-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YAR BAIWAH Hausa Novels

YAR BAIWAH Hausa Novels

YAR BAIWAH Hausa Novels

Bismillahi Rahamanir Raheem!!!   ๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH๐Ÿ™Ž

Maman Ussee Yau yakasance jumma'ah yayinda kowa ke hada hadar zuwa masallaci garin yayi haske gwanin sha'awa kowa lamarin gabansa kawai yake  tafe take tana yan wake wakenta dauke da tulu akanta zataje debo ruwa rafi kasancewar yau kasuwar garin nasu so take taci kwalliya Dan zuwa kasuwa Sameera kenan YAr BAiwa ahankali kawarta indo ta lallabo tabayanta tace Keee, hava indo meye haka nihar kin tsoratani wallahi ohh wadda aka kira da indo tayi ๐Ÿ˜€ tace kekuma gaki da tsoro kamar kura ko samira tayi murmushi tace to sai kawai naganki kwatam toya akayi kawalliya naje gdnku banga ki ba eah wllhi Inna ce ta aikeni sayen omo kinga sauri ma nakeyi tace karna Dade to sa himma nima kinga danakai wan nan din nakare sai mun hadu kasuwa ko taimata sallama suka wuce.

Kai tsaye gidansu ta nufa da sallamarta ta aje tulun washh wallahi umma nagaji  ke banason shashanci Dan wan nan diban ruwan ne wai kingaji rafin nisa gareshine daxakice wai kin gaji sa himma kiyi wanka kinga ankusa tasowa daga masallaci, kije kasuwar ki yo mana sayayya ta amsa da to tashiga daki ta kwabe kayanta tafito da daurin kirji tashiga bayi tai wanka ta fito tana Shafa mai da hoda nidai gefe nakoma ina kallon ikon Allah anata cika fiska da kwalli da digo digo ohhh dariyace ta kusa subucemin nadai gimtse INA kallon Samira an takarkare ana Shafa Jan ๐Ÿ‘„ takare takoma fannin sa kaya wasu kaya atamfa ce ba laifi kam a wurin samira da ita a ganinta yau Zata goge sosai.

Sameera yarinya ce yar kimanin shekara goma sha Biyu farace  ba Sol ba irin chocolate colour din nan Allah yamata baiwar kyau  bakinta Dan karami dashi dauke da siraran labba ga hakora farare Sol kanana Jere gwanin sha'awa tanada idanuwa masu kayatarwa irin na mejin bacci sexy eyes ba laifi kam batada jiki kuma baxa asakata layin maras kiba ba masha Allah da ita son kowa kin Wanda yarasa ga tada shaf brain shiyasa ake kiranta da yar Baiwa duk abinda aka fada mata bata mantawa ga hankali uwa uba hakuri batada kiriniya ga basira sai dai kash abu dayane samera batadashi iyayenta talakawane ga samira nason boko  kamar me intaga Dan birni cewa take Dan koyamini turaci Allah yayi sameera mai son abu duk abinda tasa kanta to ta rike kenan kuma da an fada mata so daya ya shiga kanta 

Umma na fito bani sakon so nake nadawo da wuri so nake naje wurin Dan birni kinsan yau yadawo Ohh kekam da naci kike to Allah Bada Sa'a ungo ki sayo min kayan yaji da sukari kinji tace to innna ta amsa tafito tana tafiyarta a hankali ba abinda ke damunta har takai kasuwa tana sayayarta saiga garbati   shida tawagarsa suka tareta ke yar Baiwa sunanda kowa ke kiranta dashi kenan. Tin dazu ina jiranki kin shanyani mekike nufi itadai  bata ce komai ba ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta can sai ga Indo ta isu takallesu ta watsar wai kai wanne irin bawo nekai ana soyayya dolene kunbi kun takurawa yarinya kun hanata sakat duk Inda taje sai kunbita kamar wasu mayu.      Ke yarinya ki iya bakinki mtseew indo taja karamin tsaki kukan dai anyi shashashai wllhi ilu na tare da garbati yadaga hannu  zai mareta sai iro yace kai Narabaka gidansu basa yafiya wllhi kumuje tunda uwarta tazo indo taja hannun samira suka wuce kekam dai kinji haushi su wadan nan banzayen zaki tsaya suna garaki to indo yakikeso nayi dasu kinsan halin garbati zai iya kullamin sharrin da  banjiba bangani to ki tsaya sokonci har a Rena ki in anmiki tsiwa xakiyi kinuna bakya tsoronsu inba haka. Ba kinatare dajin haushi to Inda banxoba fa sai yaya kenan sai ya kuwa illa in rokesu mtseew kinji haushi wllhi yar Baiwa nidai muje kiraka ni nasayowa innata magarya tam muje.

Suna tafe suna tadi abinka da kawaye har sun manta Indo kawar sameerace tun suna yara sa'an ni. Juna ne gidansu  ba wani nisa dagidansu sameera indo akwai tsiwa ga iyayi batada hkr kuma bata daikar raini shiyasa ake shankunta ko a cikin gari uwa uba tanada yayu masu shiga mata gidansu duk Wanda ka taba ka tsokalowa kanka  basa Barin kota kwana.

Sallamu alaikum inna nadawo xanje gidansu Dan birni akoya min boko to yar Baiwa saikin dawo kardai ki Dade kinji ta amsa da to ta fito da azama zuwa gidansu kabeer duk da tana shakkun Hajiyarsa Dan ta tsaneta hasalima batason yana zuwa gidan baxata manta ranar da takirata da mayya kekam kullun sai kin likewa Dana to ahir dinki sameera bata kawo komai aranta ba ita burinta kawai akoya mata turanci ta iya zata jure duk wani fada na Hajiya matsawar za'ta samu abinda takeso wan nan kenan.

Tana shiga gidan saida gabanta yafadi tadai danne ta Shiva cikin gidan kai tsaye falon Hajiyar ta nufa suna zaune ita da 'ya'yanta husnah da yusrah sai kamal kanin Kabeer da Sallamarta tashiga su yusrah naganinta suka washe baki suna dariya ohh Yar Baiwa sarkin son karatu har an iso kenan cewar kamal Hajiya Kareema najin an ambaci sunanta ta hade rai kamar bata taba dariya ba Samira na shigowa ta gaida Hajiyar INA wuni lafiya atakaice San nan taja tsaki mtseew da dawowar tashi baza'a barsa ya huta ba kuma zaki wani zo kidamesa haba Hajjiya meye laifinta nine nace tazo ai dalibata ya kk ya kwana biyu hpe dai kinzo dashiri danyau akwai sababin darussa ta murmusa tace eah uncle to shigo ki zauna kamin naci abinci sai mu fara Husnah kuma Ku shirya musamman ma ke yusrah naga bakya maida hankalinki sosai sunka turo  baki hva yaya week end nefa yakamata mu huta kai bana son shashanci kutashi maxa Hajiya kareema hararar samira kawai take itadai ta tsani yarinyar nan nacewa ne da ita to dolene saita iya turanci itada take ba yar kowa ba tashin kauye ko ubanme iya turancin zai tsinana mata oho yarinya kamar mayya tabi ta ha nata sakat itada danta inyazo week end said a dare da rana yana tare da shegiyar yariyarnan sai Yarbaiwa cewar Hajiya acikin zuciyarta.

Itadai sameera ta takure gefe jiran fitowar   uncle Kabeer kawai take yazo yafara koya mata abinda zata karu tabar gidan yana kamalawa tafito da book rike a hannunsa yace to daliba muje garden ko ta mike su yusrah ma suka biyota suka biyo bayanta  suna isa kowa ya zauna a kujera yafara gabatar musu da lesson yayinda yar Baiwa da yayi tambaya take amsawa itada batamada lesson book amma yusrah sai a hankali gara ma Husnah tana Dan ja haka da haka har suka kare kasancewar ba lokaci dayawa 'Yar  Baiwa tai godiya takoma ta ma Hajiya sallama ta wuce zuwa gidansu tana zuwa ta rungume ummanta tana murna take Bata labarin abinda aka koya mata haka rayuwar samera takansance har karshen sati itadai burinta tasamu ilmi Dan ta taimaki mahaifanta!!!


2 be continued

Maman ussee


๐Ÿ™Ž 'YAR  BAIWAH๐Ÿ™Ž2⃣


Maman usseeRukayya 'ya CE ga malan sa'idu ita kadai Allah ya azutarsu da ita bayan sunsha wahala matuka kamin su sami haihuwa shekarar su 10 da aure ko batan wata  ba'a taba yiba a gidansa kwatsam sai ga cikin Rukayya ansamu karkuso kuga murna a wurin malan sa'idu ya dauki burin duniya yasaka akan cikin nan mai dakinsa har mamaki take duk da itama tana burin taga kwanta a duniya Dan baxata manta ba ko haihuwa akayi idan taje barka ba'a. Bata jariri wai  batasan zafin haihuwa ba Dan haka.Baxa a bata ba tasha kuka amma dayake mijinta na matukar kaunarta sai ya lallasheta da kalamai masu dadi yana kwantar mata da hankali yana lurar da ita haihuwa ta Allah ce kuma Allah yana sane dasu karta damar da kanta wata rana suma  Allah zai basu nasu rabon haka ne kam gashi hkrinsu yabasu yau Allah yabaiwa salamatu ciki haka sukayita renon cikin har Allah ya ingantashi Rayuwa kenan(mai hakuri mawadaci) malan Sa'idu mutumin garin Raba ne asalin su fatakene sukanje fautaci gari gari anan ne Allah yaha dasa da salame sunana da ake kiranta kenan jinisu ya hadu sosai Dan ita yar dagacin garin Damagara ce kuma duk  bako a gidansu yake sauka suke basa masauki anan me Allah ya hadasu har aure ya shiga duk da dagaci. Baisoba a cewar sa  bayason ya  baiwa.bako yar sa Dan su danginsu auren dangisukeyi haka salame ta dage sai sa'idu aka wanke aka kaita garin raba duk da sun raina da arxikin sa'idu haka suka baro yar uwarsu suka koma damagara haka kuma rayuwarsu takansance itada masoyinta gwanin sha'awa malan sa'idu marayane su   biyu mahaifinsu ya haifa malan sa'idu shine babba sai mai bi masa atine  wadda bayan haihuwar tane mahaifinsu yarasu duk nauyin gida yadawo akan Maman sa'idu duk da lokacin. Bai wani girma ba sosai atine na karama itama haka dai sukaci gaba da rayuwa yau da dadi gobe da ciyo har Allah ya tashi kafadarsu  Atine kuma tayi aure ta auri Habu Wanda shi a birni yake zama da akayi aure yadauki matarsa suka koma can da zama sai dai insunxo ziyara 


Haka rayuwa tasance gwanin sha'awa salame da sirikarta bamai jin Kansu har aka wayi gari ta haifo santaleliyar yarta mai  ban sha'awa kowa sai santin 'yar yake kamar kasace ka gudu daranar suna ta zagayo aka saka mata Rukayya sunan mahaifiyar Maman Sa'idu suna kirantada 'yar baiwa kasancewar Allah yamata hkr tun tana karama batada hayaniya ko wanason Rukayya  haka ta taso cikin kulawa ga takwararta na sonta bataso taji kukanta ko wasa ake aka doketa yanxu nan zakaga Baaba ta daura ta yafa wai sai taji mafarin dukan yar lelenta abinka da yara kowa shakkar taba Yar Baiwa yake Dan kar yajaxama kanshi mita a wurin Baaba Dan har gidansu mutun takanje idai game da yar Baiwane 


Luv u all my fans

Maman ussee

๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH๐Ÿ™Ž5⃣

Maman Usman


Haka suka ci gaba da ratsa sabara har suka cinma titi sukaita tafiya tun Rukayya na kallon gari gari har ta gaji tai Bacci tasake farkawa kuma basu kaiba.


Ai kuwa basu suka isa garin sokoto ba sai misalin karfe 6 na yamma suna isa suka dauki hanyar arkila federal lowcost adai dai saitin wani gida ma dai daici yayi faking kamin nan ya umurci Rukayya data fito bayan ta fitone ya bude both ya Ciro mata yar Jakarta ya CE shiga mana ai nan gdnku ne ta dauki jakar ta shiga cikin gdn shi kuma ya bude get yasaka mortar a cikin gida San yabi bayan Rukayya.


Da sallamar sa ya shiga cikin gidan yana kwalawa Atine kira maman sajeeda maman sajeeda kin gammu sai yanxu ko oyoyo Abba cewar Abdallah yaxo da gudunsa mahaifin nasa yadaga sa sama yana dariya sweet boy ya ina mamanku da Auntynku suna  kitchen cewar fadil daya fito da niyar zuwa masallaci ya gaida Abban nasa yaja hannu Abdallah suka wuce Atine tazo ta rumgumeshi sannu da zuwa my Dear kunsha Hanya ya INA yar tawa banganta ba au ai na zata tashigo tin dazufa nace da ita tashigo Dan zanshigo da mota kila ko bata gane kofar bane oho bari in dubota  daga nan na wuce masallaci da an fara kiraye kiraye ko ta amsa da to.


Yar Baiwa kuwa tunda tashiga gidan takasa gane hanya kawai sai kalle kalle take ta Shafa nan ta taba can tanata mamakin ikon Allah can dai ta tsaya a wurin flawers tanata mamakin wai yau itace a birni muryar mutane datajine ya fargar da ita sai ta kewayo ta Inda ta biyo daga farko Rukayya INA kika shigane ko baki gane hanyar  bane ta sadda kanta kasa shima murmushi yayi ya ja hannun ta ya kaita har cikin gidan kamin ya koma zuwa sallar magrib,


Yarta  barka da zuwa ya su yaya da Baaba ta amsa suna nan kalau sunce na gaidaku harma da abu akace na kawo muku tau Rukayya bari yanxu kiyi sallah sai kiyi wanka kici abinci kinji ko bara na kira sajeeda taje dake dakinta saita nuna maki komai kinji ki saki jikinki kinji nan ma gidankune munan iyayenkine ki daukini a matsayin ummanki ki dauki Abban Abdallah a matsayin mahaifinki bakida matsalar komai kinji ta ammasa da to,


Kallon falon ta farayi Wanda aka kawatashi da kujeru masu kyau sai kayan kallon da dining area sai kuma dayan gefen store da kitchen sai dakin yara dake kusa da store gefe daya kuma room& falor ne sai dakin me gidan dake kusa da na sajeeda cikin kankani lokaci takarewa gidan kallo a ranta fadi take aljannar duniya dankari Ashe akwai ire iren wadan nan Abubuwan more rayuwa haka tab gaskiya maganar hausawane da sukace nazaune baiga gari ba.


Murya Sajeeda CE ta dawo da ita a duniyar tunanin da ta Lula  yar uwata zomuje kiyi sallah kinji ta amsa da to yayinda tabi bayan sajeeda dauke da Jakarta a ka suna shiga dakin wani sanyine ya doki fuskar Rukayya tare da daddadan kamshin air fresh sajeeda taja hannunata sukashiga bayi ta muna mata komai kamin nan ta fito ta barta me Rukayya zatayi inba sake baki ba ta fara tabe tabe ba abinda yafi Jan hankalinta irin gani. Kanta datakeyi a mirror sai murmushi take can dai sajeeda taji shuru ba labarin fitowar ta gashi ita har ta gama sallah amma Rukayya. Bata fito. Ba ta kwankwasa kofa yadai Ruky naji ki shuru koda matsalane a San nan ne yadawo haiyacinta ta tuna nan wai bayan gidane ta kunna tap tayi alwala San nan tafito tana fitowa sajeeda ta bata sallaya da hijab ita kuma ta fada toilet Dan tahadawa Rukayya ruwan wanka.


Bayan ta kamala sallah ne sai ta karewa dakin kallo ba komai bed ne kawai sai drower sai dressing mirror   ba laifi kam gidan ya tsaro sosai bayan tayi wanka  ta fitone sai ta Shafa mai kawai sajeeda CE tabata. Body spray tashafa Dan sajeeda akwai son kamshi zata girmi Rukayya kadan Ruky cewar sajeeda kidaukeni a matsayin yar uwarki kuma kawarki nasan bamu wani saba ba Dan ko munje can Raba ba wani dadewa mukeba su mummy sun muna bayanin komai bakida wata matsala kiyi sallar isha sai muje muci abinci kinji ๐Ÿ˜Š murmushi tayi hadi da yin sallah  tana idawar itama sajeeda sallar tafara yi  bayan takammala ne suka fita tare suka fito zuwa wajen cin abinci anan suka tarar da iyayesu har sun fara cin nasu sai Abdallah ne yace daddy wan nan CE new Sister dinmu ko ai na Santa a Raba take itace Baaba take cewa yar Baiwa ko aikuwa kowa ya fara dariya kai son ka cika surutu dayawa eah sunanta Rukayya daga yau sister Ruky kunjiko fadil yes momi suka amsa Abin yabaiwa yar baiwa sha'awa a ranta tace  lallai inbaka mutu ba zakasha kallo haka akaci abinci cike da raha ana kamalawa sai kuma aka fara labarai anan ne kuma Daddy yafara yiwa Rukayya tambayoyi. Ba laifi tasan wasu wasu kuma    bata amsawa sai kuma fadil da Abdallah suka CE su bacci sukeji Sajeeda ma taja Ruky sukabar mummy da daddy a falo.


Daddy yanisa gaskiya da ace Baaba bata amince ba da an cuci yariya kinga yanda takeda brain kuwa Dear Mummy tayi murmushi Allah dai yabamu ikon rike amana ameen  ta amsa nimafa azo asan yanda za'ai dani Dan ah gajiye nake ya kashe mata ido daya ta murmusa da tasan halin Mijin nata,


A bagaren su Sajeeda kuwa banda tadi ba abinda akeyi sun Dade suna fira kamin nan su kayi addu'a suka kashe wuta suka kwanta Rukayya kam godiya takeyi ma Allah wai yau itace a. birni dasunan boko.


Muje zuwa kuna tare da  Zeenat Yusuf maman ussee๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWA ๐Ÿ™Ž6⃣


Maman ussee


Tun da asuba mommy tashesu daga bacci Dan su yi sallah bayan sun idar ne kuma suka sake koma wa bacci kasancewar week end ne ba makaranta,

 Basu suka tashiba ba sai kusan 10:am wanka suka farayi kamin nan sajeeda ta ja hannun yar uwartata domin suje cin abinci Dan tasan yanxu kowa ya tashi dayake al,adar gidan ne atare ake cin abin suna fito gaida iyayensu sunka farayi kamin. Nan Abdallah da Fadil suka gaidasu suma mommy CE tace 'yata bawata matsala saiki Rukayya tace ba komai insha Allah daga nan kuma akayi saving din kowa yafara cin abinci amma banda Rukayya dantakasa cin abinci itasam bata saba dashi ba tafi son dumamen tuwo ko koko da kosai ko waina amma INA ita in cin wan nan kwamacalar,

Daddy ne ya kula da ita sai yakira sunanta Ruky ya.bakya cin abinci ne ta sadda kanta kasa cikin in INA tace a gida koko nakesha ko dumamen tuwo ai ko mexasuyi inba dariya ba Mummy CE tace ki Dan Dana mana kiji ai da dadi inbaxaki iya shaba to kici doyar mana tadai daure tayi spoont daya na damar miyar typeyocer din ai kuwa saita hau sha Sajeeda dariya kawai take kasa kasa ,


Bayan sun kammalane daddy yace dasu su shirya aje islamiya yaushi da kansa zai kaisu Dan ya mika Rukayya nan danan kowa yahau shiri kowa tafito cikin uniform din Islamiya Daddy yafito suka fice gabaki daya mommy kawai suka bari agidan,


Abakin get yayi fakin yayinda su Sajeeda suka nufin classes dinsu shi kuma ya nufi office din malamin makarantar yaga batar da Rukayya a matsayin daliba akayi mata tambayi ba laifi kan Dan ko a can Raba tana zuwa makarantar allo bayan an kamla aka bashi takarda yasa hannu yabiya kudi sai suka CE yakoma da ita gobe sai ta fara zuwa kuma da uniform suka sake fadamai dokokin makaranta yayi musu godiya ya ja Rukayya suka tafi a mai makon subi hanyar gida sai taga sunbi wata hanyar mexatayi in ba kallo ba ido ya samu abinci dai dai wata yar plaza taga Daddy yayi parking yace ta jirasa  batasan meyaje yiba bai jimaba sosai taga yadawo da Iedoji biyu a hannusa ya. bude set din baya daba kowa yasa su a ciki sa,ilin da yadawo yatada mota suka nufi hanyar gida,


Mummy suka tarar harta kammala komai na gyaran gida da Inda sukaci abinci sannu da aiki mommy yara ga kaya nasiyowa Rukayya da yadin uniform saiki bada dinki ayimata iri biyu iri. Nasu Sajeeda Dan gobe zata fara zuwa sauran kayan sa wane nixan fita  sai nadawo aff ana manta kinsandai makarantar  Boko suna jarabawa ne sai nadawo Hutu zan kaita zadai aci gaba da koya musu extra lesson kamin da dawo hutun Dan naga ba wani Hutu mai yawa bane murmushi tayi hadi da yimasa godiya da fatan  alkhairi,

Rukayya kuma tana zaune ta kurawa TV Ido ko kyabtawa batayi mummy ta dafata tace muje kitayani gyaran daki sai mu Dora girkin rana Dan su sajeeda sai 4:pm zasu dawo ta fice yayinda Rukayya ta rufa mata. Baya tana nuna mata abubuwa da  yakamata ta kula dasu wan nan kenan,


A cikin yan kwanaki n da tayi a gida. Bata fuskantar komai sai farin ciki ga soyayya da yan uwanta ke nuna mata suna debe mata kewa sosai sun shaku da sajeeda inka gansu gwanin sha,awa komai tare sukeyi Dan ko a Islamiya tare suke komai sajeeda itace take koya wa Rukayya wasu Abubuwan da bata gane ba cikin sa,a kuwa da am fada ta rike shikenan malamansu har mamakin irin Baiwar da Allah yayiwa Rukayya suke gashidai bawani dadewa tayi ba amma inka ganta saika rantse ta shekera a cikin islamiyar gida kuma ga lesson ana musu badama tana kawo wuta sosai Daddy yasan bayada haufin inya kaita skull za,a sakata aji daya da Sajeeda dayake ita jss 2 take, Tun tanajin kunyar saka wando da Riga harta saba Dan kuwa yanxu Rukayya ta goge dama can ita kai waye ne da ita  batada matsala in basuda lesson itada Sajeeda suke taya mummy aikace aikacen gida dayake anyi Holiday.


