-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

AIKI SAI MAI SHI: Buhari ya kafa kwamitin yi wa fatara da talauci dukan kabarin kishiya

AIKI SAI MAI SHI: Buhari ya kafa kwamitin yi wa fatara da talauci dukan kabarin kishiya

AIKI SAI MAI SHI: Buhari ya kafa kwamitin yi wa fatara da talauci dukan kabarin kishiya



Shugaba Muhammadu Buhari ya Kwamitin Rage Raɗaɗin Fatara da Talauci a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaba Yemi Osinbajo, a ƙoƙarin cika alƙawarin da Buhari ɗin ya yi na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci, a cikin shekaru 10 kacal.

“Ina cike da farin cewa wannan shiri da mu ka shata na kakkaɓe talauci da ƙuncin rayuwa ga mutum miliyan 100 an tsara shi ne ta hanyar magance kurakuran da aka ɗibga a baya, sai kuma kafa tubalin shirin daƙile fatara.”

Buhari ya ce Shirin Rage Raɗaɗin Talauci zai kuma binciko dalilan da ke haddasa talauci, sabubba da rabe-raben talauci ta yadda za a san irin kulkin da za ta sa domin ta yi masa kwaf-ɗaya.

‘Yan Kwamitin sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, gwamnonin Ekiti, Sokoto, Nasarawa, Bsrno, Ebonyi da sauran su.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Karamin Ministan Kuɗaɗe, Ministar Agaji da Jinƙai, Ministan Gona da na Cinikayya.

Cikin ƙarshen makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES HAISA ta buga labarin da ya nuna cewa: har yanzu malejin tsadar rayuwa da maganaɗisun rashin aiki na riƙe da maƙogaron ‘yan Najeriya .

Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya tabbatar da cewa Tattalin Arzikin Cikin Gida na Najeriya na ƙara bunƙasa. To amma fa har yanzu rashin aikin yi da ƙuncin rayuwa sun riƙe wa talakawa da marasa galihu maƙogaro, ta yadda miliyoyin ‘yan Najeriya ke iya haɗiyar ruwa da kyar.

Shugaban Tawagar IMF, Jesmin Rahman ya bayyana haka a lokacin ganawa ta nesa-nesa da su ka yi da jami’an gwamnatin Najeriya, ganawar tsawon mako guda cur, daga 1 zuwa 8 Ga Yuni, 2021.

An shafe kwanaki ana tattauna baturuwan da su ka shafi tattalin arziki da kuma ƙarfin ci gaban Najeriya.

IMF ya ce dukan tsiyan da naira ke sha a hannun dalar Amurka da sauran manyan kuɗaɗen duniya, abu ne mai kyau, domin zai kawo daidaito a kasuwar hada-hadar kuɗaɗe a duniya.

“A yanzu tattalin arzikin Najeriya na ci gaba da samun ƙaruwa da haɓɓaka. Ya na farfaɗowa daga taɓarɓarewar da ta shafe shi, sanadiyyar ɓarkewar cutar korona.”

Sai dai kuma duk da haka IMF ya ce rashin aikin yi ya kai ƙololuwar maleji, haka ƙuncin rayuwa ya riƙe wa miliyoyin ‘yan Najeriya wuya, su na ta shure-shuren da ko kafin ɓarkewar korona ba su yi irin wannan galabaitar ba.


“Tsadar rayuwa ta ƙara haifar da tashin farashin kayan abinci da kayan masarufi.

IMF ta kuma lura da cewa duk da gwamnatin Najeriya na ƙara matsa-lamba wajen tatsar haraji a jikin jama’a da dama, ba kasafai ake ganin tasiri ko albarkar kuɗaɗen ba, saboda maƙudan kuɗaɗen da gwamnatin ƙasar ke kashewa da sunan biyan tallafin man fetur, aikin allurar rigakafin korona da sauran hanyoyin da gwamnatin ke yawan kashe kuɗaɗe rututu.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa naira ta yi faɗuwar-‘yan-bori a lokacin da asusun Gwamnatin Tarayya ya huje.

Dalar Amurka na ci gaba da lakaɗa wa naira dukan tsiya a kasuwar ‘yan canji, daidai lokacin da rumbun ajiyar Gwamnatin Najeriya na ƙasar waje ya yi ƙasa, ta yadda bai taba raguwa cikin shekaru huɗu baya ba kamar wannan lokaci.

Rumbun Ajiyar Kuɗaɗen Najeriya a Waje ya huje, saura dala biliyan 34.

