?’ ‘kina harkane?’ ‘kin tayarmin da tsumi’ ‘za ki yi dadin harka’.

Suna son yin amfani da kwayoyi dake tunkudo cikon halittarsu, kamar kirjinsu ko mazauninsu.

Wasu sukan sanya zube a yatsunsu na kafa

Wasu daga cikin abubuwa dake jefa mata harkar madigo lesbianism:


Makarantar kwana ta mata, yakan fara faruwane yayin da mace ta kai matakin sha’awar da-namiji, takuma sami kawaye masu karancin tarbiya.

Amfani da manyan wayoyi dake sadasu da fina-finan basa da kawaye masu madigo

Takurawa mace da kuma hanata aure a lokacin da take kishin ruwan da-namiji

Macen data taba sanin namiji ta kuma shiga takura na tsaro daga iyaye ko magabata.

Karancin ilimin na iyaye da rashin sanin hakkokin ‘ya’yansu akansu.

Zama da mace mai yin madiko ‘lesbian’.

Kau da kai daga sakamakon lahira

Shahara a munafurci da aikata sabo

Gudun daukan cikin shege

Don a yarda ita kamilace.

Illolin madido:


Tsanan da-namiji da rashin sha’awarsa

Masu madigo kan bi juna gidan mazajensu

Yin madigo kan haifar da masifu da bala’i

Wadanda suka yi nisa, idan sun yi aure mazajensu basa gamsar dasu

Basu damu su yi abin da mazajensu zasu gamsu dasu waje jima’I ba

Ba su cika son aihuwa ba.

Basa jimawa agidan miji

Akwai bukatan iyaye su farga, musamman iyaye mata sanin asalin kawaye dake mu’amala da ‘yarsu.


ALLAH YA KARE MANA ZURI’ARMU, AMIN. Za a iya duba: Rushe tarbiya ta duniyar yanar gizo da sauransu.

0 Response to "Ga siffofin mata masu yin madigo ‘lesbians'"

Post a Comment