Maman ussee๐Ÿ˜˜ Ina Alfahari da Ku my fans๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž7⃣ 

Maman Ussee 


Haka Rayuwarsu taci gaba da kasancewa gwanin sha,awah har holiday ya kusa karewa yau ya kasance Sunday kowa da kowa na falon gidan anata firar duniya   gwanin dadi fuskar kowa cike da annashuwa da anuri Abdallah ne yace Daddy gobe Holiday zai kare kuma kasan kamuna alkawarin zaka mana shopping yau ko Fadil ya amsa eah little bro Mummy tace harda ni kenan za'aje shopping din Daddy yace OK to Ku shirya sai muje tare kunji  yes Daddy suka mike Dan shiryawa Rukayya an zama yan gida yanxu kowannen su yafito cikin shiri Rukayya da Sajeeda jalabiyace a jikinsu dark blue sukayi rolling abin yayi kyau fadil da Abdallah kuwa Riga da wandone suka sa mummy itama Doguwar rigace ta shadda taji kwado kai familyn fa sun birgeni haka suka fito suka shiga mota Mummy dasu Sajeeda a Baya fadil da Abdallah a gaba  asu zarce ko inaba sai a Zabira shopping mall nan kowa yayi ta zabar abinda yakeso Rukayya dai kasa daukar komai tayi Dan ita kunya takeji Sajeeda CE kedaukar komai Biyu inta dauka saita daukar wa Ruky bayan sun karene sukaje wurin bill akayi bill Daddy yabiya suka sake fitowa kowa sai kallon su yake nusamman Ruky da Sajeeda kamar yan biyu ba karya Allah yayi  Halitta Dan ko Sajeeda ba bayaba a fagen kyau, Daddy bai zarce dasu ko,ina ba sai Daddy's smart anan sukaje suka ci abinci suka zaga gari sosai kamin nan suka dawo gida.


Gab da magrib suka dawo zubewa sukayi a fallo kowa ya gaji Dan yau sunsha yawo sun more sosai gsky bayan su hutane Daddy yaja su Fadil da zuwa masallaci Mummy kuma ta wuce zuwa dakinta yayinda da umurci su Sajeeda dasuje su yi sallah suma kuma su shigar da kayan ciki haka suka kwashi kayan zuwa Inda yakamata su  adanasu. Bayan sun idar da Sallar Isha suka fito bayan aka ci gaba da hira can Daddy Yakira sunan Rukayya, Rukayyatu ki shiryafa gobe zaki soma zuwa skull insha Allah saboda haka saiki shirya kinji murmushin jin dadi tayi yayinda da ta CE nagode Daddy Allah yakara girma bakomai ai kidage dai kinji ko to 'ya ' yan Daddy aje ayi bacci saboda a tashi da wuriko kunji yes Daddy af na manta Ga uniform din Ruky can a bed dina Sajeeda jeki kidauko mata gobe sai a shirya da wur wuri kinji tau Daddy  bakida wata matsala Rukayya. Nariga nayiwa principal magana interview kawai za a maki su zasu baki komai da komai saboda haka kidage kawai inkiyi kokari za a sakaki class daya da 'yar uwarki Sajeeda tam ta amsa suka fice dakin su kowa yayi addu'a ya kwanta yayinda 'YAR BAIWAH take farin ciki sosai mafarkin ta yakusa yazama gaskiya.


Maman Ussee๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž 8⃣ 

Maman Ussee 


Monday morning tun 6 suketa shirye shiryen zuwa skull Sajeeda CE ke nunawa Rukayya yanda zatasa kayan skull din ,kai gsky fa kinyi kyau tawan kinga yanda skull uniform din nan suka karbeki ta kashe mata idon daya Ruky ta kaimata duka ta goce suka fito falor sunata dariya yayinda su Fadil ma su. Shirya tsaf Daddy kawai suke jira bai wani jima ba ya fito sanye da kayan shi dagani shima aiki zaije daya aje yaran,  ba bata lokaci Mummy tai musu addu' a suka fice dukkansu suna daga mata hannu,


Bayan sun shiga mota Daddy ya tuka zuwa skull din dake dai dai Bafarawa east, garin yacika sosai da mutane kasan cewar yau Monday masu zuwa skull na fita yayinda masu zuwa aiki ke kama ga bansu da zuwa aiki kai tsaye daddy cikin makarantar ya danna motarsa wato KEY SCIENCE ACADEMY, bawani bata lokaci Sajeeda dasu Fadil suka nufi assembly yayinda Daddy ya nufi principal office da Rukayya bayan yagabatar da ita a fadamai rules din makaranta ya amince kamin nan aka bashi takarda yasa hannu yayi godiya sosai ya wuce yayinda PC ta kira senior master domin a iyiwa Ruky inter view da Name dinta aka fara ta amsa Rukayyat  Sa'eed  bayan nan kuma sai aka cigaba da yimata sauran questions tana amsawa yanda yakamata, mintuna kalelan aka  bata class yayinda aka kira, class master dinsu ya rubuta name dinta a Register kuma aka umurce shi daya kaita ya gaba tar da ita wa yan class as a new student kai tsaye   , Jss 2 blocks ya nufa da Rukayya kamar dai yanda Daddy ya. Bukata cikin sa,a kuwa ajinsu Sajeeda ne  bayan shigarsu, student suka mike tsaye,

Good morning sir, morning how r u today, we are All fine sir, OK sit down,

Anan yagabatarda ita yayi kiran register kuma ya umurci class rep data bata set shikenan yafita Dan yagama aikinsa, 

Fitarsa keda wuya Sajeeda ta doka uban tsalle ta rungume Rukayya tana murna sosai, Hi kinga Allah ya amshi addu,a na ko so yanxu muna class daya if u did not understand anything just ask me ๐Ÿ˜Š murmushi kawai Ruky tayi hadi da samun set bayan nasu Sajeeda yayinda su Muhibba yan sit dinsu Sajeeda suke tambayar ta dama tasantane eah yar uwatace she's my sister daga nan kuma aka cigaba da gaggaisa irin na new students da old kundai gane๐Ÿ˜œ uncle me English ne ya shigo da yake  ba musulmi bane ya gabatar da lesson dinsa ya kuma basu pappers dinsu na fist term bayan ya kare sai mai science yashigo shima yagabartar da nasa lesson din kamin nan aka buga aje break fast  Sajeeda da Rukayya tare suka fito zuwa dinning area anan ne Sajeeda ta ringa nunawa Ruky abubuwa da dama wadanda bata saniba da kuma Inda ake komai da komai haka suka kasance har time dinda aka koma class ba laifi Rukayya ta dage sosai sai sun hada Kansu ita da yar uwarta  ba abinda basayi tare har lokacin barin skull din yayi suka shiga skull bus Dan dama ita ke mayardasu gida saidai da safe Daddy ya kawosu su Fadil da Abdallah  bangarensu daban kasancewar su a primary suke sunada masu bus din duk da skull din dayace amma kuma Nursery daban primary daban ss da jss ne kawai a hade Sajeeda da Ruky suka shiga tare aka yita sauke wadanda ke kusa yayi da aka zo unguwarsu suma suka sauka sunayiwa sauran yan mates dinsu bye bye sai mun hadu gobe inji su Hibba sajeeda ta amsa da to,

Bayan su shiga gida suka tar rar dasu Fadil da Abdallah har sun dawo kasancewar su 12:30 ake tayar dasu sukuma sai 1:30 suke tashi Daddy. Baidawoba haka suka cire uniform dinsu suka sake wanka kamin nan suka saka uniform dinsu na Islamiya da time yakusa yi.


A RABA FA?


Tun bayan tafiyat 'Yar Baiwah Baaba kullun cikin cewa take harda Dan zazzabin ta na kewar jikar tata kullun ta lisafe da ko kwana nawa yar baiwa tayi a birni kullun tunanin ta yanxu a wane hali jikarta take sai dai zuciyarta tana hayamata duk Inda yar baiwa take to addu,ar da take mata yana tare da ita da A kullun baaba sai taiwa Rukayya addu,a kuma batason  taji lbrn komai indai  ba firar mutuniyar ta bane hakan CE ta kasance ko a wuri mahaifinta sai dai yana da jarumta  baya nunawa dankar ya karyawa baaba zuciya haka suka kasance gidan shuru shuru har na tsawon sati biyu tun basu saba ba har yazama jiki suka saba kowa yadan fara sakin jikinsa aka dawo yanda ake da saidai kuma in an tuna ayi kewa sabo kenan.


Maman ussee๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž9⃣

Maman Ussee

Ruky da Sajeeda zaune a dakinsu sunata fira sai dariya kakeji wow gsky nazata inaje skull din nan zan fuskanci Matsala, ashe ba haka nan bane, kai dadina dake tawajena tsoro gareki, ninasan ba abinda zai faru kawai dai kedince akwai tsoro. Kinga tashi kar muyi latti kinsan halin mutumin naki mai tajwid akwai disgi ni kuma na tsani mutun mai disgi hakafa ranar safa CE kawai bansaba  ya hanani shiga ajin Ruky tace OK kinsan dai gobe akwai Hadda ko saboda haka yau. Ba, bacci Dan kar muje bamuyiba kinga gbe akwai skull cox Hutu yakare yanxu da dare zamu rika yin Hadda dinmu,


 Bayan sun kammala ne suka fito sanye da uni din Islamiyarsu sama sama suka ci abinci Dan karsuyi latti ayi musu duka sauri sukeyi Rukayya rike da hannun Fadil yayin da Sajeeda take rike da hannun Abdallah Dan a kafa suke zuwa Islamiya tun bayan ranarda Daddy yakaisu, 

Sunci sa,a suna shiga ana tare yan latti kai tsaye ajinsu suka nufa. Bayan sun aje su Abdallah a nasu ajin.

Ai kuwa basu tsiraba Dan koda suka je mai tajwid yariga yashiga hkr suka fara basa dakyar suka ci sa,a yabarsu suka shiga bayan shanyasun da yayi a waje haka yakaraci darasin sa yabar ajin.

Basu suka tashi ba sai misalin 6:pm aka tayar dasu kowace daliba ta kama hanyar zuwa gidansu,  Ruky da Sajeeda tare da yan kannesu suma suna dai daga cikin masu zuwa gida kasancewar magrib ta kusa da isarsu gida kowane ya nufi dakinsa Dan bayarda farali suna idar da Sallah falo suka xo , a nan suka tararda mummy itama ta fito  yaran Daddy sannuku har kunyi sallar ne eah OK to Allah ya karba ya bada lada suka amsa a tare ameen mummy, yadai Ruky hope ba matsala a skull ko karki damu da sannu zaki sabane fatana kawai Allah yataimaka yabada sa,a kuma a dage kunji eah suka sake amsawa, haka sukata fira jefi jefi kiran sallar Isha ne ya tayardasu bayan sun kammalane suka fito domin cin abincin dare,

Anan suka tarar da Daddynsu Dan rabon da suganshi tun safe daya ajesu a skull gaida shi suka fara kamin nan kowa ya zauna a set dinsa mummy tayi serve din kowa akaci akasha aka koshi sai kowaya kama gabansa yayinda Ruky da sajeeda suka fara tilawar Haddan su dakuma assignment dinsu bayan su kammala sukayi addu,a suka kwana sai. bacci.


Kashe gari haka ta kasance tun wuri suka kimtsa suka fito inka gansu kanar wasu twins gwanin sha,awa yau ma Daddy ne yakaisu skull daga nan ya wuce GT Bank da acan yake aiki bayan an kare Assembly kai tsaye kowace daliba ajinsu ta nufa Dan daukar darasi Sajeeda da Ruky a tare suke tafiya har class dinsu kowace ta zauna a set din ta kamin class master yaxo yakira register daga nan kuma  

Malami mai lesson ya shigo ya fara gabatar musu da lesson.


Maman Ussee๐Ÿ˜˜ 


Naga sakonku nagode sosai da kulawa nasoyana Allah yabar zumunci.


๐Ÿ™Ž YA RBiAWAH ๐Ÿ™Ž 1⃣0⃣

Maman Ussee


Time din break yayi Sajeeda da Ruky suka fito waje class sunayin break yayinda sauran student ke lamarin gabansa, Ruky nikuwa Sajeeda kinsan abinda yake bani mamaki a,a saikin fada wan nan malamin nan na daxu mai disga mutane din nan kinga yanda yabar ummy nata zuba surutu ya kyaleta amma na tabbatar da wani member din class ne daya sha zagi yau kuma na ga sai wani shige mata yake kodan yaga tafi kowa girmane a class din, hey are u jealous ๐Ÿ˜€ Ruky takai mata duka wane irin jealous kuma ni ina ruwana dashi kawai dai naga hakan baidaceba ne shiyasa na gaya miki OK to kawo takalminki na ajiye miki kije ki gaya musu ustaziya Rukayyatu 'YAR baiwa ๐Ÿ˜ dalla Banason rainin hankali daga kawai na fada miki Abu shikenan sai ki wani canja min magana ๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€ dariya sajeeda tayi hardasu kyalkyatawa kamar zata fado kasa aiko Ruky ta ji haushi ta kwashi kayanta fuu ta fice daga wurin hava ke kuwa sorry mana tsayani muje tare INA ko saurarenta bataiba ta fice class abinta sai daga baya ta saiko suka shirya kamin adawo break.


Sannu sannu.bata hana zuwa sai dai a Dade ba,a kai  ba yau su Ruky zasu zana end of second term examination, a cikin skull kuwa bawanda baisan Sajeeda Abubakar &Rukayya Sa,eed ba komai nasu atare sukeyi duk Inda kagansu tarene ba abinda yake rabasu ko a gida ma hakan ne gasu da ilmi uwa uba kyau gasudai ba wani girmane dasu ba Dan daka gansu zaka yarinta karara a tare dasu sai dai sunada ladabi ga girmama na gaba dasu a class inkaji suna surutu to lallai Abu mai mahimmanci suke tattaunawa. Baruwansu da wasu frnds sudai barsu da karatu Dan kullun abinda Daddynsu yake jaddada musu kenan kosunyi fada to yanxun nan zakaga sun shirya al,amarinsu yana mutukar.birge jama,a ko unguwarsu  bamai cewa sun tsokaneshi Dan su karatun ne kawai yasha musu kai alhmdllh cikin sa,a suka fara Rubuta exams dinsu har suka karashe akayi holiday, 


Murna gurin Rukayya ba,a magana Dan dama ta matsu ayi Hutu Dan taje Raba dama Daddy yace da anyi Hutu zasuje tare suyi one week sai sudawo sabida islamiyarsu dayake sunyi nisa sosai, bayan sun dawo gida da kwana  biyar suka daga sai Raba gabaki dayansu harsu Fadil da Abdallah ai kuwa kuxo kuga murna wurin Baaba kamarme taga yan jikokinta musamman ma Yar baiwa taga yanda tayi Haske ta goge hardasu kiba gwanin sha,awa kai lale marhabin da yan sokoto cewar Malan sa,idu nan nan kawai yake da 'ya'yan nasa yanajin wani farin ciki a ransa yarsa CE ta dawo haka tubarkallah masha Allah,  bayan an nutsa kowa yaci ya koshi aka fara sabuwar fira yayinda suka gode sosai da namijin kokarin da Daddy yayi musu godiya suka ka rayi da fatan alkhairi, satinsu daya a Raba suka juyo yar baiwa kawai suka bari koshima badan sunsoba saidan rokon da Baaba tayine shi,isa suka barota ta kara sati sai Daddy yazo ya dauketa sukoma, bayan kwana biyu Baaba na zaune itada Rukayya suna tadi take tambayarta bawata matsala daiko eah bakomai lfy lau wllhi bakiga yanda ake bani kulawa ba sosai da sosai to madalla ai hakan akeso Allah dai yasaka musu da alkhairi Rukayya ta amsa da ameen amin shiyasa nake sonki Baabata dankin iya addu,a ๐Ÿ˜€ dariya Baaba tayi tace ja,ira har yanxu dai sakarcin naki nanan Ruky tace to in  ban maki ba wanikeda shi Wanda yafiki ai kekadaice dagake. Bakari ๐Ÿ™Š tabdi wai yar baiwah yaushene kika iya surutu haka lallai zaman birni ya saka ki iya magana ๐Ÿ˜ณai baaba Dan baki zauna da Sajeeda bane haka take kamar parrot indai surutune uhum menene fara kuma me Ruky zatayi in banda dariya aikuwa Baaba takaimata duka ta goce tsaya kiji parrot akecewa inaga sai naje sake skull dinmu kin kara wayewa ja,ira kekam dai Allah ya shiryeki ta CE ameen tana murmushi.

Maman Ussee๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™ŽYAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž1⃣1⃣

Maman Ussee๐Ÿ˜˜


Satin Rukayya biyu daddy yazo yadauketa suka koma sokoto cike da kewar iyayenta musamman ma Baaba dasuka shaku sosai,

Haka Rayuwa taci gaba da kasancewa yau farin ciki gobe akasin haka dama ita rayuwa haka ta gada , amma a wurin Rukayya abin ba,a cewa komai Dan kullun cikin farin ciki take yayinda duk tayi sallah saita Roki Allah yasa kama daddy da aljannah hakama mummy dakuma iyayenta. Haka suka karaci holiday dinsu har ya kare duk Wanda yasan Rukayya ada idan yaganta a yanxu bazai ganetaba inhar ba farin sani yayi mata ba Hutu kwanciyar hankali haiba kwarjini duk sun baibayeta batada wala matsala a skull ma hakan ne Dan so dayawa tasha samun kyaututuka da dama awajen malamai kai harma da students akan baiwar da Allah yayi mata ilmi. Ba,a magana Dan ko quiz za,ayi to Ruky da sajeeda na ciki haka ma divert ko inter schools compotions za,ayi to dolene asaka yar baiwa ga tada da speach mai dadinji dakuma saurare takowane fanni gata ilmin addini Dan kuwa saura kadan ta Haddace alkur,ani mai girma, Sajeeda namatukar son Rukayya kamar yan uwanta na jini haka take jin ta kamar uwa daya uba daya suke ba,abinda Rukayya zata CE tanaso Sajeeda. Batace tana sonsa ba koda kuwa. Baimata ba a duniya inhar kanason kaga. Baccin ran Sajeeda toka taba Yar baiwa haka ma ko a wurin Rukayya batason ko kadan taga yar uwarta cikin damuwa kuma sajeeda bata taba jin haushi ko kyashin Rukayya tafita ilmi ba duk da dai itama tanada nata iya gwargwardo wadan da basu sansuba cewa ma suke yanbiyu ne kasan cewar tun bayan dawowar, Ruky a gidansu Sajeeda Daddy bai taba ban-ban ta musu kayaba kai harta takalmi da sarka iri daya ake saya musu hakan yayiwa mummy dadi sosai yanda Daddy yadauki Ruky kamar sajeeda baya taba nuna wani banbanci duk abinda zai iya yiwa sajeeda to tabbas zai yiwa Rukayyama, duk da yasha samun yan korafe korafe a gurin Abokanansa dakuma wasu amma indai ya fahimci ba maganar arzikice takawo kaba, tun daga ranar kun raba hanya dashi bayason sa ๐Ÿ‘€ ido Dan yasan duk abinda yayiwa Rukayya Dan Allah yayi kuma yanada tabbacin zaisamu ladansa a gurin Allah .

Haka abin yake ko a wurin mummy indai kawayenta suka fara kushe Rukayya nan da nan zata watse mutun komai dangartakar ta dashi kuwa ita a ganinta ko ba ita, ta haifi yar baiwa ba ai Abbanta ciki daya suka fito dashi kuma duk abinda zai cutar da Rukayya bata sonsa Dan tasan duk abinda tayi Dan zumuncine kuma Dan Allah da fatan samun lada a gun Allah. ( Anya a wan nan zamanin zaka iya samun Dan uwanka maisonka da kaunarka saboda Allah kuwa zumuncin yanxu sai a hankali kowa nasa kawai yasani Ya Allah kabamu ikon so da kuma kauna ga yan uwanmu, Ameen ya Ra bbi).

Rukayyace zaune a falo tana koyawa su Abdallah home work dinsu Sajeeda kuma na gefe tana Dan duba wani English litreture mummy kuma ta fita da yake yau ba Islamiya kowa na abinda yasa a gaba sallamar Daddyce ta sa kowannensu dago kansa sama Dan amsa sallama Sannu da dawowa Daddy, yauwa yaran Daddy sannunku da gida umman taku har yanxu bata dawo. Bane wan nan zuwa biki haka har yamma tayi gashi inaso muje gidan wani amininah da muka Dade bamu haduba baya kasar jiya yadawo muje muyimai. Barka da dawowa ko bakwaso ๐Ÿ˜Š sukayi ga aki dayansu Daddy muje basai munjira mummy. Ba kawai cewar Sajeeda yes Daddy kinji Abdallah , no gsky daddy ajira sai mummy tazo inyaso sai mubarshi sai anjima da dare muje Daz my gal shiyasa nake sonki dan kinada hankali ba kamar wadan  nan ba Sajeeda ta turo. Baki fadil kuma gwalo yayi mata ta kaimasa doka ya goce ya boye bayan Sister Ruky plzz my sist kice karta dake ni to meye namin gwalo ai nima watarana Daddy zai yabeni bakaman kai ba ko little bro cewa da Abdallah eah hakane Sist kyalesu shida sister Ruky, muma watarana rana sai mun musu gwalo dat my bro oya give me five suka tafa ita dai Ruky murmushi kawai tayi itama tace da fadil leave them kaji sweet.bro dina itama sajeeda ta kwai kwayeta kaji sweet    bro dina Ruky ta jefa mata pillown kujera ta gudu ita da Abdallah zuwa daki hmmmm Sajeeda da Ruky kenan everlasting friend


Maman Ussee๐Ÿ˜˜ 


I love you All my fans ๐Ÿ’‹


๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž1⃣2⃣

Maman Ussee๐Ÿ˜˜


Misalin karfe 8:30 mummy da 'ya'yata suka shirya cikin shiga ta alfarma kowansu yaci gayu, Daddy ne ya leko ohh wai haryanxu baku kammala bane koyaya? Nop we r ready kai kadai kawai muje jira OK let go.

