-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Dalilin shanyewar ƙafa bayan allura a ɗuwawu

Dalilin shanyewar ƙafa bayan allura a ɗuwawu

Dalilin shanyewar ƙafa bayan allura a ɗuwawu

"Injection Nerve Palsy" matsala ce da ke faruwa sakamakon raunata jijiyar laka ta 'sciatic nerve' da ke kai saƙonni zuwa wasu gungun tsokokin ƙafa.

Wannan matsala na faruwa ne idan aka kuskure aka tsira allura a kan jijiyar yayin yin allura a ɗuwawu, ko idan ruwan allurar ya lalace, ko kuma idan allurar ko ruwan allurar ya kawo kumburi a kewayen jijiyar wanda hakan ka iya danne ko shaƙe jijiyar har aikinta ya kassare.

Waɗanda suke da haɗarin gamuwa da wannan matsala sun haɗa da:

  • Wanda bai ba da haɗin kai yadda ya kamata ba yayin yin allurar, musamman ƙananan yara.
  • Mai rama sosai.
  • Faɗawa hannun wanda bai ƙware ba.
  • Da kuma wanda tsautsayi ya faɗawa.

Alamomin wannan matsala na faruwa ne a dukkan rassan jijiyar a ƙafar nan take ko bayan wani ɗan lokaci.

Alamomin sun haɗa da:

  • Matsanancin ciwo,
  • Sagewa,
  • Rauni ko rashin ƙarfin ƙafar,
  • Rashin ji a fata idan aka taɓa,
  • Wahalar tafiya: ɗingishi, jan ƙafa, da sauransu.

Da zarar an lura da waɗannan matsaloli da aka ambata a sama, a gaggauta sanar da jami'in lafiyar da ya yi allurar domin ɗaukar matakan gaggawa. Wannan matsala ana warkewa kamar ba a yi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti na iya kawo naƙasu ga ƙafar.

Saboda haka, akwai buƙatar ganin likitocin fisiyo (Physiotherapists) da ke kula da matsalolin jijiya, ƙashi, da tsoka domin  sune ke da alhakin farfaɗo da aikin ƙafar.

Source: Physio Hausa.

0 Response to "Dalilin shanyewar ƙafa bayan allura a ɗuwawu"

Post a Comment