Duk da irin ƙarin farashin litar ɗanyen mai da aka samu a watannin baya, Babban Bankin Najeriya ya bayyana sauran kuɗaɗen ajiyar ƙasar da ke waje bai haura dala biliyan 34 ba.

Rabon da asusun ya yi ƙasa zuwa wannan adadin kuwa tun cikin watan Yuli, 2017, shekaru huɗu da su ka gabata kenan.

Tsakanin 31 Ga Mayu zuwa 10 Ga Yuli, asusun ya ragu da dala miliyan 222.3.

Kafin nan kuwa can baya a cikin Disamba, 2020 sai da asusun ya kai abin da ke ciki ya kai dala biliyan 36.5.

PREMIUM TIMES ta kira Kakakin Yaɗa Labarai na CBN, domin jin ƙarin bayani daga bakin sa, amma bai amsa kira ba.

Fito da ƙididdigar adadin raguwar asusun ya zo daidai lokacin da Gwamnonin Najeriya na jam’iyyar PDP su ka yi zargin cewa Gwamnatin APC ta maida NNPC kandami a sha a yi wanka, CBN ya koma rijiyar tsakiyar gari, sai kamfatar ruwan ciki gwamnatin APC ke yi kawai.

A wani sabon zargin yadda ake ta kamfata da jidar kuɗaɗe a ƙarƙashin gwamnantin APC, Ƙungiyar Gwamnonin PDP sun bayyana cewa manyan hukumomin tara kuɗaɗen gwamnatin tarayya sun zama wuraren da a kullum a ke ta yi wa dabdala da rubdugun wawurar kuɗaɗe.

A taron da gwamnonin na APC su ka yi a Uyo babban birnin Akwa Ibom, gwamnonin na PDP sun nuna fushin yadda kamfanin NNPC ya zama babban kandamin a sha a yi wanka, wanda gwamnatin APC ke kamfatar maƙudan kuɗaɗe kai-tsaye ba tare da bin tsarin federaliyya wanda dokar Najeriya ta gindaya ba.

Sun kuma bayyana cewa tuni Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tashi daga bankin ‘yan Najeriya, ya koma rumbun watandar jami’an gwamnatin Buhari.

Sauran hukumomin da Gwamnonin PDP su ka zarga ana amfani da su a ƙarƙashin gwamnantin APC ana nuna bambanci da son rai ana talauta ‘yan Najeriya, sun haɗa da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), NIMASA, NCC, Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS) da kuma Hukumar Kwastan ta Ƙasa

Sun bada misali da yadda NNPC ke kashe kuɗaɗen fetur duk yadda ta ga dama, a lokacin da ta ga dama, ga wanda ta ga dama kuma ko nawa ta ga dama.

Gwamnonin sun tunatar yadda watan Afrilu NNPC ya ƙi bai wa Gwamnatin Najeriya ko sisi daga kuɗaɗen da ya kamata ta bayar daga cinikin fetur, domin a raba wa Tarayya, Ƙananan Hukumomi da Jihohi.

Wannan mummunan hukuncin karya doka inji PDP, ya tauye wa ‘yan Najeriya kuɗaɗen da suka kamata a yi masu ayyukan bunƙasa ƙasa.

CBN Ya Zama ‘Yar-rototuwar Da Ke Wa Gwamnatin APC Aman Kuɗi Su Na Lashewa -In ji Gwamnonin PDP

“Shi kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zama ‘yar-rototuwar da ke wa gwamnatin APC aman kuɗi su na lashewa a lokacin da su ke so.

“CBN ya zama babu mai sa masa ido ko mai hana bankin duk abin da ya ga damar yi. Domin ta kai har ya na buga kuɗaɗe yadda ya ga dama, ya yi abin da ya ga dama da kuɗaɗen kuma ya kashe duk abin da ya ke son kashewa, ba tare da ana yi masa linzami ba.”

A ƙarshe gwamnonin waɗanda a taron, har da Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, sun yi kira ga bankunan Najeriya da su taimaka su ceto naira daga karyewar da darajar ta ke yi a dullum wayewar gari.

Faɗuwar Darajar Naira:

Shafin bayyana darajar naira ko faduwar ta a kasuwar ‘yan canji mai suna abokiFX.com ya bayyana a yanzu Dalar Amurka 1 daidai ta ke da Naira 505.

Ƙididdiga daga FMDQ kuwa ta nuna cewa banki ana sayar wasu sayo kaya daga waje da masu zuba jari Naira 411.75 a dala 1.

0 Response to "AIKI SAI MAI SHI: Buhari ya kafa kwamitin yi wa fatara da talauci dukan kabarin kishiya"

Post a Comment