Gida ne na alfarma Wanda ya amsa sunansa gida, ba karya naira tasha kuka a gidan Dan an zuba dukiya a duk fadin Sama road ba gidan da yakai kayatuwar gidan kai tsaye Daddy cikin gidan ya nufa yayinda mai gadi ya wangale get suka shiga,

Wow Aljannar duniya lallai gskyr hausawa ne dasuka CE na zaune baiga gariba habar gidan tamkar a kasar turai duk da dai darene amma tamkar rana saboda hasken lantarki, gefe daya motocine a gibge, an jera su Reras a car pack, sai kuma a center akayi wani Dan round aka shuka flowers ruwa nata bulbulowa kamar korama hasken fitillu ya haske ko,ina ba, cewa komai dayan gefen kuma wurin hutawa ne da kujeru sai rumfa tsayawa na fada muku gayatuwar gdn bannar lokacine, iya haduwa gidan ya hadu sosai kai tsaye car pack Daddy, ya nufa yayi packing, kamin nan suka fito zuwa cikin gidan,

Wornder shall never end kunga Fallon gidan kuwa๐Ÿ˜ณ wasu kayatattu. Royal chair's, na hango kai sun hadufa ba karya masu kudi suna sha,aninsu. Gefe guda Dining area ne dauke da wani katon dining table tsarin falon komai red an white ne kai hartama da paint din falorn red ne da white kai nasha kallo fa saura kadan nadan saki layi nadai yi sauri na saita kaina Dan karsu dagoni๐Ÿ˜œ,

Daddyne yafara zaunawa tare dasu Abdallah kasan cewar shi ba bako. Bane a gidan in yazo kai tsaye yake shiga ba wani dar dar, mummy kuma tare da Ruky da Sajeeda, 

Wata matace tashigo da ganinta mai aikin gidance sannuku da zuwa  Bari na kira Hajiyar tana sama  bawani bata lokaci aka fara cika musu gabansu da cima kala_kala, yayinda kuma Daddy ya daga waya ya sanarda abokinsa isowarsu Dan yasan halin matar gidan inta itane saidai su kwana anan  baxata sakko. Ba , Bayan min tuna kadan sai ga shinan ya sakkon mutun mai baiba da kamala ga kwarjini, da murmushi sa ya tarbi abokin nasa  ya rungumeshi aka fara gaisuwar yaushe rabo,

Alhaji Basheer kenan Amini kuma uban gida a wurin daddy mutun ne mai son mutane kowa nasane yanada daraja Dan Adam  baya wulakanta talaka duk Wanda yaxo gunsa zai tarbeshi kamar nasa ga taimako sabanin uwargidansa Hajya kubra macce mai fada ga nuna isa batason talaka ya rabi mijinta Dan ma Alh Basheer na tsaye ne kuma yana takwarata da Allah kadai yasan tsiyar da zata tsula. 'Ya'Yansu shidda Abubakar Umar Usman da Aliyu sai kuma twins Afra&Afnan bayansu bata sake haihuwa. Ba, Abubakar shine babban dansu sai Umar ke bimasa duk da bawata tazarace tsakaninsu ba Usman da Aliyu ma bawani nisa a tsakaninsu,  bayan ta haifi Aliyu tadan jima bata sake haihuwa ba har an cire rai sai Allah yabata cikin afra da afnan Alh Basheer yayi murna kwarai da gske kasancewar  bashida yara mata duk maza ne adalinlin hakane su Afra suka taso cikin gata sosai ba iyaye bakuma ga yayunsu ba .


 Bamai takura musu sai abinda sukaso sukeyi tun suna yara abindai ba,a cewa komai idan kanaso kaga fadan Hajya to taba mata yan biyunta  ba abinda sukeso a duniyar nan Wanda Hajiyarsu bata musu(Jan kunne๐Ÿ‘‚Hatara iyaye mata mukula sosai da sangarta 'yayanmu dominsu amanace awanjemu ki๐Ÿ‘‰ sani Allah zai tambayeki game da tarbiyar da kika. Baiwa 'yayanki dolene mu tsawatar musu Dan ance kaso naka duniya ta kishi inkaki naka duniya ta soshi haka zancen yake Allah yasa mugane Ameen) 

Alhaji Basheer rikaken Dan kasuwane  kuma shahararren mai kudi Wanda ketashen kudi a wan nan zamani duk da dai ba sa,an daddy. Bane kusan Allah mai hadin zumunta. Wata rana ne Alhaji. Basheer yaje Bank dinda daddy ke aiki domin ya cire wasu kudade nashi sai aka samu akasi bai samu yanda yakeso ba kuma gashi tafiya zai yi yarasa mafita shine daddy ya taimakesa yasamu kudin iya adadin abinda yakeso to tun daga ranar yazama duk indai kudi yakeso a bank dinsu Daddy to Daddyn kawai zai nema hartakai ma daddy da kansa ya sha kawoma Alhaji Basheer kudi har gida wan ne yasa sukayi sabo har Alhaji Basheer yakan Dan saka daddy wani abu Wanda yake na sirri kuma ayimasa yanda yakeso batare da ansha wahalaba wan nanne dangantakar Daddy dakuma Alhaji Basheer ,

 Bayan sun gaggaisa Ruky da Sajeedama suka gaida shi cikin girmamawa, sosai yaran suka bashi sha,awa ya yaba da hankalinsu sosai har yake tambayarsu ajinsu nawa da skull dinda suke suka bashi amsa kai tsaye ya CE gaskya kunada kokari so keep it up duk Kansu dariya sukayi sukace Insha Allah , Jim kadan sai ga Hajya Kubra manta manta anfito ana wani tako daya bayan daya kamar,batason taka kasa tana wani nuna is a ,daga saman stairs falon ta nufa gurin da su Daddy ke zaune anata labaran duniya shida Alh su mummy kuwa hankalinsu nakan palasma TV dake jikin  bango suna kallon news.

Au Alhaji wai  baki mukayine,murmushin taikaici yayi, yana mai jinjina hali irin na matarsa , Eah kawai yace mata yaci gaba da abinda ke gabansa .

Sannuku kawai tace dasu takoma warta dama ko sakowarda da tayi taga Alhaji ya matsa mata da kirane shine ta sakko taga meyene gaidata su Sajeeda suka shiga yi a dakile ta amsa tayi ficewarta Alhaji baiji dadin abinda tayi ba ammato ya ya iya. 

Wuraren 10:30pm suka yima Alhaji Basheer sallama ya dauki kudi yabasu sukaki karba aikuwa yayi juyin duniya sukaki saida yanuna bacin ransa kamin nan, daddy ya umurcesu dasu karba kishi Sajeeda CE ta amsa Ruky kam ki tayi saboda kunya. 

Muje zuwa


Maman Ussee๐Ÿ˜˜

Kuyi hkri aiki ne yamin yawa shiyasa but insha Allah gobe zanyi mai yawa nagode sosai masoyanah๐Ÿ™


๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž1⃣3⃣


Maman Ussee


Da isarsu gida kowa, yanufi dakinsa Dan kwantawa, a huta yaukam ba, zancen fira , Ruky da Sajeeda wanka kawai sukayi sai alwala kowacce ta nemi shifida, sai. Bacci 


Kashe gari tun safe suka tashi bayan sun kammala ayunkan gida kai, tsaye dakin mummy suka, nufa bayan sun gaidata da. Ne , 

Suka nufi dakin daddyn su, shima sukayi gaidashi, kamin nan sukaje suka ci gaba da sauran yan aikace aikacen gida Dan mummy bata barinsu girki saidai ta nuna musu amma har yau bata sake musu girki ba acewarta su yarana har, 

Yanxu baza ta sake musu komai ba, sai nan gaba iya kacinsu shara sai wanke wanke , da sauran Dan abinda , baza,a rasa ba.

Time din break nayi kowa ya halara mummy tayi saving din kowa, aka fara cin abinci , bayan an kammala ne Daddy ya ke tambayar su daya bayan daya koda matsala ne Dan,

Dama haka yakeyiwa kowa. Daga nan duk mai bukatar wani abu saiya fada kowa yace , Bakomai Daddy ya wuce zuwa  Bank. Dan yau ba skull ana hutun good Friday ne yaran yau basa zuwa skull , Bayan sun kamala aikinsu sai suka tambayi mummynsu sunaso, ne suje dubo wata yar class dinsu datake, nan unguwarsu . mum tace dasu karsu Dade suyi sauri su dawo , tau suka amsa kamin nan suka dauki hijabs dinsu,

Suka ficce daga gidan , gidansu Hafsat suka nufa nan ne bayan layinsu da sallamar su suka shiga cikin gidan, bayan sun gaida umman Hafsat sai suka shiga dakin Hafsat din, bayan yan gaishe gaishe , suka fara fira irin nasu na yan makaranta,  Basu suka dawo ba sai bayan an taso daga salar jumma,a dayake yau Friday ne , kai tsaye gida suka nufa koda sukaje mummy tayi baki bayan sun gaida sar da bakin mummy dakin su suka shiga suka sayi sallah bayan sun kammala,  suka fito suka Debi abincinsu suka koma dakin su, sunata wasa da dariya batare da wata damuwaba yan biyun mummy kenan!!! 


Maman Ussee๐Ÿ˜˜

Note

Dan Allah kuyi hkr wllhi kwana biyu bana jin dadin ne amma yanxu naji sauki zanci gaba dayi muku insha Allah nagode sosai da kulawarku๐Ÿ’ฏ๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH๐Ÿ™Ž1⃣4⃣


Maman Ussee


Safiyar Talata tun safe suka tashi suka fara shirye 2 na zuwa skull, bayan sun kammala da komai da komai Daddynsu yadaukesu yakaisu bayan ya ajiyesu sai ya ficce zuwa wurin, aikinsa Su Abdallah da Fadil ma nasu bangaren suka nufa, yayinda Sajeeda da Rukayya, suma suka wuce, zuwa assembly, ground, 

After ankare Assembly duk student's suka ficce, zuwa classes dinsu Dan daukar darasi, bayan Class master din su Ruky yashigo ya kira register, sai aka fara gabatar musu da lesson din nasu .

Kwanci tashi baya hana zuwa yau har su Sajeeda da Rukayya sun rubuta JSCE lafiya lau murna gurin Daddy da Mummy kamar me, Haka Rayuwarsu taci gaba da kasancewa har lokacin da exams dinsu ya fito Daddy yayi musu alkawarin zai canja musu skull dan ya yaba da kokarin yaran yayinda Alhaji  Basheer shima yayi alkawarin zai bada nasa contribution, din idan zasuje gaba Dan shima yaran suna birgesa, more especially

Tarbiyarsu ga girmama nagaba dasu, 

Kamin karshe Hutu Daddy yakai Rukayya da Sajeeda Raba domin suyi hutunsu acan , sunsha Hutu kam Dan saida sukayi kusan wata Daya acan  ba karamin Dadi hakan yayima Baaba Dan tana matukar son Rukayya , bayan sun dawo, Hutu kuma sai suka dukkufa zuwa Islamiya Dan dama sauran kadan su sauke kuma Daddy yayi musu alkawarin sai sun sauka zai kaisu SS one Dan dama hakan sukeso badan ma sunje Hutu a Raba ba da yanxu sun sauke  hakan sukeyi kullun akaci sa,a kuwa Rukayyace ta fara sauka bayan Sati daya Sajeeda ma tasauke Murna da Daddy yayi. Bata misaltuwa kullun saiyayiwa yaran sa addu,a Allah yakara musu basira Alhmdllh Addu,arsa ta karbu Dan kuwa ga sakamakon hakan yagani.

A tare daddy ya hada musu walimar sauka a gida bayan an gabatar musu da wata walimar a makaranta, ba laifi kam an taru  bayan an gabatarda yan naseehohi akayi musu addu,a sai yan kayan rabo da akayi  bayan an rufe taro da addu,a kowa ya watse,

Daddy ne zaune da yaran sa anata wasa da dariya uhuum Abban yara wai mexai hana ka kokarta ka kai su Iman ne naga can ana karatu sosai ko cewar mummy Daddy ya nisa eah haka ne amma kudin ne , sunyi yawa kuma nafiso nakaisu Inda zasuci gaba da Hadda Dan ,dama nayi shawara zan kaisu, Sultan Abubakar Maccido Islamic college, koya kika gani ,ai Ruky da Sajeeda najin haka su fara murna yeee Thanks much Daddy we love u Daddy Allah yakara budi sukaje suka Rungume Daddyn nasu suna murna ,daga nan kuma aka ci gaba da hirar duniya kamin time din sallar magrib yayi , Dad yaja su Fadil zuwa masallaci yayinda su Sajeeda da Rukukayya suka shiga cikin dakin su domin gabatar da Sallar magri b.

Bayan kwana biyu Daddy yadaukeso sai new skull dinsu dayake akwai masu yin day a ciki akwai kuma masu yin boarding Daddy baya da Ra,ayin barinsu suyi boarding, Day yasaka su bayan ya yayi musu registration, da duk wani abubuwa da yakamata sanda akayi musu interview, aka basu classes saidai ba,a ajesu a class daya ba kamar yanda sukeso ,  badan  ransu yaso ba,haka suka hakura Dan bayanda zasuyi, haka suka zauna a new skull din taso dayake akwai Dan banbanci kadan Dan yanxu sai 4:pm suke tashi dan, skull din hade take da Islamiya Ruky da Sajeeda baruwansu dashiga harkan da banasu ba hakan cema tasa basuyi wasu sabbin kawayewa ba Dan acewarsu kowa ya tsaya matsayin sa Inda Allah ya ajesa , kwana biyu sukayi suna a cikin makaranta akan BAIWAR Ilmin da Allah yayi musu abin sai Wanda yagani Teachers suka fara sonsu duk Inda kaji cikin skull zance Sajeeda da Ruky akeyi Abin yafara bawa wasu student's din haushi Dan yanxu da wuya ayi wani skull conpotiong  ba dasu  ba gasu da kyau kamar diyan laraba da yawa ss3 student, sun sha musu gargardi akan wasu malaman, abin har mmki yake baiwa su Ruky Dan su a tsarin su ba soyayya a halin yanxu Dan Daddy baya barinsu ko da wasa balantana ma a skull dayake dokar makaranta CE .


Maman Ussee๐Ÿ˜˜๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž 1⃣5⃣


Maman Ussee๐Ÿ˜˜ 


Sajeeda da Rukayya yaran kirki, wadanda bazaka taba cewa sun tsokaneka ba , zaune suke a harabar, area class, sun duba wani book, dukadai ne zaune a gurin sai wadan da. Baza,a rasa ba, Sajeeda ta kalli Rukayya, yadai Sist naga ki wani iri neyake faruwane. Murmushin karfin Hali kawai yar baiwa tayi,

Mekigani ne hln ba komai, nikuma dadina dake shegen zurfin ciki yanxu akwai abinda yake damunki a duniyar nan dabaza ki iya fada mun shi ba, koda yake ,may be kinada ,

Wata wadda ya dace kiyi sharing din fillings dinki da ita wadda ta wuce ne, nakula dake tun jiya bakya jin dadi but saboda, karfin hali irin naki nayi ta tambayar ki amma kin ki, fada ,

Namiki alwarin yau idan har baki gaya min. Ba to damunje gida nikuma sai na gayawa ,mummy ita ai dolenki, ne ki fada mata ๐Ÿ˜ณ zaro ido Rukayya tayi hadi dacewa hava Sist kin kasa fahinmta ta. Kawai ne nagaya miki am OK ,

Kawai dai na tuna da Raba ne shiyasa hmmm Rukayya yaushe kika koyi karya nidai nasan wllhi dakwai wani abin da kike boyewa kuma zan gyaleki. Baxan sake tambayar ki. Ba amma nima wata rana ko kin gani cikin damuwa to karki kuskura kice wai zaki tambayeni meke damuna, Dan ba fada miki zanyi ba ta tashi fuu da dauki sauran tarkacenta ta kara gaba, dafe kanta Rukayya tayi Dan batasan ya zatayi da fushin Sajeeda ba ,

Tana matukar son 'yar uwarta.

To amma tayaya zata iya fada mata wan nan abun ai sirrin ta ne. Bedace sai Sajeeda taji ba duk da yake tana fuskantar yan matsaloli 

Kadan amma tayi alkawarin ko mummy. Baxata fadamawa ba Dan ita kunyama takeji ace wai girma yazo mata duka duka shekarunta nawa yanxu 15 ne fa am still young ta furta a filli yayinda tayi wani Kayataccen, murmushi, ๐Ÿ˜Š bara naje nayi bikon my Sajeeda yar rigama nidai maman Ussee, gefe. Nakoma nasha ๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€ dariya ta mai isana kamin nan nace su Rukayya manyan mata girma yazo kenan๐Ÿ™Š ba,aso a fada a gida lol.

Duk abinda sukeyi akan Idon sane yakasa jure taya zai iya hakura da Rukayya da dinbin so da kaunar da yake yimata kuma da kunya yaje yasameta da sunan wai yana, sonta yarinyar karamace  batasan meye so ba but zai yita renon Soyayyar ta a cikin zuciyarsa har sai nan gaba kadan ya fada mata dama duk wani move nata akan Idinsa ne bashida wani aiki sai na kallon ta a duk fadin skull din. Baiga wata ya macce wadda zai iya , baiwa zuciyarsa ba kamar Rukayya tun farkon kasu su ,skull din yake masifar sonta duk ,da dibin yanmatan da ke zarya a gd da kuma waje shi baiga wadda tayi masa ba irin Rukayyah Ring bell din da yaji ne yadawo dashi daga Duniyar  tunaninda ya tafi Dan zuwa yayi musu lesson dama da an dawo daga break, yanada class dinsu cikin sauri ya kwashi abinda zai bukata yakara gaba .

Towai waye wan nan๐Ÿค” Bakowa bane ila uncle Faruq yaro mai ki da kansa ga kyau ga ilmi uwa uba ga kudi bayason raini ,kokadan bai cika damuwa da abinda be shafesa ba duk da iyayensa nada kudi. Bedamu da nasu ba yafi bukatar tasa dukiyar gumin kansa , mahaifinshi ,yanada kudi ba kasan. Ba Amma Faruuq basune gabansa  ,ba bayan dawowarsa daga maleshia karutu shine yanema kansa aikin koyarwa a S A M I C duk da wurare da yawa, ana Bukatar sa .

Amma shi duk bayasonsu ,yafiso. Ra,ayinsa ,

Saigashi kuma Allah ya jarabceshi da son wacce batama San yana yi ba hmmmm duniya kenan.

Rukayya Bata fice Class dinsu ba saida ta fara zuwa gurin yar uwarta Sajeeda tabata hkr dayake kunsan Sajeeda da Rukayya sai Allah nan da nan a shirya sukaci gaba da wasansu da dariya Ring din bell ne yadawo dasu Rukayya tacema Sajeeda Sist bara na wuce Dan wllhi Uncle Faruq ba mutunci ne dashi ba zai iya hanamin shiga class idan har yarigani kuma. ,baya latti yanxu haka in ance yana hanya bana musu , to sarkin tsoro fara gudu tundaga nan suka kwashe da dariya su duka Ruky ta kama Banyan zuwa Class dinsu har ta kusa kai ta tuna da book dinta yana hannu Sajeeda dazu ta ficce dashi kuma Uncle Faruq yabasu assnmnt yaune kuma ranar dubawa da gudunta ,ta koma baya sai Class dinsu Sajeeda Sist ban note Book dina na Geography, dakika dauko dazu , cikin sauri ta karba ta nufi hanyar class dinsu saidai  tayi rashin sa,a Dan kuwa har yariga yashiga ๐Ÿ˜ณ zare ido tayi hadi da Dora hannu aka๐Ÿ™† nashiga ukku yauni Rukayyatu , wan nan Uncle din mai disga mutane yaxanyi dashi ,bayan ta saita kanta kawai tayi shahada tace excuse me sir yes ya amsa batare da ya juyo ya kalli me magana ,ba duk da yasan ko wacece, am sorry nayi late wallahi na manta note book dina ne a class dinsu YAR uwata koda naje na karbo harkashigo kayi hkr plzz, baice da ita kalla ba saida yagama rubutu a white bord kamin nan ya juyu ya kalleta in serious student taya za,ayi kibar note book dinki a hannu wata inhar yanada muhimnanci a tare dake bari kiji u wll not attend my lesson kuma ki  bacce min da gani kina disturbing , dinmu hkr tashiga bashi kamar tayi kuka ,amma ko kulatama beyi ba haka ta karashi tsayuwarta takoma bakin class ta zauna, yayinda shi kuma a cikin Ransa yake cewa am sorry my Angel bansan ya zanmiki ba shiyasa namiki hakan.


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž1⃣6⃣

Maman Ussee๐Ÿ˜˜

Gefen Rukayya takoma tana duba book dinta ,yayinda uncle Faruq yaci gaba da lesson Sometimes yakan Dan , dubeta duk da dai baya ganin fuskarta ,amma yana ganinta a zaune wani ,nishadi yakeji idan har yaganta , bayan.

Yakare lesson dinsa yana fitowa cemata kawai yayi ke biyoni muje ki karbo sauran note book din yan class ,dinku kisameni a staff room ko dago kai batayi ba ,balantana ma ta bashi amsa saida ya sake maimata kiran ta ke Rukayya bakyajina double funishment, sai nasa distilling, master yakoya miki hankali ,a sanyaye, tace sorry uncle wllhi banji bane ina kara2 ne kuma ta duk ji kawai dai, yabata haushi ne yasakata zaman 30mnt a waje kuma yamata hasarar daukar lesson dinta ,gashi harda wani CE mata ke danya raina mata wayyo ,bayan ta basa hkri ne tashiga class ta hada books din yan ajin nasu guri ,ta fita bata zarce ko,ina ba ,sai staff room.

Dashigarta kai tsaye , teburinsa ,taje ta Dora books din bayan ta sake. Basa hkr baice da ita komai. Ba kawai dai yana kisima kyau da kuma sweet voice dinta hardai dayake cewa kayi Hkr uncle jiyake kamar  ya rungumeta hardai inta bude idonta masu kara tafiya da imanin sa, da kyar yasamu ya saita kansa cikin voice sarkake yace da ita u can go but karki sake maimata hanka kinjiko ta amsa da to kawai tayi ficewarta , shi kuma gogan tunanin yanda zai iya bullowa Ruky kawai yake yakasa Dan besan yazata karbi zance nasa ba.

Kai tsaye class dinsu ta nufa cike dajin haushi uncle Faruq sai wani tasata a gaba yayi yana kallon ta da wasu mayyun idonsa kawai ya hanata samun abinda tazo nema akan wani ka,ida nasa na banxa ,to na banxa mana cewar Rukayya ai nabasa hkr amma yakasa ganewa, tana shiga sai ga wasu yan SS3 student prefect sun shigo class din bayan kowacce , student ta nutsu suna wani yatsina Ku wayece dazu mukaga tabi ,uncle Faruq a cikinku Ruky ta yi shuru kowama baiyi magana ba ,Ku wai ba .

Magana ake muku bane kun maida , mutane wasu yan iska , can sai wata ta nuna  Rukayya Sisters wan Nance , kan uban chan, shine Dan rainin wayo kinaji ana magana kin yima mutane shuru to biyomu, ๐Ÿ™† Rukayya tafara magiyar rokonsu ,amma Sam suka dage saita biyo,su

Ba yanda ta iya dolenta ta bisu , sanda suka gama disgata kamin nan suka bata punishment, din wankin , toilet kai ranar Rukayyatu taga bala,i ,iri iri duk sanadiyar uncle Faruq akan wai su sonsa sukeyi kuma suna zargin Rukayya ma wai ,sonsa take basu, San ita yanxu kara dasa tsanar sama sukayi a zuciyarta ,baita takoma ,class ba sanda akaje shot break gashi dama bata jin dadin jikinta maranta ke ciyo gakuma wani azababben ciyon kai.

Sajeeda CE tashigo class din tayi mmki sosai dataga Ruky a saman decks, tanata barcin wahala Dan yau ta bautu, Shafa fuskarta Sajeeda tayi sleeping beauty kintashi muje short.Break ,tadanji jikin Ruky da zafi nan daban ,

Sajeeda ta rude Sist meya faru tafara jijjigata Ruky ta bude idonta da kyar saboda zafinda suke mata Sist bana jin dadine muje,

Ki kaini skull clinic itace ta taimaka mata har zuwa clinic din.

Bayan Norse ta dubata ,saita. Bata magani kamin ,nan bacci yadauketa Sajeeda ta kwantar da ita akan bed din clinic cike da tausayi takoma Class dinsu. 

