-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

 Duba Bayanin Yadda Ake Lalle da Sifa

Duba Bayanin Yadda Ake Lalle da Sifa

 Duba Bayanin Yadda Ake Lalle da Sifa Kwalliyar Lalle musamman ga ’yan mata budare jigo ne a cikin tsarin fito da kwalliyarsu, sun gadi wannan kwalliyar tsawon lokacin da tarihi ya kasa tuna sanda mata suka fara yin kunshin lalle a matsayin kwalliya.


Yin lalle kawa ce ga dukan macen da ta dauki kanta cikakkiyar mace ba sai wadda take da miji ba, dukkanin jinsin mata ba wadda kawa bai zama wajibi a gare ta ba don ita ce cikar ta na ‘ya mace, hasalima ita ce hanya babba wadda ke rabewa a bayyane tsakanin mata da maza.


Lalle, ya kasu gida biyu akwai lallen gargajiya da aka gada kaka da kakanni, da kuma lallen zamani wanda ake kira sifa. Suna da bambanci kwaran da gaske.


Lallen gargajiya ana yinsa ne ta hanyar amfani da sansamen iccen lallen da ake dakawa bayan sun bushe a mai da su gari, sai a kwaba a shafa a kafa da hannu domin kawata fata da gyaran jikin mace.


Lallen sifa ana hada ta ne ta hanyar yin amfani da garin fulawa da garin bakin dutse wato Dayis don ta yi baki a hada su da wasu sinadarai domin inganta ta, ita ma wannan siffar ita ake amfani da ita wurin yin zanen fulawa a hannaye da kafafu, sai kuma sinadaren rani da ake sanyawa wanda shi kalar ja ne.


Idan aka yi wa mace kwalliya da siffa hade da Rani abin zai yi sha’awa da kyawo


Lalle wani sinadiri ne mai dauke da amfani daban-daban wanda addinin musulunci ya kwadsaitar da mata su yi lalle domin akwai sirrika tattare da yinsa, duk da yake dai da yawan mutane suna alakanta kwalliyar lalle da jan ra’ayin samari ga ‘yan mata ko kuma daukar hankalin mai gida ga matarsa.


Kwalliyar lalle dadaddiyar al’ada ce ga al’ummar Hausawa wanda yake da matukar tasiri gare su ganin yadda suka baiwa lalle wata martaba ta musamman a yayin bukukuwan aure ko suna da sauran bukukuwan da ake yi wa kwalliya ta burgewa da shiga tsara.


Muhimmancin da ke gare shi ne ya sanya aka samar mishi bagire cikin jerin tsarin shirye-shiryen bukin aure ‘ranar kunshi’ kunshin nan da lalle ake yinsa. Amarya ba za ta cika ba sai an fente mata jikinta da lalle a kafafunta da hannaye abin da zai mayar da ita abar kallo.


A bangaren kiyon lafiya lalle na da rawar da yake takawa wadda take muhimmiya ce, da farko dai lalle kariya ne daga curutoci da dama da suke addabar jama’a,  misali yana zage cutar kafar da duk aka yi shi samanta, sannan yana tabbatar da samuwar ni’imar mace ba tare da gushewa ba, yana gyaran fata domin shi matsayi ne na ‘natural toner’ da ba ya jeme fata sai dai ta yi haske ta yi kyau saboda ya goge duk wani datti da ke da fata, kuma hakan lallen gargajiya kawai ke yinsa abin da aka rage daurawa a duniyar mu ta wannan zamani.


Idan mace tana son gyara fuskarta ta yi kyalkyali, laushi ta yi amfani da lallen gargajiya, ‘yan matan wannan zamani suna da hanyoyi da dama da suke amfani da lalle a wurin yin kwalliya hakan ya sanya a yanzu an dauke shi sana’a ta hannu kuma yana da kasuwa kwarai da gaske yana samar da kudin kashewa.


A bincike da Managarciya ta yi bayanai sun nuna cewar matan da ke kwalliya da lalle na samun kwarjini da kima mai girma a tsakanin mazajensu da samarinsu .


Mazaje da yawa sukan baiwa matansu kudi daga cikin aljihunsu domin su yi kwalliyar lalle.


“In muka yi lalle da gyaran jikinmu har kyauta da yabo muke samu na musamman wajen mazajenmu, wannan yana nuna mana  mutukar sha’awar da suke da ita a wannan bangaren” kalaman wasu mata da Managarciya ta zanta da su.


Mata da ‘yan mata a cigaba yin kwalliyar lalle sosai domin ki zamo sarauniya abar son kallo da kuma shauki daga mazajenku da masu son aurenku.


Hotunan kayatattun lalle da sifa na zamani0 Response to " Duba Bayanin Yadda Ake Lalle da Sifa"

Post a Comment