An Cafke Mutum Biyu (2) Da Sukaci Gasashen Naman 'Yan Sanda A Jahar Oyo

An Cafke Mutum Biyu (2) Da Sukaci Gasashen Naman 'Yan Sanda A Jahar Oyo


Rundunar 'yan sandan dake reshen jihar Oyo, ta tabbatar da kama mutum biyu (2) kan zarginsu da cin gasashen naman 'yan sandan da aka kona yayin zanga-zangar yan sandar Sars(Endsars demonstration).

BBC ta tuntubi mai magana da yawun 'yan sandan jihar Oyo, mai suna Fadeyi Olubenga, inda ya tabbatar da cewa an tasa keyar mutum biyune a yau Asabar a lbadan babban birnin jihar. 

Ya ce an kaddamar da binciken neman wadanda suka yi wannan aika-aikar ne bayan wani bidiyo da aka rinka yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutane suka kashe 'yan sanda da kuma kona su, Tare da yin amfani da adda suna daddatsa naman su suna ci. 

Ya kuma bayyana cewa an tafl da wadanda ake zargin zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke babban birnin jaha Abuja domin ci gaba da gudanar da bincike. 

Source: BBC 


0/Post a Comment/Comments

Previous Post Next Post

Stay Conneted

Most Recent