Maman Ussee๐Ÿ˜˜

Nagode sosai my fans๐Ÿ˜Š
๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž1⃣7⃣

Maman Ussee๐Ÿ˜˜

Rukayya bata farka ba sai guraren 2:pm koda ta tashi ba,inada ke mata ciwo saidai kawai batajin kuxazari ,a jikinta hakan, dai ta kejinta fayau da ita ,uncle Faruq yasha Allah ya isa kamar me a gurin Ruky Nurse CE ta taimaka ,ta gyara jikinta kamin nan tafito a jima anjima takan yi tsaki kadan.,

Jefi jefi acinkin zuciyarta kuma cewa takeyi wllhi baxan. Taba yafewa Uncle Faruuq ba Dan duk shine silar shiga ta damuwar da nake ciki a yanxu haka kurum Dan mugunta ,yahanani shiga class gashi yau ban fahimci komai da akayi ba yamin hasarar the whole day mugu kawai bantaba jin na tsani wani mutun ba kamar kai. 

I Hate u, I hate u, I hate u ,uncle faruuq wasu hawayene suka fara wanke mata fuska kwata kwata yau ji take kamar ta kashe Faruuq Dan duk shine sanadin komai da yafaru da ita ko a gidansu bata taba irin wan nan wahalarba sai gashi yau ansaka wankin toilet shidda ita kadan ta , ga maranta dayake mata ciyo kadan kadan rumtse ido tayi ta sake budewa yasake maimaita Wllhi baxan taba yafema ba wannan cutuwar,

A bangaren faruuq kuma tun bayan tafiyar Rukayya tunanin ta kawai ya adabeshi book dinta ya dauko ya rungumeshi ki yake ,kamar ita din CE a hankali ya fara gutta I LOVE YOU SO MUCH, My Angel, ya sumbaci book din kamin nan ya hada sauran book din ya aje a cikin locker din  Decks, din sa ya dauki na Ruky ya fita dashi gabaki daya ma skull, din yabari,

Sajeeda kuwa lesson ake amma bata fahimtar komai ,duk hankalinta yana gun YAR uwarta Dan batasan a wane hali takeba Allah Sarki Sajeeda ta Rukayya ,da kyar taga karfe 2 Dan ma a hana su fita sai anyi sallar Azzahar kawai dai Sajeeda ji take kamar ta daura hannu aka ta kwala ihu Dan jitake kamar ciwon Rukayya yadawo jikinta batasan ya mummy zata dauke ta ba, idan har ta gane Ruky batada lfy gashi bata samu damar zuwa clinic ba ,haka ta hkra sai guraren 4 haka taje ta dauko Rukayya a clinic suka shiga skull bus sai gida,

Da shigarsu gida mummy ta tarbesu Dan taga Sajeeda CE ta riko Rukayya wadda ciwon ya kara tashi da kyar ma take gani dishi 2 take gani subahanallah Yaran Daddy lafiya dai meyake faruwa wani Abu aka muku ne Sajeeda ko kamar jira take mummy tayi magana saita fashe da kuka , ke lafiya meyasamu Rukayyarne, kike kuka yi shuru gayamin meyake faruwa ne, mummy Rukayya batada lfy yau gabaki  daya a clinic ta wuni  ,

Taslima mummy tashiga yi kamin nan ta dafa jikin Rukayya taji zafi rau ba bata ,lokaci tayima Daddy waya take sanar dashi halin da ake ciki ,batare da wani bata lokaci ba sai gashi.Nan yadawo ,daukar Rukayya yayi yasaka ta a mota shida mummy, suka kaita asibiti Sajeeda kuma aka barta gida ita dasu fadil da Abdallah kuka kawai takeyi Fadil ne me tambayar ta Sister meya faru da Sister Rukayyahnah naga an dauke ta cikin shashekan kuka tace batada lfy ne Fadil kuyimata addu,a Allah yabata lfy cikin gaggawa Ameen suka amsa kamin nan suka wuce dakin su kowa ba dadi a ransa ,suna taya Yar uwarsu jimami (Ya Allah kabamu Ikon so da kuma kaunar Yan uwanmu tsakani da Allah da zuciya daya) Daddy bai zarce ko,inaba sai specialist. Hospital da zuwansu bada wani bata lokaci ba aka karbi su yayinda aka shiga baiwa Rukayya taimakon gaggawa , Daddy hankalinsa a tashe sai dama kinsan Rukayya batada lfy shine kika kasa gayamin, to akan wane dalili, sorry Abban yara wllhi bansan cewa batada lfy ba kasan bayanda za,ayi na sani ban gayamaka ba kawai dai irin zurfin cikintane bata fadaba cewar mummy Daddy yanada zaune yakasa tsaye ko kadan bsyason abinda zai taba lafiyar yar mutane saboda ita amanace a gurin sa , yayi alkawarin zai kula da ita kamar yanda zai kula da 'ya'yansa da ya Haifa gashi Rukayya tasamu rashin lfy baima sani ba sai yanxu, shi duk laifin mummy yake gani Dan tafisa kusanci da su to meyasa bata fadamasa ba tun wuri sai. Bayan Abu ya zama whose

Maman Uzuwa๐Ÿ˜˜

Muje zuwa!!!


 ๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž1⃣8⃣ 

Maman Ussee๐Ÿ˜˜

Doctor ne ya fito daga room dinda aka ajeyi Rukayya , Daddy ya tarbesa cikin hanzari yadai likita ,cemasa kawai yayi ya biyosa zuwa office din sa,  batare dawani bata lokaci ba yabi bayansa mummy kuma Room dinda Rukayya take ciki  ta shiga koda tashiga ganin Rukayya tayi kwance abinta sai sharar bacci takeyi ana mata karin ruwa, 

Tausayintane ya kama , Allah sarki Baby Ruky Ashe bakida lafiya shine kikaki fada min har sanda Abu yayi tsanini ban kyau taba daban gano cewa , ur not felling too well ba but I promiss daga ,yau zan kara himma wajen kula dake banason ko kadan wani Abu yasameki Rukayya Allah yabaki lfy , ta sa hannu ta Shafa fuskarta mai haske ,

Abangaren daddy kuma bayan yashiga office din Doctor ya zauna, Doctor yamaida hankalinsa a gurin daddy Dama ba wani dogon matsala bace kawai dai tasha wahala ne matuka watakilla ko ansaka wani aiki ne mai wahala or something, like that kuma ga period, dinta yafara zuwa da ciyon Mara Wanda duk shine yakara tsanata akan yawan. Dukin da tayi tayi that why yasaka mata fever Dan jinin bai sauko, a gurin. Da yakamata ba but Insha Allah she wll soon be fine, yanxu tana bukatar Hutu nayi mata aluran bacci Insha Allah koda zata tashi ba wata damuwa kawai dai a kiyaye gaba Dan gudun faruwar irin hakan,saboda worm dinta bayada karfin. Da juriyar daukar wahala  sosai irin hakan nan, 

Ajiyar zuciya Daddy yayi kamin nan ya yima Doctor godiya yakarbi takardar magani Dan yaje yasayo,

******* ******* *******

A gida kuwa Sajeeda banda aikin kuka ba abinda takeyi su Fadil ke Rarrashinta hankalinta duk yakasa kwanciya, ganin har 6 :pm ba mummy kuma ba Daddy gashi ita. Ba wayace da ita. Ba balantana, takira taji ko lfy duk ta rude ta kasa aikata komai tunanin, a wane hali yar uwarta take a ciki kawai takeyi jitake, kamar ta dawo da ciyon yadawo kanta, tun daworsu har yanxu uniform, ne a jikinta , takasa cirewa ko Islamiya ma yau. Ba Wanda yaje a cikin su gidan yayi quit sosai, ba dadi su Abdallah ma haka suka yita bata hkr amma, takasa daina kuka shigewarsu sukayi nasu dakin kowa yayi jugum,

Mummy na zaune ita da Rukayya daketa barci daddy yashigo, da ledar magani an rubuta NATA Benji Pharmacy,

Ajewa yayi ya zauna akan kujera yafara jeroma mummy question , kinasa Rukayya aiki mai wahala ne? Meyasa baki fada min batada lfyba saida Abu yayi tsanari? Dama kinsan batada lfya Amma shine baki badaminba? Wane aikine kikasa ka Rukayya mai wahala a yau? Answer me ,

Sukuyarda kanta tayi kasa tafara bude baki Daddyn Yara wllhi bansan cewa Rukayya batada lfya ba kaima sanin kanka ne lfy lau muka rabu da ita dazu da safe ,aiki kuma ni banda shara da wanke wanke ba abinda suke min a gida yauma ba abinda sukayi da dawowarsu daga school ne fa nakiraka a waya Dan Sajeeda CE ta shigo da Rukayya ko tafiya ma bata iyayi kawai dai mujira farka warta sai mutanbayeta ko dakwai wani mai takura matane bamu sani ba,

It's OK Allah yabata lfy kinga  an kusa magrib zanje gida na duba su Sajeeda sai na taho muku da sauran kayan bukata Dan nasan maybe nan zaku kwana, badamuwa mummy ta amsa .

Da zuwansa gida car kawai ya ajeye ya fada masallaci Dan ya gabatar da sallah, bayan yakarene yashiga cikin gidan ,  bakowa a Fallon kiran sunanta yafara yi a Hankali Sajeeda, Sajeeda , naam ta amsa cikin sanyi ta fito INA k'annen naki , Daddy inaga sun tafi masallaci OK to ki kwantar da hankalinki sister dinki taji sauki sosai ki je dakin mummy dinku kidauko  , blanket da kayan ta ki hada harda na Rukayya ki dauko cups da spoon da flalet, kinji ki dauro Ruwan zafi ki saka a Flak's kamin nayi wanka kin shirya komai sai muje hospital, din Ku dubu Rukayya kinji To ta ansa kamin nan ta fara hada abinda aka umurceta tayi guri daya , Basu bar gidan ba sai bayan Isha ,saida Daddy yafara biyawa super market ,ya sayo musu kayan tea kamin nan ya biya restaurant, yayi musu take away,

Basu zarce ko INA ba sai a ,Asibiti, Daddy ya dauko sauran kaya yayinda Sajeeda dasu Abdallah suka dauko saura, Room dinda aka kwantar da Rukayya nan suka shiga sai dai har yanxu bata farkaba Sajeeda da gudu ta isa bakin gadon ta k'amk'ame ta tana Hawaye Mummy CE ta CE ke lfyarki kuwa inkinka jimata ciwo fa kin wani riketa kamar saceta za,ayi shikuma Daddy tausayinsu yagani kasancewar yasan yanda suka shaku da junansu , 

Cikin bacci Rukayya taji kamar an riketa bude ido tafarayi tana gani bishi bishi kamin idonta suka bude fabaki daya, ta kalli Sajeeda Sist meya faru dani Inane nan, Daddy ne ya dafa kanta sorry Babynah nan Asibitine bakyada lfya ne shine muka kawo ki hpe dai bawata damuwa ko eah ta amsa yayinda tashiga tunanin abinda Yafaru da ita dazu  tsaki taja a cikin zuciyar ta sake cewa mugu kawai saida yayi sanadin kwanciyata asibiti Allah ya isana mummy CE ta taimaka mata tashiga toilet ta gyara kanta duk kunya ta isheta  bayan ta canja kaya mummy ta hada mata tea mai kauri ta mika mata tasha sai Sajeeda ta dauko Take away tafara bata a baki tanaci kadan kadan  tanajin dadin kasancewa tare da family dinta Dan soyayyar da suke nuna mata shiyasa a kullun sai tayi musu addu,ar gamawa da duniya Lafeeya.


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž1⃣9⃣

Maman Ussee


Sajeeda saida ta fahimci Rukayya tashi dayawa San nan ta daina bata abinci sun Dan taba fira , anata wasa da dariya Daddy ya kalli Rukayya, yadai baby tazu aikin meye kikayi mai wahala ne a gida ko a skull, Dam taji gabanta yafadi runtse ido tayi ta tuno da irin azabar da tasha a gurin su Sister Jameela Budurwar uncle Faruuq, sake bude ido tayi nanda nan mood dinta ya canja, gabaki daya fara,ar ta.

Ta dauke murmushin karfin hali tayi sannan tace bakomai Daddy bayaso ya takura ta duk da ya fahimci dakwai wani Abu amma bayaso yayi forcing, dinta dole saita fada basar da zancen akayi aka dauko wani zancen na daban,

 Basubar asibitin  ba sai guraren 10:30pm ya dauki su Sajeeda da Abdallah da Fadil zuwa gida yayinda aka bar mummy ta kwana da Rukayya kamin gobe su nemi sallama, Sajeeda ma  ba,ason ranta ta tafi ba Dan dai Daddy yace gobe dakwai zuwa skull kuma bai dace Dan Rukayya batada lfy Sajeeda taki zuwa makaranta ba dolene ita taje ,

Bayan sun tafi. Mummy ta dubi yarta tafara yimata nasihohi Dan ta kula da kanta, da abubuwan da duk suka dace uwa ta fadawa yarta wasu Rukayya saidai ta sunkuyar da kanta kasa Dan kunya takeji mummy sai dai tayi murmurshi , Dan tasan Insha Allah irin tarbiyar da suka baiwa yaran su da wuya su fandare inba wani ikon Allah ba kuma tana musu fatan samun kariya da duk wani sharin mai Sharri,

Kashe gari tun safe Sajeeda ta tashi tashirya cikin uniform dinta, tanata jin wani iri Dan ta Riga yasa ba da komai a tare sukeyi da yar uwarta Rukayya sabanin yau da ita kadai takeyin komai sabo kenan turken wawa. Bayan Daddy ya ajiyesu a skull saida yabiya office din principal yayi report, cewa Rukayya batada lfy sai dai next week zata fara shigo wa insha Allah da yake ranar laraba ne abin yafaru gashi kuma yau alhamis da yau da gobe baxata shiga ba Dan assabar da lahadi week end ne sai dai on monday , principal din yace it's OK badamuwa Allah yabata lfy sai dai on Monday din nan tashigo saboda sun fara texts kar tayi missing Dan nasan yar wajenka she's very hard working student Daddy yaji dadi sosai ya basa hannu sukayi misabaha kamin nan ya fice daga skull din, zuwa Hospital Dan ya dubo ya jikin na Rukayyatu.

A asibiti kuwa bayan Doctor ya duba ta da safe. Ba wata matsala sai ya rubuta musu sallama kuma ya umurci data sha maganin ta abisa ka,ida kuma cikin lokaci, Daddy kawai dama suke jira yazo su wuce da isuwarsa daukansu kawai yayi bayan yayima Rukayya ya jiki ya kwashesu sai gida daga nan kuma ya ficewarsa zuwa gurin aikinsa,

Faruuq ne yafito daga cikin motarsa kiran Mercedes sanye da Riga da wando na jeans wandon. Baki Riga kuma fara anyi mata rubuta da bakaken harufa an rubuta it's my Time bai zarce ko,inaba sai admin block yaje yayi sing kamin nan ya wuce staff office ya dauki abinda zai dauka ya nufi class dinda yakeda lesson wato A class SS one A ajin su Rukayya a zuciyarsa muradin ganinta kawai yakeyi Dan tun jiya yakejin faduwar gaba gani yake kamar wani Abu yafaru da ita bayan sun rabu jiya dashigarsa, bayan student sun gama gaidasa Sit dinda take zama ya kalla amma ga mmkin sa ba tanan  sake ,daga Kansa yayi ya kalli wurin bayaso ya tambayi yan class dinsu Dan kar suyi suspecting din wani Abu ,haka dai ya daure ya fara lesson din zuciyarsa sai zafi take baiga Angel dinsa ba, wata dubara CE ta fado masa arai dayake jiya books din su, yana hannu sa shine yayi amfani da wan nan damar ya aiki class captain Dan taje staff room ta dauko books din tanan zai San in angel dinsa na nan ko bata nan bayan ta kawo yafara mark yana kiran suna Dan mai littafi yazo yakarbi kayansa , da haka har yakai ga nata yakira name dinta Rukayya Sa,eed  shuru ba Wanda ya karba ,saida ya maimata har sau 2 .

Kamin nan yan class dinsu ka CE uncle yau batazoba ,what? Yafada adan razane sai dai a hankali yayi kokarin saita kansa kamin. Nan yace saboda meye batazoba yau muma bamu sani ba suka. Bashi amsa daga baya sukace akwai dai sister dinta a C class sai in ita za,a tambaya cewa kawai yayi suje su kirata member dayace cikin yan Class din taje block dinsu Sajeeda danyin kiranta bayan tazo, uncle Faruuq yakalleta ke INA sister dinki meya hanata zuwa skull yau , uncle batada lafeeya kuma whorse Dan yanxu haka tana asibiti ,Dam Dam Dam yaji gabansa ya fara duka acikin ransa cewa yake to meke damun my angle yazama wajibi naje naganta to amma ta yaya zanje? A wane matsayin? Ganin zai batawa kansa lokacine yasa ya. Baiwa sajeeda book din Rukayya tare dayi mata fatan samun sauki ya tambayi Sajeeda a wane asibiti ne aka kaita specialist kawai tabasa amsa ta juya zuwa class dinsu Dan daukar lesson dinta.


Maman Ussee๐Ÿ˜˜ 


Naga sakonku my fans INA godiya sosai da kulawarku๐Ÿ‘


๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž2⃣0⃣

Maman Ussee๐Ÿ˜˜


A gurguje ya kammala duk wani abinda yakeyi yaje yadauki excuse, bai zame a ko,inaba sai a specialist hospital, room by room yayita shiga amma komai alamarta baiganiba kamar ya daura hannu aka yayi ihu meyasamu Angel ya akayi bansaniba anya zan iya jure rashin ganinta kodai naje na tambayi sister dinta gidansu, ohh no baxan iyaba banaso ,ta fahimci wani Abu a halin yanxu she's still young, batasan meye so ba shikadai yaketa sambatunsa , jiyake zuciyarsa kamar zata faso kirjinsa ta fito in bai samu Rukayya ba ohh wai meyake faruwa dani ne young girl tanata wahalad dani abanxa batama San  inayiba, 

 car dinshi ya shiga ya tadata ya bata wuta sosai sai gida haka shima yakejin kansa kamar bashida lfy har mamakin Kansa yakeyi ,wai yarinyarda bata wuce 15 ba take rudashi ,haka yaga mata kala2 amma baitabajin wani fillings akansu. Ba sai ita, ita din daice a cikin zuciyarsa!! A katon Falon gidansu ya zube. Dafe da kansa , ya Dade yana zaune a gurin yanata tunanin ,yanda zai bullo wa lamarin Dafa shi yaji anyi, a hankali ya dago Kansa yayansa yagani yadai Umar lafiya kake kuwa naga kayi zurfi inata sallama bakajiba, Haka dai naganshi kwanan nan bai cika son surutu ba dama shi bai faye magana. Ba amma kwanan, nan abin yayi whorse cewar Hajiyarsu dago Kansu sukayi a tare suka gaida mahaifiyar tasu , cikin girmamawa, cike da kulawa ta amsa ,dama idan  kaga fara,ar ta to tana tare da ya'yan tane .

Hajiya Kubrah kenan manyan mata Abubakar ya dubi mahaifiyar sa mum wai yaushe ne su Aleeyu zasu dawo ne sunfa karasa exams dinsu jiyama nayi waya da Usman ba abinda ya tsayar dasu kawai dai shiriritace irin tasu,  Hajiya kubrah ta nisa oho sai sun gama hutawa inga zaman London yana musu dadine shiyasa, Amma duk ranarda Alhaji yaganosu kashin su yabushe cewar Abubakar kawai Dan dan sun maida ba a, bakin komai. Ba sun kare exams shine suke tayiwa Abba karya yana tura musu kudi bayan sunsan sun kare Dan kawai rashin kishin kai, kai dakata ra,ayinsune saboda haka ka kyalesu sai ranarda sukaga dama su dawo Kai takura maka akayi dakake karatun, wayene ya matsamaka, baice komaiba dai shi a duniya yana mamakin hali irin na Hajiyarsu kwata2 bata son a takura wa ya'yanta kawai Dan suna da gata Allah dai ya kyauta, 

To Mum su Afra fa sai yaushe, kaga Malan banason sa,ido towai Ina ruwanka ne kai kake biyan kudin makarantar ne ko ta aljihunka ake biyan kudin meye naka a ciki ,kabarsu suyi abinda sukeso lokacinsune, Umar Faruuq da yaga surutun nasu kara chaja masa kai kawai zasuyi fita yayi daga falon yanufi sashensu Dan Inda sabo yasa ba dajin irin wan nan dramer din ,tsakanin  Hajiya da Abubakar, kawai dai shi Abubakar, din ne da na cewa kullun saiyama Hajiya maganar dawowar, k'annensa Nigeria amma amsa dayace take bashi ,shibazai iya hkra yasa masu ido bane, gani yayi idan yabiyewa Hajiya da Abubakar sai sun kara karamishi wani sabon al,amarin gara yabar musu gurin,

Dakinsa ya nufa kan bed dinsa ya zube zuciyarsa sai bugawa take runtse idonshi yayi yasake budewa ahankali ya furta I LOVE YOU RUKAYYAH.


Sajeeda kuwa yinin ranar a takure tayi shi  badadi tasaba komai tare sukeyi ita da sister dinta gashi yau komai ita daya takeyi har break ma kasa yinsa tayi a dadafe taga time din tashi daga skull din yayi koshi , jitake kamar tayi,fira taje gida ta shirya ta tafi asibiti dan ganin Rukayya, Dan batama San an salami Rukayyar  ba, haka takeji kamar ma ta wuce asibitin direct.

A yauma skull bus dinsu gani take kamar ba tafiya suke yiba Dan bata ganin saurin tafiyar ,yau Sajeeda kenan aminiyar Rukayya,

San da mai bus ya ajeyeta da sauri ta fada cikin gidan amma ga mamakinta taga komai tsaf an gyara ko,ina kamshi tashi kawai takeyi ga kamshin girkin mummynsu, bakowa a falon Room dinsu ta shiga ,Ga mmkin ta sai ganin Rukayya tayi akan  bed tanata barci abinta hankali kwanace ,wani murmushi Sajeeda tayi najin dadi mai kayartarwa da sauri ta isa , bakin gadon ta Shafa fuskar Rukayya sister ya jikinki hope kinji sauki Dana Rukayya ba. Bacci takeba jin bude kofane yasaka ta kulle ido,  bude idonta tayi a hankali ta Dora kanta a saman jikinki sajeeda naji sauki sosai sister I miss u so much me too ,sukayi murmushin jin dadi kamin nan sajeeda ta cire uniform dinta ta fada bathroom domin yin wanka.


