Zalunci:-Fusatacciyar Uwargida ta cije al'aurar maigida har ya gundule, duba dalili

Zalunci:-Fusatacciyar Uwargida ta cije al'aurar maigida har ya gundule, duba dalili

Wani mutum mai suna Sibangilizwe Ngamula, yana kwance a Asibiti bayan matarsa ta cije kan al'aurarsa sakamakon haka kan kaciyar al'aurarsa ya gundule a kasar Zimbabwe.

Majiyar isyaku.com ta ce an sha samun matsala tsakanin Sibangilizwe da matarsa bisa zargin neman maza, wanda matarsa ta sha musantawa, sakamakon haka ake yawan samun tashin hankali a gidan.

Bayanai sun nuna cewa sakamakon haka matarsa ta kwashe kayanta ta tafi gidansu har ta yi mako biyu.

Bayan ta dawo ne kuma sai rikici ya sake kaurewa tsakanin ma'auratan, sakamakon bacewar makullin daki, wannan lamari ya sa matar Sibangilizwe ta dunkule hannunta ta kai wa mijinta duka a fuska,  ta kuma cakume golayensa ta murde su har ya fadi, daga bisani kuma ta kama  al'aurarsa ta gatsa masa cizo mai tsanani da hakoranta har kan al'aurar ya cire.

Saidai an garzaya da Sibangilizwe zuwa wani Asibiti inda yake jinya, amma wata majiya a Asibitin ta ce Sibangilizwe zai iya ci gaba da jima'i duk da yake kan al'aurarsa ya cire kuma wasu jijiyoyin al'aurar sun tabu

Source:- Isyaku.com


0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

Stay Conneted

Most Recent