-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Wata Sabuwa: Ƙungiyar ASUU na shirye-shiryen sake tsunduma yajin aiki

Wata Sabuwa: Ƙungiyar ASUU na shirye-shiryen sake tsunduma yajin aiki

Wata Sabuwa: Ƙungiyar ASUU na shirye-shiryen sake tsunduma yajin aiki

Ƙungiyar malaman jami’o’in ta ASUU ta bayyana shirin ta na sake tsunduma yajin aiki muddin babban akanta Janar na ƙasa bai biya mambobin ƙungiyar haƙƙinsu na tsahon watanni 13 da su ka gabata ba.

Shugaban ƙungiyar ta ASUU reshen jami’ar jihar Plateau, Dr. Lazarus Maigoro ne ya bayyana haka ga manema labarai a Jos babban jihar.

Dr. Lazarus Maigoro ya bayyana cewa, babban Akanta janar na ƙasa, Ahmed Idris shi ne ke ƙara ruruta wutar rikici tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya.

Ya ce domin tuni shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin biyansu hakkokinsu amma shiru.

Tsarin IPPIS da aka samar a karkashin ofishin babban akanta janar na da manufar riƙa biyan dukkan ma’aikatan gwamnatin albashinsu kai-tsaye zuwa asusun ajiyarsu na bankuna, tare da sanya idanu kan yadda ake cirar kudin ma’aikatan.

Har kawo lokacin haɗa wannan rahoton ofishin Akanta Janar din bai ce komai ba game da ƙorafin na kungiyar ta ASUU, sai dai tuni dalibai da iyayen yara suka fara nuna fargaba a kan tasirin da yajin aikin zai yi a harkar karatun dalibai. A ‘yan shekarun nan dai kungiyar ta ASUU ta shiga yaje-yajen aiki, lamarin da wasu ke ganin ya taimaka wajen gurgunta harkar karatu a jami’oin ƙasar nan.

Turawa Abokai

0 Response to "Wata Sabuwa: Ƙungiyar ASUU na shirye-shiryen sake tsunduma yajin aiki"

Post a Comment