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


 ๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž2⃣1⃣ 


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


Sajeeda ta fito da ga wanka ta shirya cikin dugowar Riga ta Atamfa simple dinki , dama ita bata Faye yin make up ba inkaga mai Make, up to Rukayyace, 

Sallar La,asar ta farayi kamin nan ta zauna ita da Rukayya tana gaya mata abubuwan da suka faru yau a skull, ohh kinga har na manta ga book dinki da , aka bani dazu uncle Faruuq ,mtseww Rukayya taja tsaki Sist bar fada min sunansa mugu kawai ๐Ÿ˜ณ cike da mamaki sajeeda ta kalleta wani abune yayi miki hln ,Rukayyah , sai a sannan ne ta tuno da katobarar da tayi but bayanda zatayi dolene ta fadama ,sajeeda gaskya koba komai baxata iya yimata Hidden din komaiba,

Nan ne ta sanar da ita duk abinda yafaru . Sajeeda ta dafata kinga kiyi hkr ba shine sanadin shigarki damuwa ba dama dai can su Sister Jameela suna jin haushinki kawai ki rabu dasu Allah yana gani ki rage tsanar da kikayi masa wllhi baki ga yanda yadamu dazu ba danace bakida lfy har tambayana ma yayi a wane hospital, aka kwantar dake nagayamai kinsan kuma ba kyau ka tsani Dan uwanka musulmi Rukayya nasanki da saurin yafewa kiyafe masa kimaida komai ba komai ba zai wuce kinji my Sister,

To kawai ta CE amma ga alama maganar bata shiga cikin rantaba tadai basarne Dan bataso Sajeeda ta fahimci wani Abu a cikin zuciyarta ko cewa takeyi hava Dan bakisan azabarda nasha bane shi,isa kikace hakan.

Suna zaune a dakin sun dauko sabuwar fira mummy tashigo dakin ta kalli 'ya'yan nata cike da sha,awa  tana matukar so tagansu cikin farin ciki da annashuwa, yadai yaran Daddy ana tadine, Rukayya kinsha maganin ki eah tasha mummy yanzun nama ta kare sha ai zan kula da komai insha Allah yauwa yar albarka Allah yayi muku Albarka a tare suka amsa da Ameen. 


Faruuq kam Sam zaman dakin ya gunduresa jiyake  inama ace yasan gidansu Angle da yaje yanxu kozata wulakantashi Amma kuma tayaya shida ba yawo yake cikin garin sosai ba balantana ma ya iya sanin unguwarsu harta, kai ga sanin gidansu Ohh Allah gani gareka , ka sassauta min wani kuna yakeji a cikin zuciyarsa haka ya wuni ba walwalla a tare dashi da kyar yaga marece yayi ya Dan samu yayi wanka yasaka kayan sa Dan yazaga gari ko zai rage zafin ra dadin da yakeji a cikin ransa Dan ya fahimci zamansa shikadai ba karamin kara, dagula masa lisafi yakeyiba. Unguwar  mabeera ya nufa gidansu wani friend dinsa yana cikin tukin mota phone dinsa, ya hau ring, kamar karya daga danshi a halin yanxu ba kowane surutu yake iya saurareba indai bana Angel dinsa bane, baima tsaya duba mai kiran ba receive kawai ya lasha ya kara wayar a kunne Hello!!! Daga dayan bangaren aka amsa Hello sweety ykk koba,a fadaba yasan ko wacece Salma kiyi hkr ina driving, ne yanxu zan kiraki anjima.

Baima jira cewar ta ba ya katse wayar tare da jinjina hali irin na Salma kullun. Saita kirasa ta wani mayance masa ko anaso dolene oho.

Wacece Salma? Salma  Kabeer 'yace ga Alhaji kabeeru Mainasara , aminin Alhaji Bashirne mahaifiyar Salma kawar Hajiya kubara CE ta sosai Dan kusan halin su ne yazo daya, shiyasa amintar tasu tahadu saidai ita mahaifiyar Salma tsayayyar mace CE duk abinda tasa agaba to ba shakka saita mallakeshi  su hudune a gurin mijin amma saboda kissa da tuggu irin na Hajiya Suwaiba saida tasaka duk aka kori kishiyoyinta yazama ita kadaice a gurin mijin sai abinda tace ta saye shi tamayar da Alhaji kabeeru mijin Hajiya.

Su shiddane a gidansu Abdullgafar sai Abdullwahab Da Abdulrahman Sai kuma Salma Da kanwarta Safeeya Salma cikakkiyar yar bariki CE sosai, ta goge sosai da duniya ta hadu da Faruq ne a ranarda sukaje gidansu ita da hajiyarta tun daga ranar da yafara ganinshi taji a duniya batada Wanda takeso sama dashi , duk da tanada nanema duk bata saurarensu tun sanda ta hadu da faruuq da kanta tayi masa talar kanta, butshi ko kallo ma bata isheshiba, Dan shi ya tsani macce marar kamun kawai Wanda Salma na ciki kawai dai yana kulatane sanadiyar Hajiyarsa Dan ya taba yiwa salmar walakanci a gaban Hajiyar ta nuna masa baccin ranta kuma ta umurceshi da karta kuma ganin ya yima Salma walankanci saboda hakan ne yake Dan kulata but har yanxu itace take kiransa da kuma yawan zuwa gidansu acewar ta zo gaida Hajiyar ne kuma ita dama Dan taga Faruuq take zuwa gidan.

Faruuq yaja tsaki dama nasan Salmace wllhi baxan daukaba Dan yau najawo kaina kira kenan ba adadi kashe ma wayar zanyi Dan na huta dai2 nan yayi packing a kofar gidansu misbahu abokinsa .wayar ya dauko yakira Misbahun bai wani dadeba ya fito ya shiga motar Faruuq din, suka fice daga unguwar.


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž2⃣2⃣


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


Shigiwar Daddyce ta saka su fitowa domin su gaidasa, ahh lallai Rukayya jiki yayi sauki kina daishan magani ko eah Daddy inasha sosaima to masha Allah,haka aso after sallar Isha kowa ya hallara a falo domin cin abincin dare kamar yanda suka saba ,mummy CE tayi saving dinsu, bayan kowa yaci ya koshi Alhmdllh, suka dawo falo domin yin kallon labarai Wanda kusan ma ince kullun akidar gdn ne kamin time din bacci yayi, saida kowa yara jin bacci San ,nan da guda2 yaran kowa yabar falon mummy kawai aka bari da Daddy ko suma dama jiran yaran kawai sukeyi suma suka kashe duk kayan kallon suka tafi dakunansu domin yin bacci, 

Sajeeda ta Riga Rukayya tashi daga bacci dayake tasan dawan garin bata tsaya tayar da itaba alwala kawai ta fada toilet ta dauro ta bayar da farali ta dauko qur,ani ta fara karatu cikin muryarta mai dadin saurare Daddy ne ya kwankwasa kofar dakin Amma jin ana karatu ya tabbatar masa da sun tashi daga bacci shima dawowarsa kenan daga masallaci, kira,ar karatun sajeeda ne yatayar da Rukayya da yake a bayyane take karatun addu,ar tashi daga bacci ta fara yi kamin nan tayi mika ta sauko da kafafunta kasa ta nufi bathroom domin yin wanka ta gyara kanta, fitowarta daga wanka daure da towel a jikinta dayan towel din kuma tana tsantsane kanta , dago kai Sajeeda tayi manya masu gari antashi daga bacci eah Sist shine baki tayardani ba to ayi hkr ya jikin naki Rukayya ta kalleta cike da murmushi naji sauki sosai kiyi sauri ki shirya karki makara  Allah yabada ladan karatu.

Shaf sajeeda ta manta da wai yau ana zuwa skull Dan ganin yar uwarta bata shirya ba a gurguje ta shiga wanka ta fito tafara saka uniform dinta ta dauko sock da sandals dinta yasaka Rukayyace ta daukar mata skull back har suka fito zuwa dakin mummy suka gaidata kamin nan sukaje dakin Daddy shima shirin yakeyi Dan ya ajiyesu ya wuce gurin aiki GT Bank, yadai Rukayyah ya jikin naki Naji saiki sosai Daddy to Allah ya kara sauki suka amsa atare itada Sajeeda, har cikin mota Rukayya ta rakasu Fadil ne agaba Sajeeda da Abdallah kuma a baya ta daga musu hannu har suka bar unguwarsu zuwa skull su Abdallah Daddy yafara saukewa kamin nan ya nufi hanyar skull din su Sajeeda itama ya sauketa direct assembly ground ta nufa bayan gabatarda jawabai aka sallama student kowa yakama Hanyar zuwa class dinsa.


A bangaren Faruuq kuma kasa bacci yayi da dare har wani. Zazzabi2 yakeji yana rufeshi  da kyar ya iya tashi yasha magani zuciyarsa sai zafi da kunci take masa yakasa controlin din Kansa ,jiyake kamar zuciyarsa Faso kirjinsa zatayi ta fito in bai samu Rukayya ba ,washe garima sanda ya makara tashi Abubakar ne yaji shuru baiga fitowarsa ba ya shiga knocking din door din Umar can cikin bacci yaji ana kwankwasa kofar dakinsa bude idonsa yayi ya kalli agogon dake manne abangon dakin nasa what? Yadan zaro ๐Ÿ˜ณ Ashe har gari ya wayema shut yau na rasa jam,i saboda ke my Angel I love you ya furta a gurguje ya fada toilet ya dauro Alwala ya. Bayar da farali kamin nan ya shiga wanka yana fitowa mai yafara shafawa bayan ya taje Kansa da cum saida ya shirya tsaf cikin shada brown color yasaka hularsa car key dinsa yadauka da Jakarsa ya fito a waje suka Hadu da Abubakar suka gaisa, kamin nan yashiga cikin gida domin ya gaida Hajiyarsa ,Yar mulkin tana zaune a falo da ita. Bacci safe ba akidarta bane bayan ya gaisa da mahaifiyar sa kai tsaye sashen Abbansu yaje yana zaune shima yana karatun alkur,ani sanye da jallabiya ya rusunah ya gaida mahaifinsa , Cike da nuna kulawa Abban Nasa ya karba tare da tambayar Dan nasa ko dakwai wata matsalane no Abba ba komai murmushi Alhaji Basheer yasanya ma dansa Albarka da fatan alkhairi a zuciyarsa kuma yana matukar son Umar Faruuq saboda halayenda na kirki rashin son abin duniya duk da akwai shi a gidansu amma shi kwata2 ba wan nan ne gabansaba, Bayan yagama gaida iyayensa kai tsaye car pack ya nufa yashiga motarsa Dan zuwa skull da kuma fatan ganin sweet Angel RUKAYYAH tasa.


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž ' YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž2⃣3⃣


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


Da shigar ,Skull din tarkashensa kawai ya kwasa sai class dinsu yauma kamar kullun. Batanan ,  sai dai ya kuduri niyar ko tayaya. Ne sai ya ganta Dan bazai iya jure rashin ganin taba fita yayi daga class din Dan dama lesson yazo yiba yadai zo ne yagani kotazo,

Bayan break Sajeeda ta fito ta zauna a in da suke zama itada Rukayya daga cikin staff room yana ,hangota sai yayi kamar yasa a kira masa ita kuma sai ya fasa haka ta karashi zaman gurin ta tashi ta koma class ,Dan dama ba dadin zaman ita kadai takeyi ba, 

After skull hours uncle faruuq bibiyar skull. Bus din su yayi har aka aje sajeeda daga nesa yana hangota ,abin ya bashi mmki matuka gidan Uncle Sadeeq ya furta a bayyanane, dama my angel gidan nan take ,ban saniba , kodai gdnsu kawartane to ai yar uwar tata jiya cemin tayi sister dinta batada lfya it means cewa a gidansu daya najene ko kuma na tsaya, wadan nan sune tambayoyinda yayita yiwa Kansa baisamu mafita ba gashi He can go without seeing her, ya Dade a tsaye a gurin da yayi park daga bisani ya yanke disition zai je gidan bayan sallar jumma,a dayake yau Friday ne,

Sajeeda yauma kamar kullun tashiga gdnsu da sallamar ta ba kowa a falo direct room dinsu tashiga Rukayya. Na zaune tana linke kayansu, Sist sannu da dawowa yauwa kema  sannu da gida ya jikin hope kinji sauki ,aikuwa gashinan kin gani cewar Rukayya murmushi Sajeeda tayi kamin nan ta shiga cire uniform dinta , mummy CE ta leko dakin nasu yadai Ruky ina sajeeda tashiga wanka yanxu OK to kuyi sauri Dan yau fita zamuyi daku unguwa inaso Ku rakani in an taso sallah , Ku shirya kamin time din yayi , Dama Rukayya zaman  gdn ya gundureta Neman wurin fita kawai takeyi ga dama ta samu da ga nan take yiwa Sajeeda magana cewa mummy tace suyi sauri Dan unguwa zasuje basu wani. Bata lokaci ba Dan sunmafi mummy d'okin zuwa unguwar , after masallaci suka fito daga gidan sunsha kyau kam daga su har mummyn tasu rigar shadda CE a jikinsu dinki gown ne ya dibesu sai mayafi dasu kayi rolling dashi mummy kuma less ne a jikinta ta saka babban mayafi da jika, a daidaita suka tare suka shiga bayan sun fada masa Inda zaya kaisu.

Faruuq kuma da isarsa gida wanka ya fada bayan ya fito wasu kayan yasaka shadda fara Sol  dinkin ta zarce ya amsheshi sosai ya saka hula da agogo turare sa ya dauko ya fesa Magic Dream bayan ya fito daga side dinsa cikin gdnsu ya nufa cike da fara,a yau yasamu solution din matsalarsa, sai dai mi yana shiga cikin gidan Salma ya hango a kan daya daga cikin kujerun falon ta wani hakimce tana taunar cwiengum kan nan nata ba dankwali yasha Karin gashi wasu matsiyata kanya ne a jikinta ko sheda da kyar take iya yinta a zuciyar Umar cewa yake mtseww sai ita gani take ta hadu macce ba kamun kai awa diyar arna jiwani zama datayi don Allah a hankalin yayi sallama Wanda in ba kwantar da hankalinka kayiba bazakaji meyake cewaba Salma ta dago a hankali suka hada ido tayi saurin kashe masa ido daya wow ta fada kayi kyau sosai Faruuq baima bi ta kantaba ya ficewarsa sama ya gaida Hajiyarsa kamin nan ya cemata zaije masallaci. Umar ta kira sunansa idan kadawo I have something to talk about with u so don't be let Tau kawai ya amsa ya fara saukowa daga saman,

Yana tafiya a hankula kawai ji yayi an rungumeshi ta gabansa  .

Saurin fincike ta yayi kamin nan yashiga koramata jawabai ke bakida hankali ne meye hka zaki wani rikeni keba musulma bace hln to bara kiji as from today don't u ever try to do such a thing angain mtseee yaja tsaki ya dingijeta yayi ficewarsa murmushi tayi don't mind Faruuq u will soon be mine and only mine, ta haura sama zuwa dakin Hajiyarsu Umar din.


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž2⃣4⃣


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


Da fitarsa. Bai zarce ko,inaba sai mosques bayan an idar da sallah yadade yana addu,a Allah yabashi Rukayya yasaka ita alkhairice a tare dashi bayan ya tofa cike da kwarin gwaiwa ya nufi car dinshi bayan ya tayar da ita bai zarce ko,inaba sai unguwar Arkilla sai dai cikin rashin sa,a gidan a kulle yagashi shin kodai mistake din gida nayi dazu ko kuma idanunane suka hango min gidan da. Bashi bane ohh God wai neyake faruwa dani ne ji yake kamar ya fasa ihu yadade a nan inguwar bansamu wata mafita ba kamar yayi kuka dauriya kawai yakeyi shikadai yasan irin azabar ra dadin da zuciyarsa kemasa ji yake idan bai samu Rukayya ba yana gab da kamuwa da ciwon zuciya ohh love luck what u made me do, jiki a sanyaye ya shiga gidansu kwata2 yama manta da maganar Hajiyarsa , direct room dinsa ya shiga bai wani jimaba phone dinshi yafara ring ya dauka sunan mum. Dinshi yagani daga wayar yayi tare da Sallama daga dayan bangaren tace ya banganka ba koka mantane ohh sorry Hajiya nashigo kainane yake min ciwo  but ganin tafe ta katse wayar, a kasalce ya tashi yafito zuwa jin kiran mahaifiyar tasa  ba kowa a Falon  stairs yafara takawa a hankula kamar kazar da kwai yafashe a ciki da sallamar sa yashiga room dinta saman kapet ya tarad da ita tana cin fruit. Ba kowa a dakin sai ita dayanta air condition aiki kawai yakeyi, Hmmmm Hajiya kubrah kenan manyan matan duniya gaidata yayi cike da kulawa ta amsa shuru yadan gifta na minti 5 kamin nan ta gyara zama ta maida hankalinta a gurin danta Umar faruuq.

Sunan sa ta fara kira ya karba ,dama ba komai ne yasaka nayi kiranka ba saidan in shaida maka sakon mahaifinku hakkine a wuyanmu mu fada muku alhamdullah Dan uwanka na yi masa magana yabani confidence sosai kai nakeso naji ta bakin ka aure mahaifinku yakeso kuyi Dan Ku ba yara bane and lokaci daya za,ayi bikinka kaida Abubakar nakirashi yafada min dakwai wadda yakeso to sauran kai inkanada wata wadda kukayi alkawarin aure da ita to saika fada Dan aje anema maka aurenta in kuma babu ni inada zabina saboda haka kai nake saurare,

Umar da tunda Hajiya kubra ta fara magana yayi mutuwar tsaye duk da sanyin dakin zufa dai ke karyo masa yama rasa bakin magana tayama za ayi masa maganar aure yanxu bayan wadda yakeso ko sani ma batayiba forget about bata saniba inma tasani iyayenta zasuyi mata aurene yanxu ss one fa take what did she know about aure kai impossible ,iyayenta ko saurarensa ma ba zasuyi ba then what is d solution now , muryar Hajiya CE ta katsesa look Umar mu iyayenka bazamu hango maka abinda zai cutar dakaiba na baka. Nan da kwana biyu ka kawo min matar da zaka aura ko yar waye inbakada ni inada wadda zan gadaku aure tare Salma na fahimci tana tsananin kaunarka Kaine dai kake yi mata wulakanci ,Dan haka na yanke hukunci matsawar baka kawomin surukata ba to ka shirya tarbar Salma a matsayin. Bride dinka ,what? Salma fa kikace Hajiya yes ita Salmar dai dakasani meye bata dashi ba mace bace ko kafitane so go an think before na sake kiranka , Faruuq ya mike idonsa sunyi jajir kamar gauta zuciyarsa kamar ta Faso kirjinsa ta fito yama rasa mezaice da kyar yakai Kansa room dinsa har wani jiri yake gani hava yaza amasa haka bayan yanxu ne yake so yafara  budewa Kansa sabuwar Rayuwa shida angel dinsa kamin wani lokaci zazzabi mai zafi ya rufeshi shi da kyar ya iya kiran abokinsa Dr. Khamal Dan ya Duba sa wan nan kenan.

 A bangaren su Rukayya kuwa tun da suka fita unguwa basu dawo ba sai bayan la,asar sunsha yawo kam Dan sunga gari sosai har kasuwa saida suka shiga mummy tayi sayayyar kayanda take bukata daga nan suka dungumo cikin Adaidata sai gida A falo suka zube Dan dayake daddy yadawo suka gaidasa ohhh shine kuka fita harda patient din idan kuka kwaso mata rana fa gashi yau anyi rana, lah daddy ai taji sauki sosai cewar Sajeeda kedai kunason yawo daine ba wani sauki karfin hali dai gabaki dayansu sukayi dariya Rukayya tace Allah Daddynmu nasamu sauki sosai tau Baby Allah yakaro sauki yabaki lfy mai amfani aka amsa gabaki daya da amin after  All Daddy tace sai Ku huta muyi shirin zuwa cikin gari again da murna sukace a shirye muke ai ohhh kajisu sarakan son yawo to da boys dina kawai zani ko my boys suka CE yes Daddy bazamu dasuba tunda mummy da Girls ta fita dazu muma da Daddy zamu fita yanxu ,mummy tace jealousy kukeyi to nima ai sai mun sake fita dasu watarana Daddy ya kashe mata ido daya  basai na bari ba murmushi tayi zama ka bari ai duk Kansu kowa dariya yakeyi cike da so da kaunar yan uwansu  bayan magrib daddy ya daukeso zuwa yawon shakatawa Dan dama already duk Friday sai sun zaga gari Dan su Debe kewa sunkan sha garin Dan suyi yawo sosai basu suka dawo ba sai 10 :pm kowa da sayayyarsa a hannu dashigarsu gida kowa room dinsa ya fice bayan sun yi sallar insha suka watsa ruwa sai bacci dayake sunci sun koshi asuba tagari Sajeeda& Rukayya 'yan biyu. Mummy da Daddy


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


I REALY THANKS FOR UR CARE MY FANS LUV U ALL๐Ÿ˜


๐Ÿ™Ž YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž 2⃣5⃣


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


Washe gari tun da safe su Rukayya suka tashi bayan sun idar da Sallah suka fara gyare gyaren gida koda mummy ta fito har sun kammala da komai dayake yanxu tana barin su su Dora breakfast danshi ba wuya kegareshiba suyan arrish daine sai Dora ruwan zafi sun saka komai a mu halin da ya dace suka koma room dinsu Dan suyi wanka bayan sun gaida mummy da kuma Daddynsu, fitowa sukayi da shirin zuwa islamiya kai tsaye dining area suka nufa basu wani bata lokaci ba suka kammala cin abinci kai tsaye suka fice dakin mummy sallama sukai mata suka fice zuwa islamiya.


A bangaren Umar faruuq kam abin yayi worst sosai Dan da kyar ya iya tashi yayi sallar magrib da isha wani zazzafan zazzabi ne ya keji duk da anyi treatment dinsa Amma ji yake kamar  baisha komai ba bacci kam a ranar sai dai barawo har abinci kasa cinsa yayi washe gari haka ya tashi jiki ba kwari yadanji sauki dai irin nasa Dan har sallar asuba yaje bayanda gari ya waye yaje cikin gidansu gaida Hajiyarsa ba laifi ta amsa masa batare da wata damuwa ba kana ta CE INA fatar kana nan kana yanke disition din da ya dace dakai ko eah kawai ya bata amsa gud haka yanada kyau breakfast dinma bai wani ci abincin kirkiba yadan tsakura kadan yatashi ficewa yayi daga gidan Dan kwata2 baya jin dadin zama gidan garinma ya isheshi yakusa barin garin gaba dayama ya huta haka ya wuni a ranar ba dadi dayan bangaren zuciyarsa yana mararin ganin RUKAYYAH ga kuma Hajiya ta taso shi gaba.

Rukayyah da sajeeda. Basu dawo daga makaranta ba sai 12:pm da zuwansu falo suka zube suna hutawa  mummy ta fito daga room dinta sannu da gida mummy yauwa yaran Daddy kuna lfy a makarantar to Alhmdllh suka amsa mata to masha Allah haka akeso  bayan sun gama hutawa sukaje dakinsu suka ajiye kayan su  sukan Dan kwanta su wuta kamin time din sallah yayi basu farka ba sai 2:pm koshima mummy CE ta tayar dasu Dan karfe ukku zasu koma Islamiya bayan sun idar da sallah abinci sukaci suka sake ficewa zuwa islamiya Dan daukar karatun marece sai 6:pm suka dawo gida a gajiye  basu wani dadeba magrib tayi suka fice zuwa dakinsu Dan gabatarda sallah.

Haka Rayuwarsu ta kasance har weekend ya kare Monday morning ko waccensu ta shirya tsaf cikin uniform dinta suka dauki skull bags dinsu zuwa makaranta Dakin mummy suka shiga sukayi mata bye bye daddy ya dauke su zuwa skull dasu da su Abdallah da Fadil bayan ya ajiyesu ya ficewarsa zuwa gurin aikinsa bayan an kare Assembly kowace student ta nufi class dinsu do daukar darasi dayake ma text za,a fara musu yau Dan sun kusa fara exams yauma kamar kullun zaune yake cikin staff office ya rasa abinda ke masa dadi abubuwa duk sun cakude masa kwata kwatama ya manta yau yanada Class dinsu Rukayya  before break yayi zurfi cikin tunani sai jin murya wata student yayi uncle muna da kaifa yanxu munta  jira munji shiru shine mukazo muyi biko dago Kansa yayi OK Fateema ganin zuwa kice su shirya yau text zan muku kinji ta amsa da to yabata sauran kayansa ya CE ta fice masa dasu kamin yazo.


Bai wani bata lokaci ba yabi bayanta Rukayya na zaune a sit dinta hankalinta kwance fuskarta daka ganta. Ba wata damuwa a tartare da ita  da shigarsa class din ita ya fara tozali da ita  baisan lokacin da ya saki wani Kayataccen murmushi ba๐Ÿ˜‡ a zuciyarsa cewa yake Alhamdullah my Angel taji sauki bayan an gama gaida shi shap shap yafara rubuta a saman white bord questions ya rubuta kamin nan yace every  body should take a sheet of paper we are going to write, a text yes uncle suka amsa Rukayya batace komai ba Dan ita har yanxu bata huce dashiba duk da Sajeeda ta roketa da tabar komai everything ,yazama normal , bayan ta Rubuta name dinta a paper bata wani. Bata lokaci ba ta fara rubuta text dinta saidai duk dagowar da zatayi sai sun hada ๐Ÿ‘€ dashi abin har ya soma gundurar da ita shikuma gogan ya kifa mata manyan Idanuwansa ko kiftawa bayayi ciki da so da kulawa wani sabon kaunarta yakeji yana ratsashi duk wani motsinda zatayi yana lura da ita dayaga ta dagoshi sai ya Ciro phone dinsa ya fara latse latse nan kuwa pics ne yake snapping dinta. Batama saniba yayita daukata pictures sunfi a kirga itace first data fara somiting din text dinta ta koma sit dinta ta zauna ita duk ta kagara yan class dinsu sukare text din Dan bama tason zama sa a class din nasu shikuma jiyake kamar suyita zama a haka after an kare text din karbar papers dinsu yayi ya fice daga ajin cike da shauki koba komai dai yau zuciyarsa zata samu sawaba kuma ya dauki pics dinta zasu debe masa kewarta.


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž 'YAR  BAIWAH ๐Ÿ™Ž2⃣6⃣


Maman Ussee๐Ÿ˜˜


Zaune suke a gurin da suka saba zama domin. Yin break shikuma Faruuq yana cikin staff room yana hango ta sai dariya takeyi da murmushi abin ya matukar kayatar dashi har a cikin zuciyarsa wani sabon farin ciki yakeji yana matukar kaunar Rukayya bayaso yayi missing din ganinta koda na minti dayane haka ya wanzu da kallon ta har suka koma Class Ya Salaam! Ya ambata Wai wace irin soyayyace haka yakasa fada mata and kuma a kullun ji yake soyayyarta na kara ratsa zuciyarsa.  Bai wani jima a skull din ba ya fita Dan dama sabida ganinta ne yake daukar time a skull din  direct gidansu ya nufa da motarsa da shigarsa cikin gida yar gdn sa ya tarar a Falo tawani hakince kallo daya yayi mata ya dauke Kansa tasowa tayi da niyar yi masa magana hannu ya daga mata ke dakata look Salma na fada miki tun ba yauba nidake bamu daceba and u still don't understand me, plzz ina rokonki 4 d last time let me alone karki hadani da Iyayena  Dan indan har kika kuskura kika shigo Rayuwa ta u wll regret, smiling  tayi kamin nan tace ai kuwa baka isaba umar Faruuq weather u like it or not u wll marry me am yours,you're my and only me mtseww yaja tsaki it seem like you're not in your sense ,shiyasa kike maganar abinda bama zai ta ba yuyuwa, ai kuwa. Baka Isa ba Dan nice mahaifiyar ka kuma dolene kabi umarnina abinda nikeso shi zakayi yau kwana ukku kenan banji komai daga gareka  ba saboda haka na yanke disission and it is Final , saboda haka kawai ka saurari zuwan Amaryarka Salma. Cewar Hajiya Kubrah tunda ta fara magana umar mutuwar tsaye yayi kasa motsa yatsansa yayi ji yayi jiri na Neman ka dashi kasa saurin rumtse idonsa yayi nawasu mintuna yasake budewa jiyake kamar a cikin marfarki Salma yagani zaune akan ciyar Hajiyarsa tana mishi murmushin mu gun ta , dakyar ya iya saita zuciyarsa Dan idan baikai zuciyarsa nesa ba kila a yanda yakeji zai iya kashe salmar kowama ya huta room dinsa yashiga yadade yana tunani kamin nan wani nannauyan bacci yasace shi, 

Rukayya dabatamasan meyake faruwaba tana zaune Class dinsu hankalinta kwance har aka tashi daga skull suka fice warsu gida itada Sajeeda .

Haka Rayuwarsu ta kasance har akayi Holiday tun ranar kuma bata sake ganin faruuq ba duk da tanaso ta daina tunanisa Dan bataga dalilin da yasa take sha,awar ganisaba a yanxu Dan tasan ba shiri sukeyi ba itadashi amma meyasa nake muradin faninsa oho tabaiwa kanta amsa kawai mantawa zanyi dashi Dan ba abinda ke tsakanin ni dashi haka kurun tunanina yarasa Wanda zai tunano sai wanda na tsana bayan anyi musu Hutu bada dadewa ba Daddy ya shirya musu tafiya Raba itada Sajeeda Dan acan zasuyi hutunsu hakan yayiwa Rukayya dadi ba kadanba koba komai zataga mamanta da  Baaba dakuma Abbanta kasa boye murnarta tayi har Ranarda suka daga dayake su biyu kadai Zasu Daddy sarkin tsaraba a kullun baya gajiya da lalurori haka ya shirya musu tsaraba mai tarin yawa yatafi dasu domin yakaisu gida murna gurin Baaba kamar me taga jikarta ta kara girma gwanin sha,awa nan nan kawai tayi da ita Daddy kuwa yasha Addu,a kamar me Dan kuwa malan Sa,idu harda kwala yayi gurin iya Daddy godiya bakomai ai yiwa Kaine Rukayya tamkar 'yace a gareni nadauketa tamkar Sajeeda  basuda wani banbanci a gurina Salame kam saboda kunya kasa magana tayi saidai murmushi bataso ta zake da yawa saboda Rukayya yar farice a gurin ta ,kwanan Daddy daya ya juya zuwa sokoto Dan aikinsa yakuma gaya musu ranarda zaidawo daukar su ba laifi yasha Tsaraba shima irin tasu ta mutanen k'auye shike da mutunta juna aka Rabu ana murna da farin ciki saidai duk da Zamansu a can din bai hanata tunanisaba har mamakin kanta takeyi lol Ruky an kamu da son uncle F๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜œ Sajeeda takanyi mata kirafi akan yawan tunane tunane but sai kawai tace mata bafa tunani komai nakeyiba kawai dai INA kewar mummy da Daddy ne haka zata kyaleta but itama kanta tasan akwai abinda yake damun sister dinta batason fada ne kawai kuma zata kyaleta inayi tsami saji cewar Sajeeda


Umar kam tun ranarda yakoma gida yahadu da baccin rai yayi alkawarin barin kasar kozai samu sawaba ga jiya sai shirye _shiryen aure sukeyi Alhaji Basheer kawai take jira aje asaka rana a biyawa diyan ta sadakinsu Dan kam harta hada lefe nagani na fada duk ta zauce ji takeyi kamar ma ace gobene saurin auren Dan kuwa Hajiyarsu Salma asiri taketa banka musu itada danta ganin ko anyi ma Umar baya tasiri shiyasa suka maida kambun yakinsu zuwa ga Hajiyarsa ba laifi a gurin su Dan kwalliya ta biya kudin, sabulu hakonsu na gamda cinma Ruwa. Shikan Faruuq  BISA yayi ta zuwa umara Dan acewarsa gara yakaiwa Allah kukansa kozai rage zafin ra dadin da zuciyarsa ke masa bada dadewaba ta fito bai fadawa kowaba sai randa zashi yayi musu sallama ya fice yayansa ya ajiyesa airport jirginsu yadaga sai kasa mai tsarki haka ya wanzu ba dare ba rana yana Addu,ar samun Rukayya Allah yasa ita alkhairi CE agaresa Alhmdllh addu,arsa ta karbu Dan kuwa yanxu Rukayya  batada wani aiki saina tunanin sa kwata2 wan nan hutun a Raba bata wani yi enjoying dinsaba. Maman Ussee๐Ÿ˜˜๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž 5⃣7⃣~Maman~ ~Usseey~๐Ÿ˜˜     ★ Masha Allah Abu yayi kyau Domin An Daura aure Lami lafiya komai yatafi yanda yadace Yayinda Yan Daurin Aure suka nufo Hanyar Dawowa Sokoto Dan Can Ne Bidirin Yake Dayake Daurin Auren. Ne kawai Malam Sa'eed yace azo Gida ayi sauran komai Yabarwa Baban Amarya wato Shugaban Biki Daddy๐Ÿ˜Š Wanda Yayi Alfahari da Hakan,, da Baban Rukayya yamasa.


   " A bangaren Amarya kuwa tun  Safe aketa shagalin Biki Amarya wanka ,, kawai take Dauka na mutunci Ba karya kam Sosai tayi kyau misalin . Karfe Hudu aka Fara walima Wanda Akayi Nasiha mai Ratsa jiki game da zaman Aure da yanda Hakkin miji yake akan matarsa. sosai Abin ya ratsa Jama,a Sai gab da magrib Aka yi Addu,a Allah yabawa Amarya zaman lafeeya da Samun zuri,a Dayyaba ,,Aka watse tun Kare walima Rukayya da Sajeeda keta Kukan Rabuwa Duk Wanda yagansu sai sun Basa tausayi Saida . mummy Ta nuna Baccin Ranta kamin Suka Hakura Dan Dolene su Rabu dama Sabo akewa kuka.         ★ Uwargida kam tun da FAROUQ yayi Fushi ya tafi taketa jin Badadi a Ranta,, Haka yaturo mata Sakon cewa Zai turo Ta Dauki abinda Takeso Yau zasu Tare a Sabon Gidansa Komai ya zuba mata aciki kawai Dai ta tattare abinda takeso Dan By 3:pm Zai turo adauketa ,, Tana kare karanta massege din Ta Fara tattara yan komatsan ta Zuciyarta sai Zafi take mata . Haka Yan uwanta da Danginta suka Zauna tare da Ita bamai Bata shawaran Kirki Duk zuga. Ta kawai Akeyi Wanda Hakan kara Ingiza Zuciyarta kawai yakeyi . Maman ta batazo ba Acewarta sai An gama Biki Zata Zo da Sabon Tuggu Dan Tasamu labarin cewa Salma Nada Juna biyu yanxu sun samu Gidin zama . A gidan Umar Farouq . (ohhh kuji min Mata 'yarta fa ke Auren Farouq din Amma ita Dukiyarsa,, CE kawai A Ranta Allah kashiryar Damu kasa mufi K'arfin Zukatan mu Ameen) Haka suka wuni Har Gurin 3 din kamin Yaturo aka Dauki Salma da Sauran K'awayenta Da yan Uwanta yan Kore masu Rakiya .

        ★ Ba,a Zarce dasu Ko,ina ba Sai Gidan Farouq Dake Unguwar Guiwa lowcost ,,, Gidane Babba nagani Nafada An kawata gidan Ba karya indan Nace Zan Iya Fayyace muku Yanda tsarin Gidan yake Yazama ,, Waist of Time . ๐Ÿ˜œ Lol . part Biyu ne A gidan sai Garden da Kuma Dan karamin swimming pool ,, da Filn Wasan Ball kusan Irin Ukku Basket Bolly da Kuma Hand Ball. Sai shuke shuke da kuma parking Space . Wanda yake da isowarka ,, Gidan Mutuwar Zaune Salma tayi ta sake Baki tanata Kallon kayyatuwar ,, gidan A Ranta take cewa Ohh All This is myn Wata ,, Zuciya kuma take cewa Ku biyu fah mtseww..... Taja Tsaki Wallahi dai Kishiya batayiba Acid CE Hava ,muna Zaune kalau a Hadani da ,, yar bakin Ciki zaki Ganene inkin Shigo Gidan Wata kawartace tadan  bugetah tace . 

      ” ke Ki fito Mana kin wani hakince a Cikin mota ni na matsu naga ,, ya cikin gidan yake Dan gaskiya Salma ur lucky kinga yanda gidan ya Hadu kuwa Sakowa tayi ta Nufi Dayan part din taga A Rubuta kamar Haka “ This Belongs' to RUKAYYAH!!! A Ranta Tace ,,, Ohh Farouq Dan Rainin Hankali ne jifa Ko gidan ban saniba gashi ,, Duk Nama Rasa INA ne Nawa part din Mai gadine ya iso Gun da Take ya ,, Rusuna yace Hajiya ,, Ga makulin Part dinki gaya can Karba tayi bayabo ba Fallasa ta nufi Dayan Part Din sauran Jama,artah suka Rufa mata Baya ,,Ta bude ta Shiga “Ni ma dai Sauri nakeyi na Shiga na ganewa Idona Menene Acikin Gidan Dan gaskiya Ba karya fah ,, Wow„ na Furta A Hankali. Dan A gaskiya ,, Ba,a cewa komai  wani Makeken Falone. Na Hango D'auke da Wasu Kayyatattun Kujeru komai Na Falon Black ne da White ,, Kai harma pent din Jikin Bango ,,, Dan Kara min koridor nagani Wanda Zai sadaka da Store da kuma Kitchen daga ka zagaya kuma Ga Dinning nan sai kuma wata yar Hanya ,, Wanda Zata sadaka da can Cikin gidan Dayan bangaren kuma Dakuna ne kusan ,, Guda Hudu a Jere sai Daya kuma A ,, Gefen Wadan nan da Alama Guest Room ne wato D'akin Bak'i . Sai kuma Wata Hanya Daga gefe Can na nufa ,, Wani Katon Falon nagani A gurin ,, Shikuma an masa Kwaliyar Pink komai pink da White color Fantastic na Fada ,, Tare da Zuba Idanuwa na Dan nabasu Abincinsu Shikuma Kofa Biyu ne nagani da Alama Dakin Mai Gidan ne Wata Hanya nabi naga kuma ta sadani da Dinning anan Nan ,, Ne Nafahimci Falon Maigidane Dana Salma Sai aka Sanya Kitchen a Tsakiyarsu dakuma Dinning Area ,, dawowa nayi nashiga Kifarda Naga su Salma sun Bude sun Shiga ,,,Zaune nayi Dana Hango wasu Mayyun Leader sit, Kut๐Ÿ™‰ mai kud'i ya More Wan nan Dukiya haka da aka zuba a Gidan nan Kuryan Room din wani Gadone Hadararre mai Rumfa! 

     ★ Suna Tafe ina binsu a Baya ,, Kowane Room sanda muka Shiga ba karya gaskiya Dakin , mai gidane kawai banmu shigaba Dan a kulle yake Falon suka Dawo nima nasamu Gurin zama ,,, sai Kallonsu nikeyi yayinda my Usseey. Yaga Ana shan Juice kala2 yaje yadauko Daya yafara sha banma lura ba sai Ganin shi nayi yanata zukar lemu ,,, Zare Ido nayi nace Kai ๐Ÿ™„ Rufa mana Asiri da shegen kwadayi gobe ma Bazan taho tare dakaiba Dan kar ka k'ara Kwasamin ๐Ÿ˜‚ lol.


    ★ Yan Daurin Aure sun ,iso lafeeya yayinda Ango da Abokansa basu Zarce ko,Inaba sai sabon Gidan FAROUQ . Dan anan zasuyi liyafarsu . yana isowa Kota kan Salma baibiba kawai Wuce ta yayi ya Shiga Dakin sa,, kawayenta sai tsokanar sa sukeyi suna Ango kasha Kamshi Murmushi kawai yamusu ya fice abinsa Salma ,,ta bisa a Baya yana Shiga itama ta Shigo Zatayi Magana yadakatar da ita da Hannu Durkushewa tayi ,,tafara mai kuka Abinda Bayaso kenan Dole ya Rarrasheta ,, Harsuka shirya kunsandai Mata da Miji sai Allah ,, Haka ta Daure suka Gaggaisa da fans Dinsa yayinda aka Bata kyata kala2 Kawayenta ke karba suna godiya,, yayinda Bakin Farouq yaki Rufuwa Har Gab da magrib kamin suka watse Dan suje akai Ango gurin Wankisa ๐Ÿ˜€.


     ★ Shirye2 aka farayi na zuwa wajen Wanke Amarya ,, Wanda ba,a Bata lokaciba ,,, Aka kaita bayan an karene Aka dawo da ita gurin mummy kuzo kuga. Kuka anxo Rokon gafara Haka mummy ma sanda tayi kwallah saboda sabo ,, kakar Amarya sai Baaba sai tsokanar Rukayyah take . haka taje Gurin Daddy dakyar ta Rabu dashi Dan Saida yamata wayo ta Hakura haka suka nufi ,,Gidansu FAROUQ aka damka Amanar Rukayyah a Hannun Hajiyarsa sosai tayaba takuma karba ta sanya Alkhairi Kamin aka wuce da ita Zuwa Gidanta Wato Gidan Ango FAROUQ .


  " Salma najin tsayuwar motar kawo Amarya Hankalinta ya matukar tashi ,,Jitakeyi wani. Abu na taso mata kamar Zata mutu . haka ta Daure ta Gimtse har aka Shigo da Rukayyah Lullebe da Mayafi ,, Aka Damkata Hannun Uwargida Sarautar mata Dakyar Salma tayi control din kanta Dan,, jinsu kawai takeyi haka suka karaci Surutunsu ,, suka Ja Rukayyah Zuwa part dinta Wanda komai Dayane Dana Salma saidai ita Kalar na Rukayyah Pupplene  da White ba laifi Daddy yakashe mata Kunya Dan itama an zuba mata dukiya wane Diyar wani Shahararren mai Kudi ,, Rukayyah Bata taba Tunanin Zata kasance Haka A Rayuwarta. Ba wan nan wata BAIWAH ce daga Allah Da Addu,ah a Bakinta tashiga har kuryan Dakin ta suka ajeta Saman Bed. Yayinda kowa yaba tsarin gidanta yakeyi wasu kuma Cewa sukeyi Rukayyatu tayi dace mudai Fatanmu Allah yabada Zaman . lafeeya da Zuri,ah Mai Albarka.~Maman~ ~Usseey~๐Ÿ˜˜  “Special Thanks to you my Beloved oneces ,,Bazan taba mantawa dakuba Nagode Sosai da Kwarin Guiwarku a gareni ”


★ Maman Khairy Allah ya Raya mana Ummul-khair.๐Ÿ˜‡

★ Ummu -Alkhairi B. B๐Ÿ˜˜

★Bintu Tijjani Zaifada ๐Ÿ˜

★ And my Lovely Aunt Sister Zainab Mai Kano Allah yakawo yan Biyu Ameen๐Ÿ˜€.

 Thanks much more Luv u all my Fans Lodi-Lodi๐Ÿ˜˜.๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž5⃣8⃣


 ~Maman~ ~Usseey~๐Ÿ˜˜


   ★  Gidan Amarya ya Rage daga Sajeeda sai Afra da Afnan da wasu Fans Dinsu  mutun Biyu ne su Biyar kenan. Yayinda Rukayyah ke lullub'e a Mayafi Zuciyarta sai duka takeyi ,, Wai yau itace a gidan Aure gidan Umar Farouq abu kamar Almara .

      "Sajeeda tace wai yaushe ne Zasu kawo wan nan Angon ne 10:30 fah Afra tace kin San sai anmasa Huduba kuma kinga Sai sun tsaya Dan Kinga dakwai masu so Su yi masa Naseeha Dan Rike macce Biyu sai jarumi Sajeeda tayi Dariya tace Tab kenan . Yayanku Jarumi ne ko Afnan tace sosaima ,, kinga zai nunawa Sistern ki Jarumta irin tasa Aisha tace kai kudaina Tsoratata mana kufa zolayace daku Safeena tace No way Ai dolema ya Hakura saboda Sabon Shiga CE Sajeeda tace Ohhh kukan Allah yashiryaku kunga kamar naji Tsayuwar mota may be gasu nan sunzo Suka kara feshe ko,ina da Turare kamin suka sami Gu suka zauna Rukayya Hawayene kawai ke zuba a Idan nuwanta Dan yanxu ne yakara tsinkewa lol๐Ÿ˜œ.


     ★ Bayan an kare wankin Ango Gidansu aka nufa Dan Ayi masa,, Hudu ba sosai Alhaji Basheer ya Masa Nasiha mai Shiga jiki yayi Adalci a Tsakanin su karya nuna musu banbanci Kuma ya Rike su Amana,, Ya tsaya tsakani da Allah karya fifita wata akan wata ya kwatanta Adalci  . Haka aka kaisa gurin Hajiyarsa Itama dai Fadan tamasa na a Rike Aman da Adalci ,, daga nan aka Daukeshi zuwa gidansa Abokansa sai tsokanar sa sukeyi ,, Shikuma sai Dariya kawai yakeyi yana Wani jin Dadi har suka iso Part din Salma suka nufa dashi ,, Suna Zaune itada Kawayenta daketa zugata da Sallama suka ,, Shigo aka tsaya Akayi jawabin na Salma ta zauna lfy da yar uwarta Kuma Farouq ya kwatanta Adalci ,, Akayi Addu,a Kamin aka  Baiwa Salma Kayanta na tande  tande ,, Ba yabo ba fallasa tayi masa saida Safe shima ya mata ya lura sosai Bata cikin Kwanciyar Hankali,, amma bayanda ya iya haka  Suka Ja Farouq zuwa part din Gimbiya Amarya .

   

   ★ Da Sallama suka Shiga yayinda wani Daddad'an kamshi mai sanyaya zuciya ya doki Hancinsu da Sanyi mai Dadi ya Ratsa su har Kuryan Daki inda Rukayyah take suka kai Farouq sai Daukan su Photo akeyi gwanin kyau Haka aka yi Barkwanci da  Haka dai suka karasa komai suka D'auki Su Sajeeda Domin kaisu gida ya Rage daga FAROUQ sai RUKAYYAH . What a wonderful Day Shurune ya Ratsa Nadan  wani Lokaci Yayinda Farouq yayi gyaran murya yamatso kusa Da Rukayyah ya Bude mayafinya tare dacewa . Amincin Allah ya Tabbata gareki yake ma,abuciyar Kyau. Girgiza mata Kai yayi Dan Ganin Hawaye ,, a Fuskarta Hannu ya sanya yashiga goge mata Fuskarta yayinda ya umurceta data tashi ta Dauro Alwala su nunawa Allah Farin Cikin su Da Zuwan Wan nan Ranar mai Albarka.  

    " Ba musu tashiga toilet tayi Alwala shima yashiga yayi yajasu jam,in Sallah Raka,a Biyu sukayi kamin ya matso kusa da ita ya Dora  . Hannunsa akanta yashiga yi mata Addu,ah da kuma Fatan Samun Zuri,a  Tagari . kamin ya je ya Dauko Plate da cup ya dauko Leda Wata gasaasar kaza yazuba a plate din ya Dauko fresh milk ya zuba dakyar ya lallab'a ta ta ci kadan bada yawa ba kamin tayi brush Shikuma ya fita anan ne Rukayyah ta samu ta zauna a saman bed duk sai taji wani iri saboda Bata saba ba . farouq kam Dakinsa dake part din Rukayya yanufa yashiga Toilet ya washa Ruwa kamin yafito ya feshe Jikinsa Da Turare Yana katewa ya nufi Room D'in Rukayyah Zaune ya tarar da ita Yace a,a wai Ke Zama ma kikayi ,sunkuyar da kanta tayi kasa ya matso kusa da ita yace kinga kidai kije ki cire wan nan kayan ko na cire miki su da kaina Rasa mezatace masa tayi sai murza yan yatsun ta takeyi matso wa yayi kusa da ita ya ,, Fara Rike mata Hannu wani Shock ne taji yajata Dakyar ya lallabata tayarda tacire kayanta ya Dauko mata wata Sleeping Dress .Purple colour. Had'ararriya ta Hadufa ba karya gaskiya yaja Hannunta suka fara zagayawa sanda yanuna mata komai dakomai hard Room dinsa saida yakaita ita dai Takasa sakewa Bayan yakare nuna mata komai ya dawo da ita zuwa Room Dinta Upp din. Wuta yayi yakara A,c suka kwanta Yajawota ya Rungumeta can cikin Jikinsa Jikinta ne yafara Rawa Dayaga Haka sai ya Rada mata a kunne just be Free ba Abinda zan. Maki duk da Haka Bata Sake ba Haka yashiga wasa da ita son Ransa Sanda yakusa Wuce gona da iri Rukayya ta Fara masa kuka badan yasoba ya barta A haka sukayi Bacci Wanda zankira da An daiyi maganin Ace Ba,ayi ba Dan Ba Wanda yayi Baccin kirki  acikinsu Sai guraren Asuba ya barta yatashi Dan zuwa masallaci ita kuma ta Shiga Toilet wanka tafara yi kamin tayi Sallah ta zauna tafara karatun Al-Qur,ani Mai Girma har gari ya waye.


      ★Tun ficewarsu Farouq Salma takasa Zaune takasa tsaye da kyar ta iya control din kanta ledarma ko Kallon ta batayiba fuu tashige Room Dinta kawayentane sukaci kazar Banda kukah ba abinda Salma keyi ba irin Zugarda Zuciyarta batayi mata ba  O my God yanxu Farouq dina na can tare da wata ko wane karatun yake koya mata oho Ashe haka mata sukeji idan An masu Kishiya da gaskene Ashe Ba,a Bacci haka ta wanxu cikin Tunani Matar tasiri Har Garin Allah ya waye yanda taga Rana haka taga dare . Shigowar Farouq ne ya sanyata ta fara Baccin karya kamar gaske tayar da ita yayi yace taje ,, tayi Sallah Lokaci yayi kamin yashafa cikinta yabata kiss ya wuce mtsewww taja Tsaki Aikin Banxa Bayan ka gama Lalacewa da wata shine zakazo kamin Dadin baki( Hattara mata wallahi muji Tsoron Allah yakamata musan irin abinda zamu gayawa mazajenmu saboda mumuke Neman Aljannah a gunsu Allah yasa mudace Ameen.) Haka ta Daure taje tayi Alwala tayi Sallah ta Shiga wanka bayan ta idar da Sallah tafito tashirya cikin wata Atamfah Dinkin mai kyau tana ta wani cika da batsewa kamar wadda Akayi wa laifin Wani Abin.


  " Bayan ya dawo daga masallaci part din Rukayyah ya Nufa ya tarar da ita tana ta karatu murmushi ya sakar mata kamin ita kuma ta Gaidasa ya Amsa ,, yace Yauwa Sarkin tsoro murmushi tayi cike da kunya kamin ta gama ta fito tadan gyara wasu abubuwan Dayake ma komai Normal yake sabo ne kawai dayi Sai Farouq kam Room dinsa ya nufa ya koma Bacci Rukayya ko rasa abinyi tayi taje kawai ta kunnah T.v tashiga Kallo Abinta.

   " misalin 8:30Am  Afra tashigo gidan D'auke da Kayan Breakfast nasu Da murna Rukayya ta tareta tace sai yanxu Afra tace tab koyanxuma sakone,, yakawo ni kinga Ficewata ma zanyi Dan Banaso Yaya ya Yiman surutu yafara cewa INA masa ,,Sakko tun da safe a gidansa ,, Murmushi tayi ta karbi kayan ta jera a dinning table Afra Bata wani jima ba tafice tace Zata dawo zuwa anjima Rukayyah cigaba tayi da kallonta sai gurin 9. farouq ya fito D'auke da Fara,arsa yasha wankan Boyel milk colour ,, yace yadai my Angel ,, tace lfy Lou Kinci Abinci ne ta girgiza masa kai yace A,a Ba tun dazu aka Aiko Da Abincin ba tace eah INA Jirankane yace OK to zo muje muci tare suka ci Abinci saida Farouq ya Tabatar taci ta koshi kamin ya barta Ta gyara gurin ,, ya umurceta data Dauko mayafinta suje part din Salma ,,  Ba musu ta yi yanda yace yayinda yake Gaba tana biye dashi Baya har suka is a Part din Zaune suka tarar da ita Da. Sallama suka Shiga Rukayyah ta gaidata Wanda dakyar ta Amsa Farouq ne yanuna mata guri ta Zauna Shuru ne yadan Gifta kamin FAROUQ yafara magana kamar haka :


    ★ Salma Kinga ga Rukayyah nan Amanace a gurinah kuma a gurin ki  Banason Fada,, Kuma Ku zauna lfy da juna Ku mutun ta junanku duk kanku INA sonku shiyasa na zauna tare Daku Rukayyah Ki Baiwa Salma Girman ta karki Rainata kibita Duk abinda takeso indai bamai wahala bane kimata kinsan Junah biyu gareta sai kinyi Hakuri da ita kinji Tace Insha Allah yace Good . Allah yayi maku Albarka yabani Ikon yin Adalci a Tsakaninku Rukayyah tace Amin kamin ya fice ita ma takoma part dinta Dayake Yan Yinin Amarya sun Fara Isowa haka dai Suka kasance Har Rana tayi.Maman Usseey๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž5⃣9⃣ ~Maman~ ~Usseey~๐Ÿ˜˜     ★ Gab da Azhr Su Sajeeda sukazo sosai Rukayyah taji Dadi suka Zauna sukayi ta tadi sai barkwanci sukeyi gwanin sha,awah sai tsokanar ta sukeyi badai ta kulasu banda murmushi ba,abinda take musu Haka suka zauna sai Dare Suka gyara mata Part dinta tsaf sai Kanshi ko,ina yake yi Basuda matsalar Abinci Dan Daga gidan Hajiya Ake kawo musu ,, Koyanxu Abincin aka kawo su Afra suka Ni Driver Dan Ya ajiyesu gida harda Sajeeda sanda suka ajiyeta a gida suka wuce Warsu gida.

    "Rukayyah wani wanka ta Dauka mai Daukar Hankali ta Zauna a sitting Room tana Kallo Abinta Dan Yau bakonta yazo Hankalinta a kwance. Batada wata damuwa phone dinta ne yayi Ring ta Dauka tare da Sallama ,, mummy takirata da wayar Sajeeda tace Yadai 'Yata lafeeya Lou kike ko tayi murmushi tace lfy mummy  ba komai yauwa Dama dan na gaya mikine Ki Duba Acikin Jakar da Sajeeda ta kawo miki zakiga ,, Wasu ledar guda biyu Dayar turarene na Humrah a Ciki dayar kuma maganine ki sha da Madara tace tau Insha Allah sun tan taba Hira daga Bisani Kuma suka katse wayar . ta sauke Ajiyar zuciya kamin ta ci gaba da Kallon ta.

    ★ Farouq Bai dawo gidan ba sai guraren 9:30pm Da shigowarsa bangaren Salma ya nufa Baiganta anan fallo ba ya Shiga Dakin ta kwance yarar da ita Hawaye duk ya Bata mata Fuskarta ,, wurin Gadon ya nufa Ya kira Sunan ta Salma. Bata kallesa ba Tace wai Salma menene yake damunki Kwanan nan duk Kin wani Rame kin Hana kanki sukuni wai menene Nifa ban kara Aure Dan na muzguna mikiba Dan Allah ki cire komai Aranki please hava Kamar wani abu duk kinbi kin Hana kanki sukuni Batadai ce dashi komaiba ya Rugumeta yafara lallashinta ,, dakyar yasamu ta Hakura shiya bata Abinci da kansa ya bata maganinta tasha Dan yaji Jikinta yayi Zafi saida yaga tadan Fara Bacci ,, kamin yatashi ya wuce  bangaren Rukayyah .

  ★ Da sallama yashiga wow" Ya Furta a Hankali saboda wani Daddadan kamshi da Sanyaya zuciya Daya doki Hancinsa Amsa Sallamar sa tayi tare da Gaidasa ya Amsa yace hope dai Bakiyi Fushiba Dan na makara tace No Bakomai Yace OK Kinci Abinci ta girgiza kai yadan Bude idonsa yace tomeyasa Kosai tare dani Batadaice komai ba ta saddan kanta ,, Kasa tana murza yan yatsun ta Matsowa yayi ya Shafa Gefen Fuskarta Yace zan Cire wan nan kunyar Dan. Naga Alama Zata takurani yanufi Room Dinsa saida ya Rage kayan Jikinsa ya yasanya Short Nikkah da Yar Singlet ya fito Kallo Daya tamasa Ta sauke kanta Kasa ,, Hannunta ya Ja suka nufi Dining Dan Cin Abinci Sunayi suna Yar Soyayya Nakuma gefe Inata Kallon Ikon Allah. 

     " Bayan sun Kammalah kowannensu Dakinsa ya nufa Rukayyah  Brush tayi ta watsa Ruwa ta sanya Nightes masu shegen kyau Jajaye ,, ta Bude Tuearenda Mummy ta Aiko mata tashafe Jikinta dashi ko,INA Kamin Ta zauna kusa da Bed Dinta tana Kallon pictures din da Sukayi Dazu itadasu Sajeeda. Farouq ne yashigo Dakin Shima Kayan Jikinsa Ja ne masu Guntun Hannu Zaunawa yayi kusa Da ita Yace mugani ta basa wayar sukaci gaba Da Kallonsu tare Wani yayi Dariya wani kuma yace kai Kukam dai Kun iya Daukan photo to bari nayi mana wani pic din ,, Ya Jata sosai ajikinsa yamasu photo Selpic Kamin ya Dora mata kiss Wanda ya Ba,in kashe mata Jiki ,, Turning Off din Wutar Dakin yayi yafara Yimata wasan ni Da Zafi Zafi Wanda Rukayyah ta Kasa Gane Ko tantace a ina take ,, Ganin Zai wuce Gona da iri yasanya  ta CE dashi Bakonta yazo ,, Dakyar ya iya Control din Kansa Amma fah Duk da Haka ,, Tasha Wahala Dan Dakyar Ta lallabasa ya Hakura ,, Amma yadan samu Relief sosai Rugumeta yayi sukaci gaba da Bacci Kulle musu kofa nayi Tare dayimusu Fatan tashi Lafeeya.

     ★ Sajeeda CE kwance a Room D'insu sai juye juye take saboda tasaba komai tare sukeyi itada Rukayya yaigashi Bata jin motsin kowa Lallai Yaune take jin Rabuwarsu da Rukayyah Dan Abin duk yataru yamata yawa gara Jiya Dakwai mutane to Yau kowa yayi Tafiyarsa Abin ba Dadi A Hankali ta Furta tace I miss You Sister. Allah yabaki zaman lafeeya da Kwanciyar Hankali.  Wayarta ta Dauka tashiga whatapp ,,, Dan ta tagewa kanta lokaci da Dare . saida tafara Jin Bacci ta Ajiye wayar Ta kwanta Sai Safe Daddy ya Buga mata kofa ta Tashi tayi Sallah tadanyi Karatun Al-,Qur,ani Sai Karfe 8 Tatashi tashi Kitchen Dan Ta Dora Breakfast ,, A kitchen Mummy ta Tarar da Ita Tace Hoo sannu Yau kinyi Abin kanki Murmushi Sajeeda tayi tace Mummy an tashi lfy tace Lou Yau kin fito Da wuri tace eah Mummy tace Dan kinsan Ba maiyine keda kikeda Son jiki  Murmushi Sajeeda tayi kamin suka ci Gaba da Hada komai a Tare Har suka kammala Hada komai Suka jera a Dining ,, Kowa yakoma Dakinsa Sai 10:Am Suka fito sukaci Abinci kamar yanda Suka Saba Kullun ,, Daddy yace Allah Sarki 'Rukayyahtu ana can mummy tace Ashe Bamu kadai ke Missing dinta ba yace gaskiya Baku kadai bane ,, Yauwa Sajeeda Gobe Ki shirya kifara zuwa skull Ki shirya da wurifa Dan nasan Halinki tace Angama insha Allah yace Good ,, suka ci gaba da cin Abinci bayan sun kare Sajeeda tashiga gyara gurin mummy kuwa Tashiga kitchen Dan Ta Dora Girkin Rana .


      ★ Da Asuba Farouq yatashi yayinda ya gyarawa Rukayyah Kwanciyar ta Dan Jiya baibarta tayi wani Baccin kirkiba wanka yafara yi ya nufi masallaci Dan Gabatar da Sallah sanda yanufi Part din Salma ya tayar da ita kamar Yanda yayi jiya ,, Bai shigo. Ba sai Da aka kare Sallah Yadawo Room dinsa yanufa ya kwanta.

      " Rukayyah kam bata Tashiga sai ,,, Guraren 7:30Am toilet tanufa tafara wanka tayi Brush kamin tafito tashirya tsaf da ita daganinta kaga Amarya yauma kamar jiya gyara ko,ina tayi ta fesa Turare tadawo Ta zauna tana Kallo a Sunnah T.v Kwankwasa kofa taji anayi ta tashi ta Dauko mayafin ta kamin ta bude kofar Driver ne shikadai D'auke da Breakfast yace gashi inji Hajiya tace a Gaidaki Rukayyah ta karba ,, Tace yauwa kace Angode Nima ina gaidata ta Kulle kofar ta jera komai a dinning ta ci gaba da Kallon ta Hankali kwance .

  


~Maman~ ~Usseey~๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž6⃣0⃣


Maman Usseey๐Ÿ˜˜


     ★ Sai guraren 10:Am Umar Farouq yatashi sai wanka yafara yi Kamin ya shirya tsaf Ya fito ya tarar fa Rukayyah nata Kallo da murmushinsa ya iso gareta tare da Shafa Fuskarta,,, Amarya Bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida . tadanyi fari da Ido tace Bama zan kashe kowa ba Yace to muje muci Abinci Dan Nasan Bakici kina jirana ko kai kawai ta Daga masa yaja Hannunta suka nufi Dinning area.

       " A tare suka ci Abinci Yana ta tsokanarta bayan sun karene yayi ficewarsa ita kuma tashiga gyara gun dasuka bata Ta wanke Kayanda aka saka musu ,, Abinci a Ciki ta sanyasu cikin basket Dan dama Haka takeyi idan An kawo Na Rana sai ta Bayarda na Safe hakama idan an kawo nadare saita Bayarda . kayan Rana Da Safe sai ta Bayarda na Daren Tadawo ta Zauna ta Rasa Abin yi kawai sai ta kira Abbanta bayan sun gaisa yake Tambaya ta ya Sabon guri Tace lfy Lou Alhamdullah ,, Haka sukata fira yabaiwa Ummanta harda Baaba ma sanda suka gaisa Daga nan Ta katse wayar ta kira Daddy shima Tambayarta yayi ya sabon wuri tace Lfy Lou ya kara yimata Nasiha mai Ratsa zuciya game da Zaman Aure ya Sanya mata Albarka haka tayi ta kiran Yan Uwa da Abokan Arziki Suka gaisa Harsu Afra saida ta kira Tace su Turo mata No din Hajiya bayan Ta kammala wayar ne Ta kirata cike da girmama,, Daga dayan Bangaren aka Amsata sosai Hakan yayiwa Hajiya Dadi ta Tambayeta dafatar Ba Wata matsala tace Bakomai lafeeya Lou yauwa Haka akeso Allah yayi maku Albarka Rukayyah ta Karba da Ameen ta Ajiye wayar Ta Dan kishin gida kadan Batasan Sanda Bacci ya kashe ta ba .

      ★ Farouq ne Zaune a room Din Salma wadda yakasa Gane ma kanta cikin kwanan nan Yana dai Biyematane Dan Bayaso Yashiga Hakkin Ta Allah yagani Bazai iya jure Rainin Hankali ba Dakyar yasamu ya lallasata taci Abinci saikace Gareta Aka fara Kishiya duk ta fita Hayyacinta Bayan taci sosai ya Bata magani Tasha Shida Kansa ya mata wanka yadawo da ita ,, Room dinta Ya kwantar Kamin ya yi Ficewarsa Dan Amsa kiran da Alhajinsa kemasa.

   

   " Haka Rayuwarsu Takasance a Tsawon Satin nan Har Ranarda Ya Raba masu Girki Ya Kara tarasu Ya Musu Nasiha mai Ratsa jiki Wanda Rukayyah kawai ta Dauka Salma kam Biris tayi Dan Ita yanxu Kwata2 ta canja daga Sanin da Farouq yamata Salma ce Zata Fara yin Girki Wanda Farouq ya CE Duk mai yin Girki to A part Dinta Za,aci Abinci Hakan bakaramin Haushi yayiwa Salma ba Amma ba yanda ta iya Dole ta Hakura Dan tasan Halin FAROUQ Baya canja,, maganar sa " Shikuma yayi Hakan ne Dan A kara Samun Had'in kai A tsakanin su ,, 

     " Da Dare Salma ta Rangada Girki Mai Rai da motsi yayinda ta Ci uban make ,,upp kamar ba itaba ajima Anjima ,,ta Duba agogo haka Ta tsara komai sai wani Kisisina takeyi Farouq baidawo ba sai misalin 9 Bangaren Salma ya nufa Da murna ta Taresa Shikuma sai wani Biye mata yakeyi Dan Farouq Mutun ne maison a tarairayesa nan da nan ta Gama dashi Room dinsa suka Nufa ya Rage kayan Jikinsa . Ganin Abin na Salma bamai karewa bane yasa ya dakatar da ita yace Dear sorry kinsan yanxu Bamu kadai bane Jeki ki kira kanwarki muci Abinci Kinga tana Jiranmu badan Taso ba ta Tashi yayinda Shikuma yadawo sitting Room yana jiran Isowar su.

     ★ Rukayyah na Zaune  A Dakinta Bayan ta karasa  Sallah Isha Dan yau tayi Wanka karatun Al-Qur,ani mai Girma takeyi Da murya mai Dadi a gurin mai Saurare Salma tashiga Noking din Door Rukayyah bataji ba Dan Dayake karatun ya D'auke mata Hankali Abin ya matukar Tunxura Salma tace Lallaima wan nan Yarinyar dani take Zance murda kofar tayi tajita a Bude Sa kai ,, kawai tayi Mutuwar tsaye tayi Dan Yau itace Rana ta Farko data taba shigowa part din Rukayyah tun Kawota A cikin Zuciyarta tace Tab Wan nan Dukiya da aka zuba mata a gidan nan kamar wata yar Hamshakin mai Kudi A Hankali ta fara Notice din komai Har kitchen sanda tashiga bata Tsinkeba saida Tashiga Room din da take jiyo Saurin Kira,a natashi bako Sallama ta Bude tashiga Zare Ido Tayi dataga Wani Hadararen Royal Bed ,, Da kyar ta Hadiye Yawo Tare da gyaran Murya Rukayya bata Dago ba saida takai Aya ta dago da Murmushi a Fuskarta Lah Aunty Salma kece yau Shigo Zauna mana Yake Salma tayi tace No bazama Zanyi Abinci zaki fito muje muci Rukayyah tace OK ganinan zuwa Barin Room din Salma tayi Tana ta Magana a cikin Ranta lallai wan nan saina Tashi Tsaye yarinya kamar yar Tsana Hmmm Tabdi ,, tayi  wucewarta zuwa nata part din Nidai Binta nayi Da Ido INA Kallon Ikon Allah ๐Ÿ˜€.

   " Rukayyah Kara Feshe Jikinta tayi da Turare Aoud mai Dan Karen Kanshi kamin ta Dauki mayafinta ta Rufe Jikinta tana tafiyarta Hankali kwance Harta Isa Part Din Salma da Sallama tashiga ,, Part din Fuskarta D'auke da Murmushi Farouq ya Amsa shima murmushin yakeyi Gaidasa tayi tamin ta samu guri tazauna Batare da Bata lokaci Farouq yace muje muci Abincin ko Salma sai Hararan Rukayyah take Ganin irin Kallon da Farouq yake mata A Ranta tace Jarababa yaudai kya kwana ke kadai mayyah kawai( Jama,ah kujimin Salma Da Wani zance oh oh mata Da kishi ) Rukayyah batamasan tanayiba Samun Kujera tayi yazauna Abinta yayinda Salma ta fara zubawa kowa Abinci Tanayi tana Jan Hankalin FAROUQ Wanda Gabaki Daya ya Mutu a gurin Kallon Rukayyah Dakyar yasamu yayi control din Kansa ya  kula Salma Bayan sun Kammala cin Abinci suka Dan Taba Hira Sama2 Rukayyah tayi musu Sallama Zata wuce Farouq yace Angel kona Rakaki ne Tace no Kayi zaman ka Badamuwa Salma tace wane irin karakata Halan dazata zo wanine ya Rako ta , no kinsan Yanxu Dare yakara yi kar taji Tsoro Turo baki Salma tayi Yace lallai nida naje kiranta Dazu wani ne ya Rakani Ganin Zata miyarda Zancen wani Abu yasa ya Dauko wata Caftar aka  Basar da Zancen.

    

 ★  Sosai Salma tayi mamakin Ganin Irin yanda Farouq yaketa Rawar jiki Daya ,, kusanceta Kwata2 Batama yi Tunanin Samun irin Haka daga Garesa ba Baccima Kalilan yayisa Wanda Hakan ba karamin Dadi yayiwa Salma ba a Ranta tace wayasani koya Canye abinsa kamin a shigo karyar Banxa Anxo ana mana wani fankama ashema nafita sai Rawar jiki yakeyi akaina ina Amaryar Haka tata kitsawa Har Bacci ya kwasheta . Rukayyah Baiwar Allah Tun da tadawo part dinta tarasa Abinda kemata Dadi Saboda a kwanan nan tasaba sosai da FAROUQ yaugashi Zata kwanta ita Daya wata Zuciyar kecemata yanxu yana can Yana yiwa matarsa irin yanda yake maki wani Abune taji yataso mata Ganin Tunanin ta zaiyi yawa shaidan zaiyi tasiri akanta yasa Tace "A,uzubillahi minal shaidanirrajim" Ta Basar da Zancen kwanta wa tayi a beda dinta sai juye juye takeyi Ganin Rakasa Bacci yasanya ta Dauro Alwalah tashiga yin Nafillah Sallar dare Dan Neman Samun Zaman lafeeya da Kwanciyar Hankali Yauwa maccen Kwarai Diyar Albarka Saliha acikin mata nagaidaki Macce Tagari.Maman Usseey๐Ÿ˜˜


๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž6⃣1⃣*Maman* *Usseey*๐Ÿ˜˜    ★Washe Tun da Asuba Farouq yatashi Yata yar da Salma Kamin ya Fito ya Nufi Part Din Rukayyah Dayake yanada keys na kowane part . Bude Kofa yayi Yashiga a Hankali yake jiyo Sautin Muryan ta Tanata Karatun Cikin Murya mai Dadin Saurare Murmushi Yayi Yace Alhamdullah a Fili Wani Dadi ne ya Ziyarci Zuciyarsa ,, Saboda Tun Aurensa Da Salma baita ba Ganin ta Dauko Qur-ani ta Karanta Ba duk da Yana iya Bakin k'okarinsa Wurin Ganin tasamu Ilmi saidai Yau Yakasance Abu mafi Girma a Rayuwar sa Ana Karatun Qur-ani A gidansa Bayan shi Sabanin Wakokin da yasabaji A gurin Salma wata Soyayyar Rukayyah CE takara Shiga Zuciyarsa ,, Sosai da Sosai  Da Sallama yashiga Room Dinta Zaune yaganta a Saman Sallaya Sanda takai Aya kamin ta Dago ta Amsa Sallamarsa Da Murmushi ta Gaidasa ,,Barka da Asuba ya Amsa Da Yauwa Hope kin tashi Lafeeya ,, Qlau Alhamdullah , yauwa Nixanje Massalaci dama Dan Natashe kine na manta Matar Tawa Malamace Abin Dariya yabata Tace wane Ni Daliba Dai yace koma Dai menene Allah ya karba ta Amsa Da Ameen Kamin ya Fito Dan Zuwa Massalaci ya sallaci Asuba.

      ★ A bakin Kofa sukaci karo da Salma wadda tayi labe tana Saurarensu Turo baki tayi Farouq yace Salma Ba Sallah nace Kije kiyi ba To ai gani nayi Ba ita keda Girki ba Amma kawani Zo Part Dinta Nifa Banaso A Shiga Hakkina ,, Hava Salma wan nan Wace irin Maganace Dukkan Ku Magana ne kuma ko wacce tanada Hakki akaina Dan Nazo naga Ya tashi Kuma Natayar Da Ita tayi Sallah shine Shiga Hakki Eah Shiga Hakkine mana Aida Kace Ni naje Na tasheta bakaiba Mtseww yaja Tsaki to Badani a Wan nan Tsarin. Ba Kuma dole kibi yanda Na tsara Gidana yayi ficewarsa yabarta saida ta Harari Kofar Part din Rukayyah kamin ta wuce nikuma nace A Banxa Harara A Duhu Dan Wadda kikayi Domin ita bata ma San Kinayi ba .


" Rukayyah bayan ta Kare Sallah Asuba Wanka tashiga tayi ta zauna ta tsara kwalliya kamin tadawo parlour ta Zauna ta kunnah T.v tanata Kallo Abinta wayarta CE tayi Kara ta Duba Sunan My Sist tagani Murmushi tayi tace Sajeeda early in d morning ko lafeeya Daukar wayar tayi Daga Dayan Bangaren Sajeeda tace Amarya Bakya laifi Ya Amarci Rukayya ta Amsa lafeeya Lou gashinan munayi good Dama Yau zan Fara Zuwa Skull Na shirya ne saina tunoki nace  Bara nakira naji ki Rukayyah tace Ayya Sist Allah yabada zaman Lafeeya yasa A dace kinga Kallo ma nakeyi Amma Dai zaki biyo tanan ko Sajeeda tace Ban maki Alkawari ba But saidai nagani sun Dan Taba Hira daga Bisani suka Ajiye . wayar 


 " Bayan yadawo daga masjid Yatarar da Salma Sai wani Cika take tana Batsewa a Dole Bai mata Adalci ba Ko kula ta Baiyiba yashi gewarsa Room Dinsa Harda Sa key Alamar Karma ta Damesa Gama Borin Haukan ta tayi tashiga kitchen Dan Hada Breakfast Ita wallahi wan nan Aikin yamata yawa Dole ma yasama mata yar Aiki Dan Bazai yuyu tarika tashi Kullun tana Hada Break ba Gashi ita bama Wani Abin kirki takeci Ba ta Tuna Ada in bataso ba Saidai suyi Baccin su Har su gaji in sun tashi zai Je ya yo musu ,, Take Away Amma yanxu Tun ba,aje ko,inba Tafara Tashin Safe Kai Wallahi Bazata Sabu ba wai Bindiga A Ruwa Wan nan Tsarin Sam Baiyi ba A Gaskiya Kishiya Takura ce Ina Zama na kawai a hadani Da Wahala  , wahala mana Gashi duk nagaji Mtseee gaskiya da Sake Ita kadai taketa Sambatun ta kuma dole ta Hada Break din Amma Kamin a kammala Anyi Dogon Baki yafi a kirga tsaki ba, Bayan ta Jere komai A Dinning table kamin tashiga wanka  tana Cikin shirya wa Wayarta tayi Ring ,, Ta Dauko. Farouq ne Baima jira maixata ce ba ya CE da Ita idan kin gama Hada Break kije ki kira Yar Uwarki Ya kashe Wayarsa Bin wayar tayi Da Kallo kamin daga Bisani ta Fito Kamar karta je but Sanin Halin Umar yasa taje Dole ta kirata Koda ta Dawo Yana Zaune a Fallo yana jiran su ,, Samun Guri tayi ta Zauna Kamin Da Sallama Rukayyah tashigo Fallon Salma na Lura da Irin Shu,umin Kallon da Umar Farouq yake mata A Zuciyarta tace A Banxa Saboda Kyauwun Fuskar kawai ne Dani ake Tutiya Dariya Tabanifa Sosai ,, na CE Hodi Jan Kishi Gamai Yinka ,, Haka suka zauna A Dinning Salma tayi Serve Dinsu ,, Sanda suka karene Salma Tace Dear ,, Please maganar Yar Aikin nan gaskiya Aikin yamin yawa kuma kaga yanxu Banikai nikeba ga Babynka Banaso Yasha wahala sosai ,, OK. Za,a kawo Insha Allah Dama Mun kammala Zancen Da Hajiya  But Ba ke kadaiba Harda Rukayyah ma Hava Dear kasan Mai Aiki Daya fah Bazata iya Aikin gidan nan kawai kamo mata wata gaskiya ,, Rukayya tace No Aunty Bama sai ya samo wata Ba Ai zan iya kawai dai Akawo miki Dan Kar Babyn mu yasha Wahala Murmushi FAROUQ yayi yace a,a Angel kema za,a Sama miki Dan Kema Banaso ki Wahala kinji Wata uwar Harara Salma ta Banka wa Rukayyah a Ranta Tace Nikuma so kake nawahala ba Aikin Banxa,, A,a Dear taya mutun Yace Bayason Abu za,a mai Dole kawai ka kyaleta ba tace Zata iya ,, FAROUQ yace ai Nine nace Zan damo Saboda haka zan Samo muku Ku Duka OK . Badan Taso ba tayi Shuru Dan kar tajawo wa kanta wata Maganar , 


 ★ Haka suka Kansance Har Girkin Salma ya Kare Rukayyah ta Karba ,, Wani Lafiya yan Girki ta Rangada mai Rai da motsi Dayake Rukayyah Rainon Mummy ce  Ba wasa gurin Iya Girki Bayan ta Hada komai a Dinning table tashiga wanka tsaf da ita Yanda FAROUQ yasaba shigowa yauma Haka Yashiga Wani Kamshin Dadi ne Ya Ziyarci Zuciyarsa Sannu da Zuwa tamasa kamin ya Amsa da yauwa Room Dinsa ya Nufa bayan yafito  ya umurceta dataje ta Kira Salma suci Abinci ba musu taje Ta kirata Saidai Abinda Salmar ta mata Bataji Dadi Ba Tadai Hadiye Saboda Tana mata Uzuri Ne Sai Dan kawai ta Shigo Room Dinta ta kiranta Shine ta Rufeta da masifa Haka ,, aka koya maki In kinga kinyi Sallama ba,a Amsaba kijira mana kawai kiwani shigo min Daki Kamar Kin Shiga kasuwa Hakuri ta Bata kamin yadawo Sanda ta Banna musu time kamin ta Zo da Farouq yamata Magana Cewa tayi Hava wai Meyasa baka Tausayina ne Rukayyah tace Gaskiya Yakama ka Rika mata Uzuri kasanfa yanayin Da take Ciki saida Haka,,  Baisake cewa komai  ba Har Rukayya tagama Saka ma Kowa Abinci A Zuciyar Salma cewa Take Jiwani Jagwal gwalo  Bari dai naci kar Kuma nayi Laifi ,, Dan Ba wuya nayi yanxun nan.

      " Haba kuzo kuga cin Abinci Su Salma harda Neman Kari๐Ÿ˜‚ Kuma fah  Jagwal gwalo ne Haka ta Bude Ciki ta kwashi Girki Sosai ,, Sanda taci Sosai harda Gyatsa ,, lol๐Ÿ˜œ Dear Please karakani Zuwa Cikin Gida Dan gaskiya na koshi dayawa fa Kai Salma  Sai kace A wurinki aka Fara yin Ciki da Murmushi Rukayyah tace Hava Dai Raka ta Din da zakayi shine wani Abu please Rakata mana ,, Dole ya Rakata Amma Daya Biye mata Allah kadai yasan abinda Za,ayi Sanda yakai Zuciyarsa nesa kamin Ya samu tabarsa Hmmm macce Shu,umar Gaske ce .

     ★Bayan yadawo ne Ya tar da Rukayyah Harta Gyara komai da komai Sannu da Aiki yace da Ita cike dajin kunya Murmushi tayi ,,masa kamin suka Dan Zauna a Fallon sunda n taba Kallo nawani Lokaci Daga Bisani Farouq ya Dauketa Zuwa Bed room Dinsa Yace Kallon ya isa Haka gobe kya Karasa ko ,, murmushi kawai ta Sakar masa Kamin ya bata Hot kiss Toilet yashiga Hakan ne yabata Damar Zuwa nata Room din ,, Ta canja  nata Kayan Tana Cikin fesa Turare taji Murda kofa Bata Duba ba Dan tasan Mai Shigowar Ji kawai tayi An Rugumeta ta  Baya tare da Cewa shine kika Gudo ko Toni na kawo kaina karban Turaren yayi ya Ajiye a Saman Mirror ,, ya Juyo da ita Suna jin Nufa shin Juna dago Fuskarta yayi Batayi Auneba taji Bakinsa a Nata Ba ko ,, Sassautawa yashiga Tsotsar Lips dinta Wani Yanayine marar Fassarawa Rukayya ta Tsinci Kanta Ciki ,, Ganin tsayi ya Gagaresu ,, Yasa suka Zube  a saman Bed Sai wani Shafa ta yakeyi ta ko,ina Tuni Farouq ya fita Hayyacinsa Dakyar ya iya tashi Ya kashe wutar  Dakin Da Zafi Zafi FAROUQ yake so ya Isar da Sakon ninsa yayinda Rukayyah najin Salo yafara Chanjawa ta Rokonsa Dayiyi Hakuri Amma INA Baimasan tanayiba Saboda yariga yayi Nisa Acikin Wata sabuwar Duniyar da Ya Tsinci Kansa Ganin Labarin Yagagari Saurarena Yasa nabarsu suji Dadin Shakatawa Nima Naje na Rugumi Nawa Ogon ๐Ÿ˜€Maman Usseey๐Ÿ˜˜

Note: A Duniya mutane kala2 ne wasu masu Hankali ,, Wasu kuma Allah Dai ya Kyau ta Magana itace Yakamata makiyana sugane cewa Zakaranda Allah yanufa da Chara sai yayi saboda Haka Duk mai Zagi yakama Jikinsa ,, Saboda zagi Baya qari kuma Duk Wanda Ya Zagi tsohon wani Nashi ya Raina Ni mai Hankalice so Bazan Biyewa mai zaginah Abinda kawai Nasani Ko Cikin mutun na Ciyo Bazan Daina Rubuta yar BAIWAH ba Idan kinji Zafi Gobe ki Rubuta naki Kuma bansaki Karatu Doleba so Kiyi Hakuri Nagaba yayi gaba nabaya sai Biyar Sahu kuyi Hkri Hater Bayanda Zakuyi Dani. Masoya nah nagode da kulawanku Maman Usseey love you All๐Ÿ˜


๐Ÿ™Ž 'YAR BAIWAH ๐Ÿ™Ž6⃣4⃣~Maman~ ~Usseey~๐Ÿ˜˜     ★ Kwanci Tashi Lokaci K'ara Wucewa kawai Yakeyi Yayinda Komai Sake Canjawa kawai yakeyi Amma Sha,anin Gidan Umar Farouq kam Abin  Ba,a Cewa komai Tun Ranarda Cikin Salma ya Zube Shikenan Suka Kasa Hakuri Ala Dole wai Dasa Hannun Rukayyah Dan Ganin Irin Kulawanda Yake Baiwa Salma Shine yasaka mata Magani a Abinci Cikin ta Ya Zube Allah Sarki Salma takasa Ganewa Abin Daga Allah ne Saboda likita ya Tabarta Da Cewa Ba wani Abinda yayi Course Din Problem Din Kawai Dai lokaci ne Da kuma irin yanayin Mahaifar ita Salma din. Sosai Farouq yaji Bakin Cikin Zubewar Cikin Salma sai Dai Ba yanda Ya iya Saboda Allah ne Mai Bayarwa  Wata kil Hakan Shine Alkhairi A garesa  Yayinda Salma da Mahaifiyar ta Kuwa suka Lashi takobin Sai sun Sanya Rukayyah Kuka Kamar yanda Salma Tayi sun Dauki Laifin da Batajiba Bata Ganiba Sun Daura Mata . 


  " Haka Rayuwar su tayita kasancewa Kullun Kudinsu na Hanyar Malamai da Bokayen Yan Tsibbu Sai Dai Har yanxu Sun kasa Samun Nasara Saboda Rukayyah Mutun CE mai Riko da Addini Bata wasav ko kadan Yayinda Hakama Farouq ko sunyi Abin Baya Tasiri Maimakon su Saduda Kara kaimi ma sukayi wurin Ganin Sun Cimma Burinsu.


    ★ Rukayyah na Kitchen tana Hada Girki Dan Yau Ita keda Aiki yayinda suna Makale a Waya itada F Dinta Sai Kyalkyalar Dariya takeyi Da Alama Zancen yana mata Dadi ,,gaskiya My F Yau karka Dade Dan Banason A kalle min kai A Hanya kamin Kadawo Gida ,, daga Dayan Bangaren yace Aikuwa Kamar kinsan Yau Saina Dade Dan Kuwa Tadi Zani Yau Turo Baki Tayi Hadi da Buga Kafa irin Wanda Yara Sukeyi  Please Nidai Kadaina Min Irin Wan nan wasa Allah basonta Nakeyi ba kwai kwayonta yayi Tare da Yin Murmushi Karki Damu My Angel Ur D Only One ai Daga ke An. Rufe kofa Kinji Zan dawo Very Soon Insha Allah ,, Fadada Fara,anta Tayi Kamin taci Gaba da Hada Girkin ta mai Rai Da Motsi  Tanayi tana Duba lokaci Duk da Tasan koya Dawo Ba yanxu zai Shigo ba Sai anjima Amma Dai Tafiso Yadawo Da Wuri ,, Haka ta Kammala komai Da Komai Ta Jera a Saman Dinning yayinda taje taci Wanka Tasanya Kaya Masu Bala,in Daukar Hankali ,, Ta Zauna A Sitting Room Tana Jiran Isowar Farouq Dinta .


  ★ Farouq kuwa Baidawo ba Sai Bayan Isha Dayake Yanxu Ba Tare Suke cin Abinci da Salma ba Ganin Bataso Yasanya ya Umarci Kowa Da Yayi Nasa koba Ranar Girkin Mutun Ba ,, part Din Salma yanufa Dan Dama A ka,idarsa Duk Wadda tafita Girki Sashenta zai Fara zuwa Kamin ya Je gurin Mai Girki Da Sallama ya Shiga Cikin Gidan Tana Zaune Tana Danna wayarta Bako ta Amsa masa Baiyi Mamakin Rashin Tarbonsa Dabatayi ba Dan Dama Ya lura Kamar kar ya kara Aure ta Canja masa More Especially tun da Rukayyah Ta Daina Shigowa Part dinta wata Rana Haka Zata Garashi Sai Sunyi Nisa ta Janye Jikinta Ala Dole sai sunyi Jinga Shida Matarsa Amma Bayanda ya Iya Saboda Bayaso yashiga Hakkinta ,, Kuma yana Kyaleta ne Dan Kawai kar Ace Dan yayi Aure ne Yake mata Wulakanci Wuceta yayi ya Shiga Dakinsa Ya Dauki Abinda Zai Bukata Kamin ya Fito ya Ya Ajiye mata Ledar ta Yace Sai da Safe Bako Godiya Balantana tamasa Magana Harara kawai Tabisa da ita yana Fita taja Wani Dogon Tsaki Mtseeeww Zaku Sani ne daga Kai Har Waccan Shegiyar Rukayyar Ta tashi Ta kulle Part din ta Tayi Shigewarta ta Kwanta Saka Banxa Saka Wofi Har Barawo yasaceta Bacci.

      ★ Cike da Haushin Salma Farouq ya Fito yanufi Part din Rukayyah A yaune yaso Yabasu Gift din Motocin da Ya Saya Musu Tun da Dadewa Amma Baccin Ran da Salma ta Sanya mishi yaji Yama Fasa Kyautar ,, Wai meyasa Mata Kishi yamusu yawane yatuna irin Rayuwar su DA sukayi a Baya Ya Ce Allah ya Kyauta ya Shiga part din Rukkayah Yana Bude kofa wani Daddan Kamshi yamasa Maraba Lale ,, Tana jin Bode kofa ta gudu tazo ta yi Hugging dinsa Ta Shiga yimasa Welcome Back Kiss Tare da Yimasa Sannu Dazuwa ,, Neman Damuwarsa Yayi ya Rasa Jansa tayi sai Room Dinsa Bayan ta Ajiye kayanda yashigo dasu Hada masa Ruwan wanka tayi Tare da jansa zuwa toilet cikin Wani Salo mai Rikitar da Mai Tunani Cikin kashe Murya tace My  F kayi wanka Sai kaci Abinci kona Tayakane murmushi yasakar mata Tare da Yawota Ya Rugumeta sosai ya lalubo Bakinta Yashiga tsotsa Ganin A Cikin Toilet suke kuma Tasan Halin Kayanta yasa tadanzare Jikinta cikin Salon Dabara Tace kayi Wanka Dai First Ta kallesa ta Ciremai Kayan da Zai Saka nashan Iska masu kyau kamin taje ta Sanya kayanda Ya siyo a Cikin Frige Wanka yayi Kamin ya Fito Daure da Towel Murmushi yayi a Cikin Zuciyarsa yace Allah yamaki Albarka My Angel Ya Fito ya Gyara Kansa Yasanya kayanda Ta Ajiye masa kamin Ya Fito Zuwa Sitting Room.


 ★ Yana Bude Kofa Tana Shigowa Kashe Mata Ido Daya yayi tace Wow kayi Kyau shine Baka Jira Nazo na Shirya ka ba,ko Sorry Ai koyanxu Kinyi K'okari Muje naci Abinci Dan Wallahi yunwa nakeji Shafa cikinsa tayi tace Sorry Dear please kadaina Zama da Yunwa Banaso Yace to Ai Yanxu gaki zaki kula Dani sukayi Dariya Chak yadauketa Bai Direta a ko,inaba sai Saman Kujera shima yazauna Ta sanya masa Abinci Amaimakon Taci tana a,a Bashi Tashiga yi Farouq ko Yabude Ciki Sai kwasar Girki yakeyi Sosai yaci Abinci Sanda ya koshi kamin Itama ya Fara Bata Abincin sai Shagwaba take Zuba masa Bayan sun koshi ta Tattara kayan Ta miyar a Kitchen Ta dawo ta kwanta a Saman Jikinsa tana wasa da Sajeen Fuskarsa yana Kallon News Ajima yakan Dan Kalleta yana Shafa mata sumar Gashinta Daya kwanta luf  Bada Jimawa ba Bacci yafara yin Awon gaba da Rukayyah Gyara mata Kwanciyar ta yayi Sanda yagama Kallon News Dinsa ya Dauketa Chak bude Ido tayi yace Sarkin Raki Badai Bacci Zakiyi ba Bayan kinsan Ban Baki Sakonnina ba Murmushi tamasa Tare dacewa My F nagaji please bari Gobe Dan Allah Girgiza mata kai yayi tare da Makale kafada.  Alamar Naki wayon Bai Direta ko,ina ba Sai Saman Bed Dinsa kamin Ya dawo ya kashe Kayan Kallon ya Rufe ko,ina Yadawo ya Samu Rukayyah Shafa Fuskarta yayi ta Bude Ido Wai My F dagaske Bazaka Hakura Sai Gobe ba Bai barta ta Karasa Zancen ba Yashiga Sance Mata Riga Wasa yafara yi da Duniyar Fulaninta Daga nan Kuma yadawo Yasha lips dinta sanda ya tsotse su Tas kamin Kuma ya Fara Aika mata da Sakonninsa Masu wuyar Fassarawa Da Zafi Zafi Yake Aika Isar 

mata Sakonsa lol๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜œ
~Maman~ ~Usseey~๐Ÿ˜˜


1 Response to "YAR BAIWAH Hausa Novels"